Page 24

489 21 0
                                    

*INUWAR ZUCIYATA ❤*
     _(Zarah Ko Jeedah)_

*Na Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh Gee*

*ViaWattpd@Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai*
________________________________
*Yan uwa bakina bazai iya nuna maku irin dunbin farincikin da nake ciki😊Nagode sosai masu kirana à waya da masu ai komin sakonni suna tambayar jikin Hajiyata da sauki sosai tana godiya yan uwa, musamman Rahmat Nalele😅ni taki ce h'ar abada Mama suna godiya da karamcin da kika nuna masu Allah yabaki zuri'a masu albarka ameen😘.masoyana Ni Raheenat ina godiya idan na ce na lisafo ku zan cika pag biyu ban gama ba dan h'aka ku sa a r'anku ina alfahari daku Allah ubangiji ya biya mak'u bukatun ku na Alheri ameen.Insha Allah daga yanzu zaku d'inga samun cigaban littafinga à kullum😅Ana mugun tare☺masoyana a wattpd ban manta da ku ba kuna raina ku cigaba da yin voting and comnt❤*
___________________
*INUWAR ZUCIYATA❤ Littafin mai ban tausayi, sadaukarwa, kauna zurfin ciki, soyayya da dai sauransu ku cigaba da bina yanzu muka fara shigo cikin labarin*
__________________

*<<Page 24>>*

Ramadan yayi dariya ya ce "À rashin samari ba ". Ta ce, "To me ya raba ? Kai yaro idan ka ga soyayyar da muke yi da Alhaji à zamanin mu wallahi matsawa zaka yi ". Yayi dariya ya ce "Kun yi soyayya ya cika miki gida da kishiyoyi ?  Ki bari na auri Jikar Inna daga ita babu kari ".
      Alhaji yayi dariya ya ce, "Lallai kam naga alama, da wannan idon ka irin na Alhaji da ke biyo su zaka iya zama da mace daya ". Kunya ce ta kama Ramadan, ya mike à tsaye. Tabawa ta ce "Indai gaskiya ne ka biyo irin idon na Alhaji da mace hudu na ganka ".
    Ramadan yayi dariya ya ce "Aa, daga Jeedah ba kari ta isheni rayuwa". Ya mike yana shirin barin wurin. Alhaji ya ce "Lallai kam !  Idan kayi sa'a Jeedah naka ta jure maka ta ishe ka, don naga idonta kamar za ta jure namiji ". Da sauri ya fice yana dariaya ya ce "Kai tsofaffi baku da dama wallahi ".

*Washe-gari*

À ka yi shiri mota uku da kudin neman aure yadda ya zo a al'adar 'yan Niamey, sai goro da alewa kowanne katan goma gaisuwar iyaye, sai kudin dorawa dubu dari, mota biyu ta maza biyu ta mata.
     A ranar ba Wanda ya fita sun cika gida da yan karbar aure, iyayen kowa yana nan. Ita kam Jeedah haka ta yini Sukuku ba farin ciki ba bakin ciki ba, tana saman Mmy a kwance ta ji motocin suna shigowa harabar gidan, ta mike ta leka ta windo, Ramadan ta gani, don haka ba ta sake motsi ma ta koma ta kwanta.
      Amma kuma sai zuciya take rada mata, tashi ki kuma ganin Ramadan me Jaheed zai gaya mashi ? Kusan fuskarsu iri daya, amma ai Ramadan yafi Jaheed kyau. Wata zuciyar ta ce mata, idan maganar kyau ake yi, kyau tsantsarsa ai sai Jaheed. Ta mike à tsaye ta daga labulen windon haske ya kara bayyana a dakin, ta ringa kallon Ramadan gayen ya hadu, kusan yafi Jaheed komai, idan ana maganar tsayi da zati dolé a sanyo Ramadan a ciki, haskensa tamkar balarabe, sumarsa irin mai kwanciya ce ta taru ta kwanta a kansa.
    Sanye yake cikin riga yar ciki da wando, hula ce zanna bukar a kansa amma ba ta hana a ga sumar sa ba. To ina maganar agogo?Diamond   💎 ne zallarsa, kamshi yake tamkar yau ne ranar auren in ji Mufeeda da ta ganshi a safiyar yau.
      Ta ce "Yau kuma ina Yaya Ramadan zai je ya wani sanya babbar riga? " bai tanka mata ba. Alhaji ne ya ce "Neman aure zan raka shi, Kin san nine babbar aboki ". Ta ce "Wai neman auran jikar Inna? "
    Ya ce mata "Ehe! " ta ce "Wallahi baku dace ba ,har MA duk gayanku ka tsaya a wannan yar yarinyar, ni nayi tsammanin gogaggiyar baturiya za ka Nemo mana? "
     Ramadan bai yi magana ba ya ringa danne-danne a waya.  Alhaji ne ya bata amsa ya ce "Eh! Lallai kam, ita ya zaba ki fada ko kishi kike yi don bai zabe ki ba? " tayi dariya ta fice tana fadin "Allah ya sauwake ".
     Alhaji ya ce "kece babbar kawa nine babban aboki ". Ramadan ya ce "Kin taka ajin da ba naku ba, ban ki ba idan ka yi nadinku na gado na baka mai gadi ba ".
   Suka kama dariya, shi kadai ya ke murmushi a yau, tare da tunanin kaya dariya iri iri, nishadi yake ji komai ka yi mashi a yau faranta mishi ake yi.
      suna shiga Niamey ana kiran sallar azahar, sai da suka yi salla a masalacin gidan. A babban falon sashen Mami aka yi masu masauki, gaban Inna hadjara Ramadan ya je ya zauna ya ce "Ga babbar amarya da ke zamu dinner party ".
    Inna ta ce "Can ka karaci gulmarka bani kake nufi ba na sani ". Abba Yusuf ya ce "To yanzu dai ka fita ka bamu wuri don ma rashin kunya a gabanka za a nemi aurenka? "
    Alhaji Mubarak ya ce "Kyale shi kawai su yaran zamani wani kunya suke ji a maganar aurensu? Ka gansu nan komai Jaheed da shi aka yi na aurensa ba kunya ".
   Ramadan ya mike ya  dauki shany milk ya  bar wurin, sitro ya  sanya yana zuka, sai da ya sha ta ishe shi ya kira waya. Jeedah tana kwance wayar ta yi ringing, sai da ta katse ba a dauka ba, ya sake kiranta sai da ta kuma katsewa. A karo na uku sannan ta daga cike da yanga, ta gane Ramadan ne ta ce "Hello! "
    Ya yi dum! Jin kasala ta sakko mashi, ya tuna shi fa namiji ne. Ya daure ya ce "Ramadan ne kina ina? " ita din ma duk yadda ta so ta ja mashi rai ta kasa, dole ta ce "Ina saman Mmy " yayi wani irin salo wanda ya san dole ya saukar mata gajiya ya ce "Ok! I want see you ya za a yi? " ta yi kamar bata ji shi ba,  ta dai daure ta ce "Ok! Ina jira kana iya shigowa, ina nan falon sama ".
     Ta ringa bin kafar benen a tsanake, ya shigo falon tana kwance cikin doguwar kujera, sanye take cikin wani irin bujejen wando mai kalar pinc da T. Shirt fara kal mai dan hannu, sai fulawa kalar pink a gaban rigar, dan siririn mayafi ne a kanta.
     Ya kalli rigar cibinta a waje, tana mikewa a tsaye idonsa a kanta, ta sanya hannu ta janyo rigar. Yayi murmushi ya mika mata madarar da take hannunsa, ya cire babbar rigarsa da hularsa ya ce "Kalle ki kin wani manna riga a wannan dan jikin naki, to ya gari? " ba ta amsa ba, sai dai ta lumshe ido ta nemi wuri ta zauna, ya yin da shi din ma ya zauna a gefenta ta matsa.
   Ya ce "Meye kike wani matsawa ko dan kinga ban sanya hannuna a cikin wannan rigar taki na yi yadda nake so ba? " ya fada yana kashe ta da kallonsa mai tayar mata da hankali.
     Ramadan mai kunya ne ba ya iya doguwar magana da mace, amma dube shi a gaban Jeedah. Kunya ta kamata ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, ta ce "Haba dan Allah da girmanka? "
      Ya ce "Meye girman? Ana girma da wannan wasan NE? " ta girgiza kai .ya ce "Ban yi break ba ina dokin zan zo na ga wannan Golden eyes din naki, me zaki bani na ci? "
     Ta mika mashi madarar hannunta, ya ce "Wannan naki ne ki sha "ta girgiza kai ta ce "Ni ban fiye son madara ba ". Ya ce "Aa don Allah ki yi hakuri ki amsa bana son ki ce ba za ki ringa shan madara ba, ko kin manta a jikinki rayuwata take? "
    Ai kuwa ba shiri ta mike ta bar wurin. Ya bita kicin ta ce "Ga abinci me zan zuba maka?  Sakwara ko kus-kus ko farar shinkafa? " ya yi dariya ya girgiza kai, ya ce "Irin girkinki da na ci wancan satin ya sa na raina girkin mutane, idan ba naki na ci ba babu dandano bakina". Ta yi murmushi ta ce "Toh".
        Sai da ta fasa kwai da yawa ta yi hadi da onga da gishiri kadan, sai albasa da attaruhu da ta dan jajjaga a blander, ta yayyanka hanta, hantar ta fara zubawa da yar albasae, tana fara soyuwa sai ta juye kwan a kai, ta dama mashi custard kofi guda ta juye peak milk gwangwani daya na ruwa, ta sanya suga, sai kuma ta dora farfesun kaza da dane romo kadan, taji kayan hadi dahuwar daddawa irin wanda Inna take yi, ta juye a kwanon tangaran ta Dora murfi.
   Tana tsaye yana kallonta ta ce "To ai shi ke nan na kashe Gas, muje falo ". Ya ce "Aiki haka da sauri cikin minti talatin ". Ya amshi abincin suka fito.
     A falon suka zo suna cin abincin, santi yake yi mata ita kam sai dai murmushi, ba ta iya yi mashi magana don ba ta yi tsammanin yana da saukin kai irin haka ba.
     Ta ce "Ni fa ban yi azahar ba, bari na je na yi sallah ". Ya kalli agogo ya ce "Don Allah kar ki dade ". Tayi murmushi tare da fadin "To" ta wuce ya bita da kallo....

Inuwar zuciyata...(Zarah ko Jeedah) by RaheenatmamoudouWhere stories live. Discover now