Page 26

430 18 0
                                    

*INUWAR ZUCIYATA❤*
           _{Zarah ko Jeedah}_

*Na: Raheenat Mamoudou*

*Story by: Mamuh geee*

*ViaWattpd Raheenatmamoudou*

*Da Sunan Allah mai rahma mai jin kai*
_________________________________

*<<Page 26>>*

Fauziya kam takaici ya ishe ta, tana tsananin son Yaya Ramadan ,a tsammaninta auransa da Jeedah zai wargaje ganin irin kallon da suke ma juna wurin bikin Jaheed, sai kuma taji aure kwatsam.
     Ta kalli Ramadan cike da wasa duk zuciyarta a cushe ta ce "Lallai ma yaya Ramadan, aure ba shiri?" ya ce "Wallahi Fauziya, kinga ikon Allah, amma za a yi biki ki shirya ki ga bikin da ba a taba yi ba a Diffa ". Tayi 'yar tsuki tare da tabe baki ta ce "Lallai ma, don ma amaryar taka bata sonka ".
Ya harareta ya ce "Eh, haka nan nake son kayata, a hankali zan koya mata sona, ko ya kika ce amaryata? "
Fareeda ta ce "Lallai zamu ga amarya da kunya, in dai mune gara ki bude idonki wallahi yanzu muka fara tsokanarki ".
    Hajiyar Ramadan ce ta kore su, ita kam Jeedah duk jikinta yayi sanyi. Ramadan din ya kalle ta cike da tsananin so d atausayi ya ce "Zan je masallaci yanzu zan dawo ".
    A hankali ta ce "A dawo lafiya ". Ita din ma sallar ta yi sannan tayi wanka ta sanya doguwar riga irin mai rubi biyun nan kalar Blue, ta lullube kanta da mayafin rigar tayi zaune ke nan a bakin gadon hajiyar Ramadan. Wayarta tayi kira, ta sanya hannu ta dauka. Zarah ce ta bugo mata, ta danna calling da sauri ta ce "Wayyo my sister na mu blebed sis, kin ganni a Diffa. Zarah ta ce "Wai me yake faruwa ne?  Jeedah ta ce "An daura aurena da Yaya Ramadan mana, verry Surprise, ko ni ban wayi gari da shirin aure ba, kwatsam!  Ya zo mini ".
     Zarah ta ce "Ai ke kin yi Sa'a kowa sonki yake yi, amma ni da Jaheed babu dadi wallahi azabatar dani yake duk na fita haiyacina, don ni Dana san irin wulakancin da zai yi Min kenan Allah ba zan sanya rayuwata a cikin garari ba Jeedah. "
     Ai kuma sai Jeedah ta ji tausayin 'yar uwarta ya lullube ta, ta ce "Ki yi hakuri Yaya Zarah, ki ci gaba da addu'a ko ni zan taimaka miki da addu'a, insha Allah komai zai warware".
    Zarah ta ce "Uhm! Jeedah wallahi nayi nadama da na sani tun farko na barku kun yi aurenku, kuna son juna na zake................" katseta Jeedah tayi, ta ce "Don Allah Yaya Zarah ki daina irin wannan zancen ,bana son kina mai da hannun agogo baya, abun da ya wuce ya wuce, don ni tun ranar aurenki na shafe komai a zuciyata, Don Allah ki daina sanya ma kanki damuwa kin ji ko?"sai can ta tsinkayi muryar 'yar uwar tata tana faman kuka, tausayinta ya kama ta, ta jima tana lallashinta sannan suka yi sallama da juna.
    Jaheed yana tsaye bakin kofa yana jin Zarah tana waya kamar a mafarki wane irin anyi ma Jeedah aure,  waye ma zai yi mata wani aure kamar yar tsana?  Ba zai yiwu ba sam!
   Ya fice bankolin benensa ya zaro wayarsa ya kira Daddy. Ya ce "Hello Dad barka da yamma ya gidan? " Daddy ya ce "Kowa lafiya, sai dai an daura auran Jeedah dazu da yamma ".
    Ya ce "Daddy wani irin aure?  Waye mijin? " Daddy ya ce "Ba kowane mijin ba, Ramadan ne kai ka sani Alhajin Diffa ya fi karfin komai a wurin Inna, shine ya bayas da umarnin hakan, mu me zamu ce Jaheed?  Dukanmu 'yan biyayya ne ga abun da manya suke so ".
   Jaheed cikin wata irin murya ya ce "Daddy ya haka? Ya kuma karatun Jeedah? " Daddy ya ce "To ni ina ruwana da karatunta balle kai?  Can tsakaninsu da mijinta, amma ni babu abun da ya shafe ni da karatunta? "
       Jaheed yayi shiru ya rasa abun da zai ce, ya ce "To amma Daddy shi kenan don Allah Alhaji Babba ya ce a daura aure sai kuma a basu amarya ba ayi biki ba? Ni ban taba ganin inda aka yi haka ba, ita Jeedah me ya sa komai nata sai anyi shi daban? "
     Daddy ya ce "Haka Allah ya tsara mata komai nata daban da sauran 'yan uwanta, baiwarta ce ta zo a hakan. " Zuciyar Jaheed ta ce "To ya za kayi an riga an gama komai kai yanzun nan kana da abun cewa ne?
    Ya saki ajiyar zuciya, a hankali ya ce "Shi kenan Daddy, Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi ". Daddy ya ce "Addua'ar da muke yi muku a kullum ke nan, yadda muka bi iyayenmu kuma Allah yasa ku bimu ". Ya amsa a hankali "Amin".
      Auran Jeedah da Ramadan shine mafarin zaman lafiyar gidan su Zarah da Jaheed, amma duk da haka zaman gashi nan ne, Don Jaheed ya ci burin idan Zarah ta gaji da, zama a gidansa tai tafiyarta gida dole a gaji a raba auran ya auri son ransa, amma shine sai aka yi masa shigar sauri irin haka, lallai ma Ramadan din nan.
    Ya jima yana tunani, ya kira Isma'il ya gaya mashi, shi din ma yaji haushi, ya ce "Ya aka yi haka Jaheed, auran Jeedah ya zo mana very soon? " yayi tsaki ya ce "Ni yaron nan ne da aka aura mata bai yi min ba".
Isma'il ya ce "No, ba kai ka janyo komai ba, koni nan ina son Jeedah amma duk ka bi ka wani hana kowa sakat, gashi duk mun rasa 😆🤭. Dan kai daman baka layin masu auranta, amma ni fa?.......... Jaheed ya katse shi ya ce "Kai don Allah ni sai anjima ".
    Ya kira Ramadan sai kuma yaji a kulle wayar, ya ja tsuki ya ce "Ko uban me yake yi zai wani kashe waya? Shege dan iska sai naci Ubansa,  ya kira layin Jeedah, sai kuwa ta daga maimakon taya murna auran da tayi, sai ya lullube ta da matsifa, fada ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba.
   Jeedah tayi sakware tana jinsa, takaici ya ishe ta, ta ce "Wai kai me kake nufi ne, da wannan fadan naka?  Nifa ban gane nufinka ba? " ya ce "Ai kin san ko meye nufina, sai dai ki ki fahimtata. Ni ai niyyata ba wata boyayya ce ba, tunda aka kawo min Zarah gidan nan ko dan yatsanta ban rike ba, niyyata idan ta gaji da wulakancina ta koma gida su warware auren a Aura min ke, amma shine kika yi mini haka ko? "
     Jikin Jeedah yayi sanyi, tama rasa me zata ce, sai a yanzu ta sake amincewa da zancen Zarah, tausayin yar uwarta ya kuma lullubeta, wace irin kiyayya ce wannan yake nuna mata? Anya kuwa Jaheed yana da hankali?  To ko son ne ya zauta shi bata sani ba?
      Daga can ta ji muryarsa yana fadin "Don haka kada ki yadda Ramadan ya kusance ki, ki rike mini amanar kanki, idan an warware auren mu da Zarah kema sai.................."

Inuwar zuciyata...(Zarah ko Jeedah) by RaheenatmamoudouDonde viven las historias. Descúbrelo ahora