❣❣ LABARIN AURENA❣❣
Nah
Khadijah AhmadHaske writers asso
31-35
Yanayin kallo da na bita dashi yasata saurin d'aga hannuwa sama "hey hey..ba wani abu bane, tayi k'asa da murya prince charming d'ina ya dawo ta rungume hannuwa a k'irji "after a long period zamu sake had'uwa, ta kalle ni bara na wuce sai mun had'u gobe" numfashi na sauke nabi bayanta da kallo a fili na furta "crazy Aneesa" na maida hankali na dan sauraran intro d'in da malami ke mana. Skul was fun naji dad'in karatun mu na yau.
Misalin k'arfe biyu na koma gida ina shiga nahau zayyana wa adda labarin makaranta har da na crazy Aneesa sis deeja ce ta mik'e tare da fad'in "adda bara na lek'a gidan aunty bara'at (mak'ociyar adda)", "to amma kada ko jima nasan halinku in kuka had'u da 'ya'yanta" "nima zan bita adda"na fad'a a marairaice, "kinji ko nikuma kubar ni ni kad'ai ko?" A shagwab'e nace "adda ba zamu dad'e ba" "ah to inma kun dad'e kun kori gaba ai kuma hajia mama zata zo" cike da farin ciki nace "yehhh..aikam dole mu dawo da wuri" mukai mata sallama muka fice. Fitar mu k'ofar gida ke da wuya muka jiyo k'ara keken me icecream a tare muka kalli juna ai kuwa muka ruga 'kar kuga laifinmu we r really love icecream especially irin wannan dere's something special about it😋).
"Nawa nawa malam" na tambaya
"Hamsin hamsin" yace
"Bamu guda hud'u" zubawa yayi ya mik'o mana, na zari d'ari biyu na bashi yayi godiya muka tafi.
"Sis deeja a hanya fa muke kike sha"
"Lil sis bafa kowa ni dake ne kurum"
Roaming eyes d'ina nayi tabbas ba kowa "nima zan iya sha kenan" deeja da dad'in ice cream ya gama tafiya da ita kai kawai ta d'aga, aikam without second thought nahau lasa munasha muna zuba bamu ankare ba sai gani mukayi munyi kicib'is da mutum bama kamar deeja da ice cream d'inta ya tsiyaye tas a jikinsa,.. Hmm, deeja masifa tuni tahau zuba masa.
"Malam baka ganine, ko kai din makaho ne?!" Nikam da ido na naga ice cream d'inta daya tsiyaye nace
"Sis deeja kinga ice cream d'inki" ido waje ta kalla kan tace "wullahi sai ka biyani" ta juya "gashi me ice cream d'in ya tafi" ta fad'a a raunane, shi dai mutumin bece uffan ba sai dai bin duk wani motsinta da ido. K'ikk'ifta idanu tayi "ahh! Ko baka ji kuma, hello! Ta d'aga hannu saitin idonsa amma sam bai motsa ba, kallon juna mukayi "Naila it seems he's deaf and dumb!" Ido na zaro waje "kenan zai iya zama mahau..." ai kan na kai aya tuni ta arta ana kare nima na mara mata baya bamu tsaya a ko ina ba sai a falon adda muna faman maida numfashi. Sai da muka sami nutsuwa muka kalla juna atare muka furta "ci...mahaukaci kenan???"
Sis deeja tace "Amma baiyi kama da haka ba"
"Meyasa be mana magana ba then?"
"May be bazai Iya handling shirmen mu bane, wait ina ice cream d'inki?"
Kallon hannu na nayi "ya fad'i a hanya" muka bushe da dariya.
"Deeja, Naila"
"Na'am adda gamu nan"suka nufi falon Abba.
Suna zuwa wa zasu gani?, a guje suka k'arasa wurinta, fara'ar dattijuwar ta dad'u
"Ga yammata na ga yammata na" rungumeta sukayi
Can na turb'une fuska "ah ah 'yar mama 'dake haka take kirana' meye kika had'e rai"
"To ba kece kikayi tafiyar ki, ki ka barni ba"
"Oh! Lallai nayi laifi" ta dad'a rungumoni "shiyasa ai nazo natafi da 'yar mama nasan tayi kewata kamar yanda nayi tata" na wangale baki "dagaske mama" ta gyad'a kai, adda na kalla ta gyad'a kai tana murmushi na rungumo mama nace "kimin alk'awari bazaki dad'a tafiya ki barni ba"
"Daman kiran yaya laure na ansa kinsan bata ji dad'i ba amma bazan kuma yin nisa dake ba saidai mu tafi tare"
"Yawwa mamata," nan na shiga bata labarin jami'ar dana fara zuwa.
(Mama mahaifiya ce ga abba mijin adda, sunanta na gaskiya Hajiya Ruk'ayya, mijinta ya rasu cikin hatsarin jirgi, abbane d'anta na farko sai k'aninsa Najib wanda take cema auta kasancewar shine k'arami, wanda yake babban soja ne yanzu haka yana Lagos, shak'uwata da ita ta samo asaline ga wata rashin lafiya data tab'a yi nayi jinyarta tun daga wannan lokacin take k'aunata ko aike in auta zeyi sai tace in be had'a dani ba bataso). Wannan kenan.
Drivern mama ne ya ja mu zuwa tangamemen gidanta dake state road inda tundaga gate sojoji suka fara mana sallama "mama kinga sojoji a gidanki"
Cike da fara'a ta ce "'yar mama AUTA ne ya dira"
'Ya dira?'..."auta?" Gyad'a kai tayi ta bud'e murfin motar ta fice tana fad'in "shigo maza kiga autana"
Ji nayi k'irjina yahau bugawa hango bindiga da nayi mak'ale jikin d'aya a cikin sojojin muk'ut na hadi'yi wani wahalallan yawu, sad'af sad'af tamkar mara gaskiya na nufi k'ofar baya na shige gidan duk gudun kada mu had'u da autan mama dan a tunani na tunda yaransa na rik'e bindiga to shikuma ya kenan!.
"Tnx for ol ur prayers I'm getting better love u ol, naso yin page biyu amma be yiwu ba, but insha'Allah i promise you a next post luv u loads❣❣❣"©Kdeey😊

YOU ARE READING
LABARIN AURENA
RomanceLabarin soyayya, sadaukarwa, cin amana... Najib da naila sun taso cikin jin dad'in rayuwa even thou mahaifan Naila r ol late, Najib ma mahaifinsa ya rasu, he's living with his mom. Sunyi aure bisa ga soyayyar da suke wa juna komai na morewar ra...