He confesses❣

709 52 0
                                    

❣❣ LABARIN AURENA❣❣

Na
  Khadeejah Ahmad
Haske writers asso

                  66-70
  
    Tun kafin motar ta tsaya na bud'e nayi cikin gida a guje inaji yana kwalan kira, a d'aki na tadda mama tana linkin kaya, na haye gadon da sauri na lafe a bayanta, tambayata take lafiya ina ban ansata ba saima kukan shagwab'a da nake, a rud'e tace "'yar mama meyafaru?"

  "Mene kuwa Allah ne ya taimaka bata ji ciwo ba"

  "Ciwo kamar yaya?"

  "Mota na tafiya ta fito.."

Dafe k'irji tayi, "ya subhanallahi,
Naila me ya kaiki wanan gangancin?"

.cikin sheshshek'ar kuka nace "bashine kawai ya d'aukoni daga gidan adda ba bayan nace kwana zanyi",

"auta na zata na fad'a maka meyasa bakajin magana iyeh? Yarinyar nan ta jima rabon ta lek'asu shine daga zuwanka zaka fara takurata to wullahi ahir d'inka bazan d'auka ba!" Ta juyo  "yi hak'uri 'yar mama kyaleni dashi na miki alk'awarin kaiki da zarar ya tafi" girgiza kai nayi na turo baki ta juya tana mai fad'a na silale zuwa d'akina.

  Sashensa ya tafi rai a cusgune ba abinda ke bak'anta masa sai yacce mama ta tak'ark'are tana masa fad'a a gaban yarinyar nan ita kuma ta kafeshi da manyan idanunta, kwafa yayi ya saki wani shu'umin murmushi a fili yace "u'll pay for it!"

  Kwana biyu da faruwar haka na shiga yin wasan b'uya da Najib gudun kada ya mini fad'a kamar yanda naja mama tayi mai, dake yau asabar na tashi da aikin sanitation ko ina na gidan na gyare shi k'al k'al, bayan na gama na dafa abincin rana sannan nayi wanka na shirya cikin riga da skirt yan kanti ruwan goro (orange) masu be za ko ya na motsa sai sun motsa nayi kyau sosai cikin kayan.

    Falo na ko ma na zauna gefen mama
A gajiye nace "Wash Allah na!", kallona tayi "sannu 'yar mama nace miki kina kiran karima me'aiki tana kama miki aikin yafi k'arfin na mutum d'aya"

"Mamana kenan bakomai wullahi kawai dake jiya na shiga skul shiyasa nagaji amma ba aikin bane"

"Ah to nidai daga yau inma kidena inma karime tarink'a tayaki" dariya nayi ganin yacce ta hak'ik'ance tsakaninta da Allah ni kuma har ga Allah banjin aikin kasancewar na saba ko a gidan adda haka nake banson ganin datti ko yaya dan da, da hali bank'i nayi kullum ba"

  "Assalamu alaikum"muka jiyo muryar Najib, da sauri nayi k'asa da kaina kamar mara gaskiya, kujerar dake gefena ya zauna ya wani mik'e k'afa, kan table, tunda na ansa sallamar ban kuma cewa komai ba na shiga wasa da yatsun hannu na,  gaisawa sukayi da mama nima na gaisheshi ba tare da na d'ago ba, kusan mintuna biyar yace
"mama bani aron 'yarki mana ta tayani aiki"

"Aiki kuma Najib wani iri", nikam gabana ne ya fad'i na d'ago a firgice
   "zamu d'an fita ne zuwa gidan su budurwar Abdul ra'uf"

   "Lafia dai ko?"

"Eh kalau zamuje ne kawai inaso su saba ne", kallon mama nayi don jin ansar da zata bashi, abin mamaki sai jinayi tace "to sai kun dawo" jinayi kamar ta kafan mashi a zuciya dan ban aminta da maganar shiba kula da yacce yake min dariya k'asa k'asa wacce na ayyana tabbas akwai wata a k'asa
  "Naila" ya kira sunana cikin horse voice d'insa, kallonsa nayi ya d'agan gira "shiga ki shirya zamu fita" a sanyaye na tashi na fad'a d'aki a bakin gado na zauna tunani fal kaina, dariyar da kemun yawo a ka jikina ya bani akwai wata a k'asa tunanin yacce zan b'ullowa abin na shiga yi can na jiyo muryarsa yana kirana, zumbur na tashi abaya na saka na nad'a talha na zari jakata da takalmi na samesa tsaye a falo har ya canjo kaya farar riga da bak'in jeans yayi kyau sosai ya sumarsa ta kwanta luf luf ta dad'a fito da asalin kyansa irin na hausa fulani, iska naji a idona nayi farr da ido ashewai tafi yamini saboda guntun tunanin da na tafi, mama ma ni take kalla

  "Lafiya dai 'yar mama?", diriricewa nayi
"Uh uhm bakomai"dariya yayi k'asa k'asa yana gyara agogon hannunsa kan yace da mama
  "Mu mun wuce"
   "To saikun dawo ka kular min da ita"
  "Haba mama wannan k'atuwar ai sai dai ta kula dani ma"
  Turo baki nayi ina bubbuga k'afa "Uhum uhum mama
kinji shi ko?"
Mur tayi "auta zan hana fitar nan indai tsokanarta zaka keyi" d'aga hannu yayi
"Ba ayi haka ba saimun dawo" ya fice.
  "Mama saimun dawo" na mara masa baya inajiyo ta tana cewa na kula da kaina.

****
  Gaban wani eatery yayi parking, mamaki nayi na juya da niyyar magana shima ni yake kallo yana wani sassanyan murmushi , kasa shiru nayi nace
  "Me ya kawo mu nan kuma"
"We are having our date night"
A rud'e nace "Date kuma?"
  "Yeah, yayi unlockn k'ofofin bismillah sauka, jiki a mace na bud'e ya fito shima ya rufe motar zagayo wa yayi muka jera zuwa cikin tafkeken eatery d'in da shigarmu wani waiter ya zo ya gaida shi tare da nuna mana wani table daga can gefe wanda ba kowa wurin an zagaye shi da wani k'yalle ja an wa wurin ado da jajjaye da fararen fulawoyi saman teburin ba komai sai plate da fork, spoon da table knife  da tissue a gefe da kuma table napkins, nidai mamaki bai  barni ba saida naga ya jamin kujera na zauna shima ya zauna kan d'ayar yana murmushi nikam sai kalle kale nake inajiran ganin ta inda budurwar abokin nasa za ta b'ullo dan a zatona sunyi zasu had'u a nan ne,
  "Ehenm.."yayi gyaran murya, na juyo da sauri, "kar ki zama "yar k'auye mana kike kalle kalle just focus on me!" Had'e rai nayi, na kauda kaina gefe, yayi dariya k'asa k'asa yana cewa
  "Ayi hak'uri dan Allah banyi haka dan na b'ata ranki ba "sanyi naji a raina ganin ya ansa laifinsa har ma yana bani hak'uri saidai kuma me ji nayi an rik'o hannuna ko da na d'ago Najib naga ya sark'e hannun mu cikin na juna a tsorace na kallesa siririyar kwalla kwance cikin idona

"Shiii..ya d'ora yatsa kan lips d'ina da rawar jiki nasa hannu na bige ina kici kicin kwace d'ayan amma ko gezau beyi ba, hawayene suka hau wanken fuska
nace "dan Allah ka cikan hannu kaga fa be kama ta ba!", ai tamkar ina magana da gunki sam yak'i sakin hannun saima ido dayake bina dashi tamkar me son gano wani abu a idona ni kuma nak'i muyi making eye contact,
  "Idan kika kuma k'ok'arin fusgar hannun nan wullahi zan miki abinda yafi haka inyaso muga yacce zakiyi!"

   Cak! Na nutsu idona a k'asa hawaye na shatata,
"Naila look into my eyes!" Naji maganarsa tamkar daga sama d'ago kwayar idona nayi a hankali na sauke a kansa ba tare dana kalli cikin idonshi ba"
   "Not me my eyes"ya kuma nema, cikin gajiya da zantukan sa nace
"Wai dan Allah meye dalilin kawoni nan da kayi"
"Saurin me kikeyi?"
  "Am bored sitting here doing nothing important!" Nace a hasale, kallona yayi idanunsa sun kad'a ya had'e rai hantar cikina ce ta kad'a tsabar firgici nahau janye hannuna a hankali, karaf ya bud'e ido mukayi four eyes aikuwa sai hawaye sukahau shatata daga idona

  "Dan Allah kayi hak'uri au..,"

"Shut up!, dan ina lallab'aki doesn't mean zakina mini yacce kikeso hv u forgotten who i am?" to tsaya kiji nagaji da kwana kwana to tell u d truth nayima mama k'aryane dan nasamu hanyar fitowa dake na sanar miki da abinda ke zuciyata!, Naila gaskiyar al'amari shine am..a yahau inda in da, hannu ya zira a kanshi ya shafo kan yace "Naila i love yhu!" Darararam k'irjinta yayi wani irin bugu nima dai kdeey d'if cajin wayata ya  d'auke dan tsabar firgita da jin kalaman Autan mama!

©Kdeey😊

LABARIN AURENAWhere stories live. Discover now