MATAR MIJINA

850 54 0
                                    

❣❣ LABARIN AURENA❣❣

Nah
      Khadijah Ahmad

    

                  91-95

    "Ban hanaki shan ruwan lipton ba, Meyasa kike son b'atamin rai ne?" ya k'arasa maganar cike da damuwa, sunkuyar da kai nai, hawaye ya cika min ido,  numfashi ya fursar ya zagayo ta bayana na zama a tsakiyarshi ya zuro da fuskarshi ta wuyana
  "Kinsan bansan kuka ko," yatsun sa ya saka cikin sumar kaina bakinsa daidai kunnena cikin maraitacciyar murya yake magana
  "Hearty u r d cause of ol dis nine ya kamata na shiga wani hali ba ke ba, ke murna ce ta kamace ki, ya kamo sangalalen hannuna, kingafa yacce kika koma meyesa hearty uhm, shafo fatar k'irjina yayi look hatta ga nan se da ya fad'a"  kuka nane ya 'karu

"Shhhh.." Ganin bazan daina ba ya had'e bakinmu gu d'aya ya shiga kissing d'ina tenderly wanda yasani manta wani damuwa"..

   Please hearty kada ki ke zama da yunwa ko da daddare ne kika ji yunwa ki nema ba kice saida safe ba na ajiye miki ruwa da flask na ruwan zafi kayan tea na kan centre table duk a gefen gadon uhm?" Gyad'a kai nayi ya bani peck a fuska "saida safe"

  "Allah ya kaimu" ya fice, har  zan sa key ya bud'e" and again dan Allah karki saka wannan zulumbuwar  rigar gobe" dariya nayi had'e da girgiza kai, zai juya nace "wait,"tare da manna masa sumba a fatar baki, har cikin zuciyarsa yaji dad'i kar kibar key a jikin k'ofar kar nazo kina bacci, "ok" ya fice, na koma  kan kujera na zauna bayan na kunna akwatin talabijin dan kallon tauraran d'an adam, wuraren goma da rabi na kashe komai na nufi d'aki kwanciya raina fal farinciki bama idan na tuna irin soyayyar da muka zuba yau da yamma wacce muka jima bamuyi irin ta ba.

~
  Ta 'bangaren zamana da Aneesa ba matsala saidai tun lokacin da ta cika wata guda ta fara canja min, har yakai batason taga Najib tare dani ko yayi zancen wani ikon Allah kuma shi Najib a lokacin sai ya koma komai ni, ya manne min har cemasa nake kai wai kamar bame mace biyu ba, yakan yi dariya yace ni MIJIN MACE 'DAYA(rufaida omar)ne kuma kece, ke Aneesa fa sai ta canja min duka a da lokacin da aka kawo ta nakan danne kishina na je wurin ta muyi yar hira wacce ita da kanta tayimin magana kan cewa bana zuwan mata, amma yanzu idan naje ma da sagaggiyar gwiwa nake dawo wa dan kallon arzi'ki bana samu, da abun ya isheni nayiwa Najib magana ta'be baki yayi yace
"kunfi kusa"

   A kwana a tashi ciki ya bayyana jikin Aneesa zo kiga murna wuri na  mama kuwa har sadaka tayi saidai abun mamaki shi uban gayyar ko ajikinsa wai an tsikari kakkausa, dana sameshi nayi masa magana kan abinda yake baya dacewa gwasaleni yayi ban damu ba saboda inda sabo na saba indai kan Aneesa ne haka yake min, cikin Anesa mai kwad'ayine tsirfa kala kala, dan haka kullum cikin aike nake in kuwa abun ya juyo mata har su pizza takeso kuma tace home made haka zan wuni a kitchen sai ya zamana na daina samun time d'in kaina har ma da na mijina wanda ke wata uwa duniya aiki, ko da yazo gari ma mama bata barin mu tare sai tace muje sashen Aneesa koda zata buk'aci wani abu,. Akwai wata rana da hearty zai dawo daga lagos kamar yacce na saba na shiga had'a masa delicious abincika dana san yafiso na tsala uwar kwalliya na hakince a falo banfi minti biyar da zama ba saiga kiran mama wai nayi maza nazo sashen Aneesa a rikice na fita ina shiga tace
  "Yawwa zauna ki matsa mata k'afa wai ciwo take mata" da sauri na d'ago kai ina kallon mama,
  "A a yakika tsaya yi maza mana", zamana keda wuya mukaji 'karar motar Najib, wucewar mintuna ashirin sai gashi..wani irin kallo yake bina dashi me wuyar fassarawa saidai kana kallon kwayar idonsa kasan tashin hankaline kwance cikinsu,

  "Ga auta ga auta, sannu da zuwa ya hanya", numfashi yake tun karfi kan ya ansa ya dawo da idonsa kaina ke tashi anan" ya fada a tsawace!

  "Bangane ta tashi ba bakaga abinda take bane?"

  "Nagani mama shiyasa nace ta tashi,"

   "To isashshe nice nan na sata,"

   "Ki tashi nace!!" A firgice na tashi, maganar Aneesa ce ta dawo damu
  "Wash Allah mama 'kafata", mama tashiga tafa hannu

LABARIN AURENAWhere stories live. Discover now