14

136 12 0
                                    

*BAKIN ALK'ALAMI✍🏻*
_(Cigaban AMINTAKA...)_

*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*

_Vote_Follow me on Wattpad@Aneelurv_

14

    Shiryawa sukayi tareda yiwa auntynsu Amal bankwana zasu tafi gida.
   Sam Amal bata son tafiyar yan matan saboda sabon da sukayi na kwana biyu, musamman Anisa da ba kusa take ba.. 
    Haka itama ta sunkuyar da kanta kasa dan bata son hada ido da Amal dan batason bankwana.
   Kafadarta ta dafa tace Anisa zaki tafi kibarni da kewarki ko?
   Aunty zan kuma dawowa in sha Allahu..ta fada kasa kasa.
    Uhmm Allah yasa ta fada yayinda Areef yake saukowa kasa yana balle battles na hannun rigarsa.
   Arfat zaku wuce ne?
   Eh yaya Areef
     To muje na ajiyeku nima zanje office.
   Wata harara Amal ta watsa masa tace...ni zan kaisu kai ka je kawai saboda you are late.  Ta fada a takaice
    Murmushi ya sakar mata dan tun jiya yarasa gane kan princess nashi..okey no problem, ya bude brief case nashi ya mikawa Arfat wrapper na kudi masu yawa wandaita kanta bata san ko nawa bane, yace...kiba kawarki tayi transport.
    Angode yaya..Arfat tafada cikin sakin fuska.
   Anisa kuwa ko kallo bai isheta ba, dan ta kula da nema yake ya shiga gonar da bazai taba samun koda fure a cikinta ba.
    Amal ta shiryo ta fito tace masu oya ma dearest sisters muje ko.
    Ta kamo hannun Anisa tana janta ajiki saboda tana son yarinyar dan ta kula ta iya takunta..Anisa baki bani no ki ba har zaki tafi ko?.  
    Kai Auntyna wlh na manta nima inason naki ai..haka sukayi exchanging numbers
   Amal ta kaisu gida inda suka yi sallama da Anisa kasancewar gobe da safe zata wuce.
   Rabuwa babu dadi haka suka rabu.

***   ***   ***   ***   ***

     _ANISA YUSUF 'DAN-SARAI_
     Shine cikakken sunanta wacce aka fi sani da Classy, matashiyar yarinya yar shekara 19 a duniya, mahaifinta Alh Yusuf 'Dan sarai babban attajiri ne a jihar kaduna, ita kadaice wajen iyayenta, gata gaba da baya ta samu, saidai kash...miskilace ajin gaba hakan yasa frnda nata suke kiranta da classy, wayayya ce sosai ga ilimi da kokari both boko da islama, hakan yasa ta shiga ran family nata, aminiyar Arfat ce sosai tun suna sch, kuma tanada hakuri da kawaici, mahaifiyarta hajiya Aysha Allah yayi mara rasuwa yayinda ta haifeta, dan bata san mamanta ba.

     Amal ta dawo gida ta samu Areef ya dawo office yayi zugum, tamkar wanda akayiwa mutuwa.
   Prince meke faruwa ta karaso wajenshi taku dai dai..
   Princess wlcm back ya fada yana goge wani irin zufa da yakeyi tamkar wanda aka watsawa ruwa
    Baki ta bude tace..ah baby a.c bayayi ne?..cire rigan mana muje ka watsa ruwa..ta shga cire masa kayansa, jikinsa duk ya saki.
   Ta kama hannunsa zuwa bathroom...cikin zinc ta saka shi tareda hada masa ruwan wanka, ta koma ta cire kayanta tareda fadawa cikin kwamin wankan suka cigaba da wanke junansu duk a lokacin kalkonta yakeyi...yana yake..
    Suka fito ta goge masa jikinsa tareda murza masa dan mai da fesa masa diffrnt perfumes daddadan kamshi ya gauraye dakin, kallonta yakeyi shidai duk yanda ta sarrafashi haka yake binta amma sam hankalinshi ya karkata ga tunanin Anisa.
    Kana nan kaya ta saka masa ta zaunar dashi sannan ta hau shirya kanta yana binta da kallo yanda ko wane sashi na jikinta yake rawa saboda babu komai a jikinta banda towel.
   Gashin kanta ta hau gyarawa ta maidashi bangare daya tana kallon yanda yake satan kallonta ta mirrow...murmushi ta mayar masa tace hmmm.
    Haka ta shirya cikin riga da sket tareda maido hankalinta kanshi tace...yallabai back to u, meke damunka?
    Baby ba komai fa
     Yaya Areef...ta kira sunansa cikin kakkausar murya tareda daure fuska...wlh bazan lamunci wannan rayuwan taka ba, dan kana son yarinya shikenan Amal tazama hoto a wajenka ko?
    Kallon mamaki yake mata ya kada mata kai tamkar yaron goye yace Amal wlh ina sonki kuma na aminta dake, inason Anisa Amal pls bana son na rasata pls.
    Hmmm ta mike tsaye tace to Allah ya taimaka ta fice zuwa falo.
   A daddafe ya tashi ya bita..a gabanta ya durkusa yace..Amal idan na bata maki rai kiyi hakuri ke kadai nasan zan samu sassauci a gareki kuma kika bukaci da nasanar dake damuwata.
    Kafa ta dora daya kan daya tace...okey tareda maida hankalinta ga kallon da takeyi na koreans film wato KILL ME HEAL ME!.
   Amal i cant do without u tamkar maraya haka nakeji na duk ranar da kika canja mun fuska, kiyi hakuri kinji my princess..ya fada a marairaice.
   Anan ta maido hankalinta gareshi ganin yanda ya damu sosai, tausayinsa ya kamashi.
   Hannayensa ta kama tareda fadan..mike kazauna kusadani my king, am really sorry pls i don wanna hot yhu, kawai halayyanka na baya nake tuna amma kasawa ranka Anisa tazama kanwa agareni kaikuma kazama angon Anisa.
   Dadi ya rufeshi baisan lokacin da yayi mata wani irin hot kiss ba tareda hugging nata...nan take suka canja akalarsu zuwa wata sabuwar alkibka ta masoyan juna...wo ho ho so hana ganin laifi...nikam anan na daga alkalamina na tsaya chak nace Allah dai yabar kauna...lolx

Urz Aneelurv💕

BAKIN ALK'ALAMI(Cigaban AMINTAKA...)Where stories live. Discover now