34

142 13 0
                                    

*BAKIN ALK'ALAMI✍🏻*
_(Cigaban AMINTAKA...)_

*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*

_Vote_Follow me on Wattpad@Aneelurv_

34

    Buga daya kuwa yayi tashiga...kallon wayan tayi ta tabe baki tareda kauda kanta, dan yabata mata rai.
    Wajen zama yasamu ya cigaba da kira tareda tura mata sakwannin ban hakuri amma sam tayi burus dashi.
    Salim ne ya dafa kafadarsa bayan sallama da yayita yimasa bai san da zuwansa ba.
   Cikin razana ya juyo yace...ah abokina saukar yaushe?
   Mamaki yakama salim ganin yanda areef ya lalace ya canja kwata kwata...Areef meke damunka ko duk jinyarce?
   Uhmmm bari kawai muje ka ganta ko?
   Oryt muje suka isa dakin da su hajiya mama da arfat suke.
    Arfat ce a gefen gadon Amal tana bata hollandia ganin ta farka ance abata luquid abu.
   Laaa yaya salim sannu da zuwa...arfat tafada cikin zakuwa...kasancewar rabon da su hadu tun ranar partyn ta da sukayi agidan areef.
   Yauwa kanwarmu...ya mai jiki fa?...ya fada yayinda yake maida kallonsa ga Amal sai tausayinta ya kamashi...
   Sannu Amal...ta bishi da ido saboda bata iya magana.
    Kallo daya hajiya mama takuma yiwa areef yakara ja baya kusada kofa dan sam yasan irin kallon da takeyi masa...tuni areef yafita aranta.
    Hajiya mama inayini...salim ya durkusa tareda gabatar da gaisuwa...ya maijikin?
   Lafiya kalau Salim ta amsa fuska a daure dan gani takeyi duk halayyarsu daya ce.
   Allah yakara mata lafiya.
    Amin...ta amsa a takaice.
    Juyawa yayi zaifita Amal tabishi da kallo cikin tausayawa yasake juyowa ya kalleta sai yaga tana zubar hawaye.
   Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya fada tareda kokarin maida hawayen dake shirin kwararo masa saman kumatunsa ya fice...
   Areef ne yabi bayansa cikin 'yan kame kame yana abokina kaga yanda Amal takoma ko?, duk ta rame tasawa kanta damuwa babu gaira babu dalili, ni narasa ganewa Ama....dakata da Allah!!!
     Salim ya dakatar dashi cikin bacin rai...Areef kaji tsoron Allah, kuma wlh kaguji haduwarka da ubangijinka, me Amal tayi maka haka har yazamto takamu da ciwon zuciya?, Anya kanada imani kuwa?, waima meye musabbabin ciwon Amal?, yarinya mai natsuwa hakuri da sanin ya kamata?...tir da halayya irin taka Areef, baka daukan shawara yanzu ka gogamun kashin kaji kadubi irin kallon da hajiya mama takeyimun...banji dadi ba wlh...ya karasa maganar yana goge hawayen dake kwarara a fuskarsa...sai anjima ya fada tareda tafiya inda yayi parcking motarsa.
    Galala Areef yayi yana mamakin kalaman salim, sam ni banga abinda nayiwa yarinyar nan ba, waima mesa mutane basa tunanin cewa Amal yar uwata ce...uhmmm yafa aransa tareda sake samun wajen zaman dan lalubar Anisa.
    Yauma baiyi nasarar samun ta ba...dan kuwa takashe wayarta baki daya...lallai babe kina tym zaki nemeni yafada aransa yayinda yake kokarin maida wayar a aljihun gaban rigarsa.

***   ***   ***   ***   ***

     Kullum cikin kuka da tunane tunane wanda yasa har tafara ramewa kasacewar bata iya cin komai...
    Anisa zo inason magana dake...yafada yayinda yake daga labulen dakinta ya wuce baijira ta amsa masa ba.
   Wajen zama yasamu tareda cewa...yaa Allah...
     Fitowa tayi kai ko hula babu balle mayafi...riga ce wacce ta kama jikinta sosai ta bayyana kirar boobs nata wadanda ko bra bata sa masu ba...da wani mini sket iya guiwa ta fito gashin kanta duk a tashe tamkar wacce akayi damben tsiya da ita...baki ta zumbura yayinda take kokarin zama kusada mahaifin nata...dady gani cikin wata irin sarkakkiyar murya mai kama da ta mai mura.
    Hmmmm...yaja dogon numfashi yace Anisa kina lafiya kuwa...kiduba yanda kike fa...kinsan cewa so ba hauka bane ko?, yanzu duk soyayya da gatan danake nuna maki zan yakiceshi nabaki kashin tsiya idan baki natsu ba...ki kalla jikinki haka kike zomani idan nakiraki?
    Dire dire da kafafunta takamayi cikin shagwaba takuma fashewa da wani sabon kuka...
   Bakin ciki yakuma ruruwa aransa tareda danasanin sangartar da yayiwa yarinya....
   Oya get up...jeki nafasa maganar dake idan kin shirya kyazo ina jiranki...ya mike tareda ficewa daga falon ya nufi back yard don shakatawa.

    Wayarta ce takuma ringing ta juya taga MY KING wato Areef....mtsw taja dogon tsoki tareda picking..
    Ina jinka...ta fara dashi
   Toooo baby yaukuma menayi akeyi mani wannan horon?..ya fada daga dayan ban garen.
    Malam kafadi abinda ke ranka inada abinyi.. Tafada a daddafe kasanewar itama ba karamin kewar guy din tayiba kawai tanayi ne dan tarama shima yaji irin radadin da zuciyarta takeji saboda soyayyarsa datayi mata shiga ta bazata.
    Hmmmmm kawai yace yayi hanging call din.
   Damn!!! Gabanta ya fadi bayan hello hello da tayi taji shiru.

Drp ur comments please!

#TeamAreef
#TeamAmal
#TeamAnisa

Urz Aneelurv💕

BAKIN ALK'ALAMI(Cigaban AMINTAKA...)Onde histórias criam vida. Descubra agora