The herdsmen daughter

9.4K 424 3
                                    

BELEL;

K'auye ne kamar ko wanne cike da ahali iri daban daban d'auke da dabi'u iri iri, sedai duk da banbancin da suke da shi akwai abu d'aya da sukayi tarayya a kai wanda shi ne zaman lafiya, kamar dai ko wanne gari walau birnin ko k'auyen akan samu ahali mabanbanta wad'anda basu jituwa ko dai saboda matsayi ko kuma muk'ami.
Mafi d'aukar hankali cikin k'auyen wasu ahali ne guda uku mabanbanta a matsayi da kuma yanayin tafiyar da rayuwa. Wannan labari ya fara ne daga zuciyar Wannan k'auyen wanda ya kasance shine mazaunin wani katafaren gidan sarauta mai cike da gargajiya da aladu, Masarautar da babu irin ta a wasu k'auyukan na k'etare.
Daga wani b'angare na k'auyen akwai wani ahali wanda ya kasance shi na daban ne, jagora a wannan k'aramin ahali ya kasance *makiyayi* ne mai kiwon dabbobi kamar yadda kiwon ya zama gado ne gare shi haka ma ga iyalan shi sedai duk da ana musu kallon masu zama cikin lumana an gaza gane cewa cikin ko wanne ahali akwai nasu b'oyayyen k'aramin sirrin sannan kuma kowanne zai kasance yana da nashi irin burin da yake son ya cika, walau na fansa ko dai na soyayya ko ma akasin hakan. Labarin ya fara ne da ................

Layla
Iskar bazara ke hurawa da k'arfin gaske hakan yayi sanadiyyar zubewar ganyayyaki daga rassan bishiyoyi dake cunkushe birjik. Waje ne kamar daji.
Gabas ta nufa da dabbobin yayinda rana ke b'ullo wa hakan ya sa idanuwan ta lumshewa sannan Iskar tana k'ok'arin yaye mayafin da ta rufe kanta da shi, k'aran da ta jiyo daga bayan ta ne ya rikita ta gaba d'aya ta kasa motsa wa sai dabbobin ta wad'anda k'aran ya sa duk suka rikice suka kasa nutsuwa, ba na farko ba kenan da ta tab'a jin Wannan k'aran ,k'aran mota ne wad'anda ake amfani dashi a gidan sarkin garin kuma yana da su iri daban daban duk da yawanci takan ji k'aran ne bayan sati sati Idan Sarki ko wani daga iyalan sa zai fita.

Teet! Teet! Motar ta sake k'ara a karo na biyu. Daga gani wanda ke zaune gefen matuk'in ya kwankwad'i boko ya k'oshi domin shigar sa ma kad'ai ya isa yin bayani. Jaridar dake hannun sa ya rufe fuska a dak'ile yayi tsaki cike da hasala yace "Filthy humans! Duk inda bak'auye yake sai ya nuna halin sa especially wad'annan gidadawan makiyayan da su da dabbobin su sam basu da banbanci!"

Shiru driver yayi ya girgiza kai.
Tun da mahaifin shi ya fara magana
*Suraj* Bai ce komai ba illa sak'ale kanshi da yayi ta window yana kallon how desperate mai kiwon ya zama hakan yasa ya bud'e motar ya fito ya tinkari inda mai kiwon yake tsaye.

Dad ba shiri ya zare gilashin idanuwan shi ya ce "what the hell is he trying to do or has he gone insane?" Driver dai bai ce komai ba se Murmushi da yayi yayinda ya cigaba da kallon Suraj wanda bai fi saura taku shida tsakanin shi da mai kiwon ba.

A garin tirka tirka da dabbobin ke yi d'aya ya buge ta, kad'an ya rage takai k'asa bata ankara ba taji Mafi k'arfin rik'o ya tarbe ta wanda hakan yasa tayi k'ok'arin rik'e abunda ya rik'e ta tun k'arfin ta saboda tsoro kuwa duk ta k'ank'ame idanuwan ta.
Cikin dak'ik'ai uku zuciyar sa ta tsaya chak kamar daskararriyar k'ank'ara, jinin jikin shi ya daina gudana for a moment ya manta inda yake ya b'ata cikin wata duniyar ta daban.
Zagayayyen fuska gareta ma'abocin haske, gashin girar ta cikakku ne wanda tsabar yawa har sun had'e tana da hanci siriri madaidaici ga kuma kyawawan lab'b'a masu kama da kunnen furen rose, abu Mafi d'aukar hankali shine idanuwan ta bayan ta bud'e su wad'anda suka kasance Emerald green wanda abu ne Mafi wuya ka samu irin shi a irin wannan nahiyar in dai ba had'i da bature ko dai balarabe ba, abu na biyu Mafi Jan hankali shine gashin kanta da ya kasance ja, babu makawa akwai wani abu na musamman tattare da ita. Da k'arfin tsiya ta fisge kanta daga rik'on da Suraj yayi mata ta fara k'ok'arin kad'a kan dabbobin domin ta bada hanya. Tayi nisa sosai kafin ta juyo karo na farko ta sakar masa da tsadadden murmushi sannan ta cigaba.

Shafa kansa yayi yana Murmushi k'asa k'asa kuma yace "does that means thank you?"
K'iran da Dad yayi mishi ne ya sa shi komawa mota yana Murmushi.

A fusace Dad ya juyo ya dube shi kafin yace " mesa kayi haka? Why did you help her?"
Baki sake Suraj yace "Dad she was desperate and out of idea ko dabbobin ma duk sun rud'e ai ban ga laifi a ciki ba don na taimaka mata."

Dad ya dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hannu sannan yace " look! I don't care if she's desperate, all that matters is that ita talaka ce kuma Mafi k'azanta cikin talakawa she's no match for us, you can't even trust such peoples, tsakanin mu da su shine su mana bauta mu taka su yadda muke so su basu kasance komai a garemu ba face k'ask'antattu"

Idanuwan Suraj sun nuna bai ji dad'in kalaman mahaifin shi ba amma yasan Dad ba irin mutanen da za'a yi wa titsiye bane a sha'anin su ,don haka bai ce k'ala ba amma da ka ganshi kasan Lallai ranshi ya b'aci....

Isowar ta gida ta kora dabbobin zuwa garken su sannan ta ruga a guje tana dariya tayi cikin daji wanda ke gefe da gidan su kasancewar gidan su yana nesa daga sauran gidajen k'auyen. Bakin wani tafkeken kogi ta tsaya ta zame kayan jikin ta gami da afkawa cikin sassanyar ruwan tana ta watsa wa tana dariya.

"Laila! Laila!! Wata y'ar budurwa wanda bazata wuce sa'ar ta ba ta nufo inda take da gudu amma maimakon ta shiga ruwan zama tayi bakin ruwan tana kallon *Laila* wanda tayi zurfi cikin nata duniyar tunanin.

Tab'e baki yarinyar tayi kafin tace "wai kam kin yi hauka ne? Ke kad'ai se dariya kike yi? Ki fito ki raka ni"

Da sauri Laila ta fito tana dariya ta kama kafad'un k'awar ta tana jijjiga wa yayinda k'awar ta saki baki dalala tana kallon ta har saida ta gama kafin k'awar ta rik'e kunkumi tace

"Yanzu kam ina matuk'ar buk'atar k'arin bayani, domin gaba d'aya kin fita hayyacin ki sai kace wanda ta fad'a soyayya?"

Laila dake zaune tana jefa dutse cikin ruwa ta fisgo hannun k'awar nata har saida ta tsorita gami da zauna wa gefen ta babu shiri tace "Kin chanka daidai !!! Na fad'a soyayya ne Zubaina" Zaro ido Zubaina tayi tace "haba de k'awa ta? Waye shi?"

Kallon ta Laila tayi gami da girgiza kai ta ce " Nima ban sani ba amma de tabbas ko ma waye shi ya tafi da zuciya ta, ji nayi kamar in bi shi mu tafi tare na musamman ne shi .!"

Gyara zama Zubaina tayi hannayen ta cikin na Laila cike da zumud'i tace "fad'a min ya kamannin sa yake? Nasan kyakkyawa ne"
Murmushi Laila tayi ta dubi Zubaina kafin tace "ba kyakkyawa ba in takaice miki shi mak'uran kyau ne, ma'abocin tsayi yadda kika san zaki haka yake da k'arfi duk da ma ban taɓa ganin zaki ido da ido ba se a labarai, k'amshin jikin shi kad'ai ya isa Jan hankali".

Baki a sake Zubaina tace wad'annan suffofi haka se kace aljani? Yo ai naga ko Suleiman da ya kasance wanda ya kere mazan k'auyen nan a kyau bashi da wad'annan suffofi!" Tsaki Laila ta ja
"Mtsew ! Ana maganar gwarzon namiji ma'abocin kyau da tausayi me zai kawo maganar wancan tankwasasshen?" Tashi muje in raka ki kafin Inna ta neme ni"

A tare suka mik'e suka nufi cikin gari........


ƳAR MAKIYAYANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ