the Brothers

3K 199 2
                                    

Yanzu de Mun ji takaitaccen tarihin Sarkin Belel, yadda d'an uwansa Omar Mammadou ya hau dokin zuciya ya bar gida sannan Mun ji yadda Yerima Ahmadu da Yerima Abdul-malik
suka banbanta bisa halayen su yanzu kuma cigaban labari zai soma.

***** ****** *****

K'asaitaccen falo,makeken gaske cike da kayan k'awa, zaune ya hango shi cikin sutura ta sarauta. Ba tare da b'ata koda second ba ya k'arisa gaban sa ya zube gami da kwasar gaisuwa.

Da taste of royalty Mai martaba ya d'ago kai ya dubi *Abdul-malik* ya ce "Naji labarin wannan karon baka taho da Mahaifiyar Surajo ba, ina fata ba wata matsala?" Sosa k'eya yayi kai a k'asa ya ce "Tana Cairo, y'ar uwarta babu lafiya shiyasa na barta a chan amma komai lafiya." Kai mai Martaba ya jinjina kafin ya sake wata maganar Suraj ya shigo

"Grandpa!" Ya fad'a yana dariya mai martaba yana son Suraj matuk'a gashi kuma kaf cikin jikannun gidan shine k'arami Kasantuwar akwai yayin sa y'ay'an Yerima Ahmadu kawun sa wanda suka had'a da *Abubakar, Ameer, da Saeed* Ameer ne k'arami kuma miskili, akwai shi da had'a guri,da gulma, Saeed shine na tsakiya halinsa d'aya da K'anin baban sa watau Abdul-malik ya k'i jinin talaka da talauci. Abubakar kasancewar shi babba babu ruwan sa tamkar mahaifin sa Ahmadu.

Suraj yana k'arisa wa ya kwanta kansa a cinyar mai martaba tuni suka shiga hirar su mai ban sha'awa ta kaka da jika Abdul-malik kuwa ya gaji da zama dan haka ya mik'e yayi sallama da maimartaba ya fice.

Nan Suraj ya gyara zama yana bawa kakan shi labarin yadda tun shigowar su Belel Dad yake ta masifa wai don ya taimaki wata Yarinya, ko kad'an mai Martaba bai mamaki ba don yasan halin Abdul-malik. Haka suka cigaba da hirar su har lokacin cin abinci yayi suka ci sannan Suraj yayi sallama da Kakan shi ya shiga cikin gida, kai tsaye b'angaren uncle Ahmadu inda ya tarar da shi zaune kan doguwar kujera suna hira, da Murmushi ya k'arisa ciki ya duk'a gami da kwasar gaisuwa, cike da farin ciki suka amsa Uncle Ahmadu ya jawo shi jiki yace
"Sai yanzu hirar ta k'are da mai martaba kenan, very well! It's good to have you here son, Yaya Ummin ka take ? Naji ance bata zo ba Wannan karon, hope all is well?"
Kai Suraj ya gyada sannan ya amsa da "eh lafiya lau kawai tana jinyar sistern ta ne shiyasa bata zo ba amma zata taho daga baya". Kai kawai Uncle Ahmadu ya jinjina gami da fad'in "Allah ya bata lafiya" duk suka amsa da Ameen.
Ya dad'e sosai a nan ma kafin ya buk'aci a kaishi wajen y'an uwanshi Kasantuwar basu had'u ba tun zuwan sa, haka kuwa akayi wani security ya yi leading hanya inda suka bar side d'in Unclee zuwa wani dank'areren side daban , tafiyar akwai rata dan haka mota suka shiga zuwa side d'in inda maigadi ya bud'e musu k'ofa cike da girmama wa motar ta kutsa kai bata tsaya ba se bakin entrance da zai sada mutum da cikin first flat, bai ko rufe k'ofar motar ba ya tsaya gami da bud'e hannayen shi ya d'aga kai sama gami da rufe idanuwan shi yana mai shak'ar sassanyar Iskar dake busawa a tsanake kana yana sauraron dad'ad'an kukan tsuntsaye masu tsuma rai ,a nan fuskar ta ya fara dawo masa, ji yayi kamar ya tsaya a haka iya tsawon rayuwar sa.

Tun fitowar Suraj yake tsaye hannu nad'e a k'irji yana kallon sa, saida ya k'are masa kallo sannan ya juya da gudu ba tare da yayi magana ba ya koma cikin falo inda ya zube rigijib kan kujera hakan yasa wayar hannun Saeed ta zame ya d'ago a fusace cike da hasala yace

"God damn it Ameer! Kai daga gulma ta ci ka gaba d'aya se ka zama tamkar mahaukaci you can't even behave like proper prince!"
Ameer ya kwashe da dariya harda rik'e ciki kafin ya had'a hannayen shi biyu yace "Sorry! Am so sorry wallahy wani abu ne ya ban dariya ka ma san wa na gani kuwa?"

Abubakar dake fitowa daga wani d'aki yana rik'e da k'aramar yarinya da bata fi three years ba yace
"kai daman kana rasa gulmar yi ne? Mutum bashi da aiki se gulma kai ba mace ba" yana kai nan ya haye kujera ya zauna gami da d'aura yarinyar kan cikin shi yana mata wasa. Saeed ya dubi Ameer dake tab'e baki yace "ina jin ka, da wacce ka zo kuma?".

Gyara zama Ameer yayi sannan yace "Yau kam Mun yi babban bak'o". Daga Abubakar har Saeed suka had'e baki wajen fad'in "Waye?".

"Crazy prince mana! I mean Suraj, yana chan waje ya tsaya ya rungume iska ya rufe idanu se Murmushi yake am scared haukar sa tafi ta da."

Murmushi kawai Saeed yayi Abubakar kuwa wasan sa yake da yarinyar tana ta kyalkyala dariya bai ma maida hankalin sa ga labaran da Ameer ke bayar wa ba.

A yanda yake tsayen wayar shi tayi ringing daga cikin aljihu hakan yayi distracting yanayin da ya shiga ,y'ar tsaki ya sakar kafin ya d'auko wayar yaga Oummin shi ce Razia dan haka ya k'i d'aga wa ya kutsa kai ciki....

ƳAR MAKIYAYAWhere stories live. Discover now