the beginning!

3.7K 234 0
                                    


  Duk Mun ji farkon had'uwar Suraj da Laila ,sun kasance mutane ne biyu mabanbanta a matsayi da yanayin rayuwa ,sannan mun ga tsananin k'iyayyar talauci da talaka dake shimfid'e a fuskar mahaifin Suraj, will the impossible happen?" There's only one way to find out!.

*****         *****        *****

   A tsanake motar ke tafiya Suraj kan shi na waje ya lumshe idanuwa yana feeling yadda iska ke kad'a wa cike da burge wa ,ga kukan tsuntsaye masu dad'in sauraro da ke dukan kunnen shi. Ita kad'ai yake gani ko da ya bud'e idanuwa, Murmushin ta, that smile that melted his heart! Ya kasa manta fuskar kuma baya fata ya manta ko daidai da na rana d'aya. 

Duk wannan tunani da yake yi Dad banbami yake wai kawai don ya yi taimako a hanya kuma ma talaka.

   Motar bata gama Tsayawa ba Suraj ya bud'e k'ofa yayi tsalle , jacket nashi a hannu ya ruga da gudu cikin katafaren gidan sarauta da ke fuskantar su  baki kawai Dad ya sake kafin yace

"all this while ina ta magana ko saurare na baya yi, dubi yanda yake behaving kamar wani bagidaje he can't even act like a Prince."

Yana kai nan wani ya bud'e masa k'ofa gami da mishi iso, cike da fankama da k'asaita ya fito daga motar ba tare da ya amsa wa Mutumin ba ya kutsa kai sashen mai Martaba wanda ya kasance mahaifin shi kuma kakan Suraj.

   Kasaitaccen falo, makeken gaske cike da kayan k'awa ,zaune ya hango shi cikin sutura ta sarauta  ba tare da b'ata ko da second ba ya k'arasa gaban sa ya zube yana kwasar gaisuwa

'''Kafin mu cigaba zai fi kyau musan asalin tarihin Sarkin Belel, kasancewar shi kaka ga  Suraj'''

    Kowacce Masarauta burin ta bai wuce mai mulkin ta ya kasance adali kuma abin alfahari ga al'ummar ta, haka ne ya kasance a wannan K'auye, gari ne wanda ya tashi tun asali ba tare da sanin komai ba na rayuwa wanda ya wuce kiwo noma da Su watau kamun kifi zaman lafiya kuwa sun d'auke ta tamkar ibada Mutum d'aya ke fad'a a ji a garin nan kuma ba kowa bane illa wani tsohon dattijo Halliru Mammadou ya kasance abin kwatance har ma a makwabtan k'auyukan ganin kyawawan dabi'u da tausaya wa na k'asa da shi hakan yasa manyan gari suka zab'e shi a matsayin Sarkin su hakan ya janyo hatsaniya mai rikitar wa tsakanin Halliru da d'an uwansa *OMAR* wanda shi ma babban burinsa bai wuce ya zama mai mulkin Belel ba ,an sha gwagwarmaya kafin daga bisani Omar ya hau dokin zuciya ya bar gida tare da matar sa Ramatou Allah kad'ai ya san inda suka shige , tun *Halliru Mammadou* yana cikiya har ya gaji , bayan an nad'a shi sarkin Belel da Watanni uku Sarauniya Aminah ta haifi d'an ta na fari *Yerima Ahmadu* bayan shekaru biyar kafin ta sake haifo na biyu *Yerima Abdul-malik* ,

    Su biyun a dabi'u da halaye sun banbanta , kamar Mahaifin shi mai martaba *Yerima Ahmadu* ya kasance mai son jama'a da taimakon talaka sedai *Abdul-malik* akasin hakan yake , a wajen shi talaka ba komai bane, kuma basu chanchanta a yarda da su ba. Da wannan dabi'u suka girma kuma Kasantuwar suna da mabanbanta halaye ba kasafai suke jituwa ba abu d'aya ke ci wa *Abdul-malik* tuwo a kwarya kuma ba komai bane illa yadda bashi da ikon fad'a a ji Idan har *Ahmadu* ya yanke hukunci Toh ya zauna.

    A haka suka cigaba da rayuwa har Akayi bikin
*Ahmadu*  da  Maryama D'iyar sarkin Madagali. Shi kuwa *Abdul-malik* ya zab'i ya tafi ya k'aro ilimi na zamani, Sarki bai hana shi ba illa saka masa Albarka da yayi.

   Shekaru  biyar kenan da tafiyar *Abdul-malik* karatu a Cairo ya dawo tare da wata kyakkyawar balarabiya da sunan ita zai Aura, hakan ya jawo cecekuce tsakanin sa da iyayen shi Amma daga bisani suka amince. Saida ta shekara biyu tana shanye gori da zage zage na dangi kafin kwatsam ta sami ciki, bayan wasu Watanni ta haifi d'an ta son kowa  k'in wanda ya rasa. Ran suna yaro yaci suna  *Suraj*.

       *Suraj* yana da shekaru uku *Abdul-malik* ya d'auki matar sa  *Razia* suka koma Egypt domin ya samu kyakkyawan educational background amma duk wani Hutu a Belel suke yin sa Kasantuwar yayi alk'awari wa mai martaba duk wani holiday zasu dawo. Wannan karon *Suraj* ya kammala karatun sa ne baki d'aya inda ya karanci architecture a jam'iar New York wato (NY university ) dake K'asar Amurka.

   *Suraj* ya kasance  mai son jama'a akasin mahaifin shi Abdul-malik, shekarun sa ashirin da uku ne a duniya 23yrs  gashi mai kwazo, ga kuma uwa uba kyau bashi da kyamar d'an Adam kamar mahaifin shi all credit goes to his mother Razia da ta tayar da shi da kulawa ta nuna mishi Cewar bashi da banbanci da talaka they all are humans.

'''Wannan kenan takaitaccen labarin Sarautar Belel da kuma asalin Suraj'''

     This is just the beginning!

ƳAR MAKIYAYAWhere stories live. Discover now