41

721 49 0
                                        

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

    *SA'EEDA MUSA DAUDA😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*


*BESTORED TO MY LIL SIS* ''' SUMAYYAH MUSA DAUDA'''


                       4⃣1⃣

murya na rawa Suhaib yace" da....d i'm so....... ry for causing all tro........bles for....... forgive..... my....... sins".
      Wani irin marin da yafi wanda mum ta mishi da ya sakar mishi a kuncin shi dan sai da Suhaib ya saki wani irin razanannen k'ara a rud'e ya dafe kuncin shi yayin da jini ke ta b'ulb'ulowa a bakin shi.
     Dad kam koh a jikin shi ba tare da ya damu da halin da Suhaib yake ciki ba a tsawace yace" ashe baka da tausayi ban sani ba ?, da girman ka kuma da ilimin ka kake aikata abunda koh illiterates baza su aikata ba, a wani wujjah ka d'au Aysha ka kai ta gidan karuwai koh so kake ka gurb'ata mata rayuwa sannan ka b'ata mata suna a idon duniya ?
    ka sa an yad'a hotuna da videon baiwar Allah a idon duniya a matsayin karuwa duk wanda ya kalla sai dinka kallon ta da matsayin watsastiyar y'ar bariki shin ka san iya adadin tsinuwan da mutane ke ta jifan ta da shi bayan sun ga hotuna da videon?, ba ka tunanin wani yayi zina da ita a gidan karuwai da ka kai ta bayan barin ka wurin?
     Ina tunanin ka yaje da ka biye ma zuciyar ka ka raba yarinya da gida tiryan tiryan ka kai ta gida gidan karuwa anya kuwa kana tsoron gamuwar ka da Allah kuwa?, duk maganar da dad yake fad'a a haukace yake yin su cuz he is totally out of his senses.
    Hawayen dana sani ne ya fara zarya a eyes d'in Suhaib dan sosai maganar dad ya dake heart d'in shi a take nadama ya dirar mishi a lokaci d'aya.
    Kneeling da gwiwowin shi biyu yayi a gaban dad yana hawaye sharrr sharrrrrr a gaban shi tare da rik'e k'afofin dad da hannayen shi cikin muryar kuka yace" ka yafe min dad ban k'arawa wallahi sharrin shaid'an ne ya ingiza ni na aikata hakan please ku gafarce ni".
     A fusace dad ya hankad'a shi da k'afa yace" wallahi idan ka sake tab'a ni koh rigata ka tab'a sai ran ka yayi mummunar b'aci shashashan yaro kawai sakarai da bai san ciwon kan shi ba i felt like da bani bane na haife ka ba dan jinina bai da bak'in hali irin na ka so get lost on my site," dad ya k'are maganar yana fidda huci mai zafi deep inside him he really meant what he said.
    Kuka sharr sharrrr Suhaib yake yi a durkushe kamar k'aramin yaro amma babu wanda ya kula shi dan koh granny ma haushin shi take ji saboda abunda taji daga bakin dad.
    Da kyar ya iya rarrafawa da gwiwowin shi har ya zo gaban Aysha ya magiya yace" Aysha na san tun zuwan ki gidan nan nake ta cutar da ke har zuwa yanzu wallahi sharrin shaid'an ne ki yafe min y'ar uwata da yardar Allah hakan ba zai kuma faruwa ba".
     Koh kad'an Aysha bata ji d'arrrrr a ran ta ba, a zuciyar ta kuwa ta maimaita k'almar "y'ar uwa" shin ya manta sunan da ya saba k'iran ta da shi wato karuwa mai raba ma y'an tasha jikin ta ?, shine sai yanzu zai yaudare ta da dad'in baki a gaban dad ya k'ira ta da k'anwar shi bayan ta san irin karan tsanan da ya d'ora mata ba gaira babu dalili dan dai kawai wani *macucin* ya b'ata mata rayuwa ya d'irka mata ciki ba da son ran ta ba?
     kai Allah ya isa tsakanina da macucin nan bana jin duk sanda na gano shi zan iya yafe mishi dan na tsane shi matuka dan shine silar jefa rayuwata a hakan har yaya na kuma *macuci* yayi amfani da daman ya cutar da ni da irin tashi salon cutan,,
     lallai duniyar masu amfana da idanuwan su cike yake da macuta da yawa, me yasa da yawa lafiyayyu sake amfani da daman lafiyar da Allah ya basu sake cutar da nakasassu bayan Allah bacin ba su suka yi kan su ba ?,  abunda kenan take ta fad'a a k'asan zuciyar ta a fili kuma ta soma jan jiki da neman hanyar da zata tazo ta bar mishi wurin dan koh kusa da ita bata k'aunar yayi kamar hanya ya tsane ta a baya haka take jin tsanar shi a zuciyan ta, shi koh ya rik'e rigarta gammm ta k'asa yaki sakin ta sai pleading d'in ta yake tayi.
     Saurin tahowa wurin ta dad yayi ya ture Suhaib tare da rik'o hannun Aysha zuwa d'akin shi mum ta bi bayan su da sauri granny na ganin haka ta sab'i vail d'in ta tayi gaba aka bar Suhaib, Suhail da Jummai a wurin.
    Ganin ba su mum a wurin ya sa Jummai mik'ewa ta bar musu wurin ita ma,,
     Suhail na tsaye a jikin bene so shocked ba tare da ya taso ba dan jin cewa wai yau d'an uwan shi ne ke nadama a kan abun da ya aikata ?, a take yaji tausayin d'an uwan na shi ya kama shi koh da yake duk abunda su dad suka mishi a kan Aysha shi ya saya da kud'in shi,,
    duk da dai yana matuk'ar tausayin Aysha da kuma kishin ta amma hakan bai hana ya tunkaro d'an uwan shi ba, Allah sarki d'an uwa dad'i Suhail na isowa wurin shi ya rage tsawo shi kad'an ya d'ago Suhaib tare da rungumo shi jikin shi yana bubbuga bayan shi a hankali alamar lallashi,,
    Shi koh Suhaib tuni ya manta da wani rashin jituwa a tsakanin su ya hugging d'in shi back yana maida numfashi a hakali.
    Sun jima sosai a hakan kafin daga baya Suhail ya rik'o hannun shi zuwa site d'in su, suna isowa ya bud'e fridge ya d'auko mishi sassanyar bottle water tare da glass cup ya bud'e bottle d'in ya tsiyayo ruwan a cikin cup d'in hannun shi ya mik'a mishi.
     Amsa Suhaib yayi ya sipping d'in shi sau d'aya ya ture glass cup d'in gefe,,
     wani irin sanyin dad'i ne ya ratsa mishi zuciyan shi a lokacin da ruwan yake bin mak'ogoron shi dan sai da ya runtse idon shi a hankali yana mai jin wani sanyin ni'ima na ratsa shi,,
     k'asa hakuri yayi sai da ya sake d'auko cup d'in a karo na biyu ya k'afa a bakin shi sai da ya shanye ruwan tasssss kana yayi gyatsa ya dire k'ofin gefe guda ya zubo ma d'an uwan shi ido yana kallon shi can kuma yace" k'almomin baki na sun yi karanci da zan iya furta maka na ba ka hakuri, Suhail na san na k'untata maka and na san na making night d'in ka sleepless amma dan Allah ka yi hakuri ka yafe min sannan ka taya ni ba ma su mum hak'uri saboda na san suna fushi da ni matuk'a, yana fad'a wani silent tears ne suka soma bin fuskan shi,,
     Cike da tsantsar tausayin shi Suhail ya ciro hanky ya fara wipping mishi tears d'in cikin murya ta wanda ya mace a tausayi yace" stop all this tears bro insha Allah every thing will be easy tunda ka gano kurakuren ka, the biggest and
the most worsier mistake shine wanda mutum yayi laifi bayan ya realising kuma he kept on repeating it so don't you ever bother your self.
     I have to do bro dole ne na d'aga hankali na i'm ashamed of what i did, wallahi nayi dana sanin abunda na aika ma Aysha", Suhaib ya fad'a cike da takaici.
     Ha dai Suhaib yayi fad'a mishi dad'ad'an kalamai masu sanyaya zuciya har yayi nasarar cire mishi 56% na bakin cikin da ke ran shi.
      A d'akin dad kuwa lallashin Aysha dad ke ta yi mum na daga gefe tayi jugummm abun ta ta rasa me ke mata dad'i, duk wani kukan da Suhaib ke yi har k'asan ran ta take ji ta dake but ta bari as a punishment given to him saboda gaba.
    Sai da dad ya tabbatar da ya kwantar ma Aysha hakalin ta kana ya raka ta d'akin ta ya bar ta nan ya komo tashi d'akin.
     Da shigowan shi d'akin shi ya tarar da mum ta rafka uban tagumi da alama hankalin ta na wani duniya, magana ya hau yi mata amma koh kad'an bata ji ba balle ya sa ran zata amsa mishi sai da ya tapping d'in ta da hannun tayi firgigittttt ta dawo hayyacin ta jefi jefi tana sakin ajiyar zuciya.
    Tausayin ta ne ya kama dad dan babu uwan da zata so ace d'an ta yayi irin abun da Suhaib yayi, cike da tausayin ta ya rungumo ta ta baya yace" sorry for misunderstanding dear kaina ne ya d'au zafi da yawa har kika ga na fad'a mishi maganganun da na fad'a d'azu, har yanzu Maryam ke ta daban ce a cikin mata baki na baza su gaji da k'iran ki da suna sarauniyar mata ba, da fatan gimbiya zata min afuwa a bisa hukuncin da nayi gaggawan yankewa ba tare da nayi bincike ba".
    K'irk'iro murmushin dole mum tayi tare da d'ora kan ta a saman kafad'an shi tace" you are forgiven i knew are upset that's why".
     A haka dai suka bama juna hak'uri mum ta fad'a mishi dalilin da yasa ta b'oye mishi cewa d'an shi ne *macucin* a cewan ta wai saboda bata son hankalin shi ya tashi ne, daga nan ta kwashe kafffff abubun da Suhail yake ma Aysha ta fad'a mishi.
   Ba k'aramin tashin hankali dad ya shiga ba da jin abubuwan da suka faru da Aysha cikin hikima mum ta hau kwantar mishi da hankali har ya sauko.
      Daren ranar sai juye juye dad yake ta yi a kan gado sai tunanin mafita yake ta yi dan ya sha alwashin sai ya kwata ma Aysha y'ancin ta ta hanyar nema mata lafiya idan aka yi dace.
     B'angaren Aysha ma hakan ta kasance da throughout barci ya kaurace a idanuwan ta, duk juyin da zata yi tunanin *macucuta* biyu ne ke darsuwa a ran ta sai dabbbb goshin asuba kana ta samu ta runtsa.

       Bayan kwana uku da faruwan haka dad ya booking musu flight su uku shi, mum da kuma Aysha ba tare da sanin su ba ranar na yi jirgin su ya d'aga sai garin *MADINA* yayin da suka bar su Suhaib a gida Nigeria suna musu fatan samun nasara a zukatan su. 


'''Shin su dad za su yi nasarar abun da ya kai su Madina?
   Yaya makoman soyayyar Suhail a zuciyan Aysha idan ta gano cewa *macucin* da ta jima da tsanar shi zuciyan ta ne ya rikid'a ya koma masoyi ?
    Wai ina ya abdallah ? wani hali yake ciki bayan barin shi gidan su Aysha ?
   Tsakanin *macuta* guda biyu da kuma ya Abdallah waye zai yi  nasarar auren Aysha ?
       Shin burin Ilu angon Shatutuwa na auren Aysha zai cika kuwa ?

   Ku biyo ni da sannu za ku samu amsosin tambayoyin ku a cikin littafin nan mai suna *Waye Macuci*'''

   *Dan jin ra'ayoyin ku wani irin lambar yabo zaku ba ma marubuciyar a matsayin wannan shine littafin ta na biyu sannan kuma me ka/kika fahimta game da sakon da marubuciyar take shi isar muku?*
       *Shin labarin cikin littafin na tafiya da sunan littafin kuwa? Kuna ganin zaku ci gaba da karanta litattafan ta masu fitowa gaba kuwa*
   

Pls share

*eedatou✍🏻*
     ~Y'ar mutanen Dengi~

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now