Page 57

692 37 0
                                        

🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
          *☀WAYE MACUCI☀*         
🏵🏵☀☀🏵🏵☀☀🏵🏵
        '''Suhaib koh Suhail'''

***********************************

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS P.M.L*💭💭💭

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
      
          
                       ©
'''Marubuciyar Rayuwar Sumayyah'''

                   *eedatou😍*

'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*    

  
        ~Da wannan shafin nake bama masoyana hak'uri da su dakace ni zuwa bayan sallah ta wani gefen kuma nake cewa da ku muna daffff da kammala wannan littafin da yardar Allah bissalam.~

                            5⃣7⃣

Aka kawo musu abinci suka ci suka sha, abba ya tambaye su lafiyan d'anuwan nashi ummi Sumayyah ta amsa mishi tace" lafiyan shi lau, haka suka zauna suna hira da y'an uwan har inna Larai ta shigo ta same su a gidan suka ci gaba da tad'in su kamar farko.
     Duk da inna Larai tana bak'in cikin ta a kan nan da za'a d'aura amma ta yi  k'ok'arin b'oye bak'in cikin ta a ran ta sauk'in ta d'aya da ma ba d'an ta bane zai kwaso damuwa a matsayin wacce zai aura.
      Yaka dai dinga tunanin nan a zuciyan ta har ta yi sallama da su ta shige d'akin ta nan tunanin tilon d'an ta ya fad'o mata a rai ta yi ta rusa kuka ita kad'an ta,,
     Zuwa yanzu babu abunda take son gani kamar ya abdallah, shin koh yana mace koh yana raye? Allah ne ya san gaibu.
       Abdallah na ka dawo gare ni na san ni nayi sanadiyan barin ka gida amma sharrin shaid'an ne, babu wata uwa da zata so ta had'a zuri'ar ta da nakasassu shi yasa har ila yau bana k'aunar auren ka da Aysha, ka gafarce ni d'ana ka dawo gare ni........, kuka mai k'arfi ya kwace mata ta sa bakin zanin ta ta toshe bakin ta ta shiga rusar kuka ba ji ba gani, sai da tayi mai isar ta kana ta rufa ido barci yayi awun gaba da ita kasancewar dare yayi. 
     Ango Suhaib kuwa sai zuba uban zumud'i yake yi dan gani yake kamar lokacin baya gudu, ji yake kamar ya murd'a hannun agogo safiya tayi.

      B'angaren su ya abdallah suma ba'a bar su a baya ba tun dare suka gama na su shirin jira suke gari ya waye su d'au hanya.
      Murna sosai a wurin tee saboda ta kusa cika burin ta na zama matar Abdallah yayin da shi kuma yayan nata daren ranar barci ma kaurace mishi yake yi a zuciyan shi ga wani uban soyayyar Ash ta ya dabaibaye mishi zuciya ya hana shi katab'us. 
      A gidan dad ma hakan ta kasance dan suma zun jido tsaraba sosai ma k'anin shi kamar yanda ya saba duk sanda zai kawo mishi ziyara balle wannan tafiyan ta musamman mai cike da tarin alkhairi.

       Durling me, durling me ki fito fa ke ake ta jira su mum are already in the park fa.
       D'as d'as d'assss take fitowa cikin takon kasaita, ta sanya tsadadden atamfa mai rashin ja a jiki d'inkin riga da skirt wanda ya matuk'ar amsar jikin ta, sai wani black vail d'in da ta d'auko ta saka a kafad'an ta yayin da take kiciniyar janye troley da hannun ta,,
       Mutuwar tsaye Suhail yayi yana kallon kyawun halittar da Allah yayi mata, sosai yau ta mishi bala'in kyau idan ka ganta zaka d'auka irin had'add'iyar amarya ce sabon shiga,,
      What a cute angel, she is shinning like a rose flower in fact more than that, a soul taker and heart controller masha Allah ya Rabbi make this gorgeous and most beautiful among all to be my life partner", abunda ya fad'a kenan a zuciyan shi bai yi aune ba sai ji yaya tace" uuummm sweety me, Allah kayan is too heavy for me to carry, duk maganar da take yi a shagwab'e take yi ta wani turo baki tana jan bag d'in a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata lokaci guda tana maida numfashi kamar wacce ta shiga filin dambe tana fafatawa da wata y'ar dambe.
      Bin yanda libs d'in ta ke motsawa a hakali yayi da ido, a take eyes d'in shi suke soma turning red saboda tsabar jaraba, ji yake kamar ya kamo ta eemmmm ya manno ta a k'irjin shi eeemmm koh sai ji sauk'in feelings d'in ta da lokaci guda ya dirar mishi, a sanyaye ya tak'o zuwa gaban ta ya rik'e hannun troley d'in hannun su na gugan na juna, tsigan jikin su ya tashi yarrrrr a take numfashin su ya fara beating fast fast, a kasalance Suhail ya fara matsowa gurin Aysha yana jifan ta da shu'umin kallo da jajayen rinannun idon shi, sakin troley d'in ta yi tana ja da baya a tsorace saboda abububuwan da take hangowa a kwayan cikin idon shi, shi kuwa sai dad'e bin ta yake har suka iso jikin bangon parlourn bai daina bin ta ba kamar zai had'a jikin ta da na shi, zaro ido ta yi tana kallon shi a tsorace yana ganin haka ya fara kawo bakin shi saitin fuskan ta, jikin ta ne ya d'auki rawa saboda sosai ta tsorata da salon Suhail lokaci guda tayi saurin rufe idon ta gam tana jiran abunda zai biyo baya saboda ta riga ta sadakar da abunda ke shirin faruwa da ita, "is this realy the Suhail i knew before or they changed him to me, oohhh no he never be", abunda kenan ta fad'a a k'asan zuciyan ta.
     Sai da ya kawo daidai fuskan ta ta yanda yake iya jiyo beating d'in heart na ta koh me ya tuno oho ya yi saurin ja da baya tare da cije libs d'in shi ya ga har yanzu ta k'i bud'ewa yayi mata rad'a a kunne yace" corrupted mind, what do you thing is gonna happen between us? ".
       Cike da borin kunya ta bud'e eyes d'in ta ta zaro su tace" what? ", tare da sakin nannauyan ajiyan zuciya tana hamdala ma Allah da ba abunda take zato bane ya farAeu da ita.
     Ya d'aga mata gira yace" yeess koh ba haka bane? ".
     " magana take yi tana buga k'afa a k'asa cikin shagwab'ar ta mai tafiyar mishi da hankali tace" no durling me babu ruwa na ni my mind is always pure".
     "Then me yasa kika rufe eyes d'in ki bayan kin san da hakan".
      Ta kuma turo baki waje tace" i was scared ne faaaaa", ta bi shi da kallo. Of what, me?, ya jefo mata tambayan.
     Ni dai durling me ka bani wuri na wuce ka ga su dad are waiting for us, ta k'are maganar tare da turb'une fuska kamar zata yi kuka.
     No ai sai kin bani amsa ta, ba ki da case da su dad koh kin manta tafiyar dan mu za'a yi ta most especially me da za'a k'ara min matsayi a fadar ki".
     Marairaice murya ta yi tace"Ohhhhhh ni dai ka matsa min i won't answer you".
     Yana kau da fuskan shi gefe yace" Ashe zamu kwana a nan kenan tunda hakan kika zab'a mana". Suna cikin hakan ne sai ga mum ta shigo dan tun d'azu suke tsaye a waje suna zaman jiran d'an aiken nasu shiru shiru bai dawo ba shine dad ya aiko ta ta dubo mishi su.
      Tana shiga ta tarar da su a hakan, ta gyara murya da sauri suka jiyo Suhail na ganin ta ya hau kame kame yana tsotsa k'eya Aysha kuwa k'asa had'a idon ta tayi da mum ta maida k'asa, haka kawai ta ji wani irin kunyar mum ya kama ta saboda yanda ta shigo ta tarar da su a hakan tunda ba wai aure suka yi ba, infact koh da auren suka yi dole zata ji kunya sosai.
      Da kyar ta iya d'aga ido ta kalle Suhail da ke dariya k'asa k'asa ta aika mishi da kallon" ka ga irin ta koh? dama abunda kake so kenan tun farko".
     Shi koh koh a jikin shi sai dariyan shi yake yi.
      Mum ta b'allo mishi harara tace" toh sarkin zumud'i zaka b'ace min da gani ne koh sai na bige maka baki ka sanya yarinya a gaba kamar zaka maida ta cike,,
      Da sauri ya gimtse dariyan shi yace" hohohoo mum taya ta d'auko bag d'in ta nake yi faaaa, toh ma na fasa taimakon ma tunda haka ne, ya wani burning face kamar da gaske".
     Kallon shi mum ta tsaya yi baki bud'e can tace" wata jakar ce a nan ba ga ta can ba oyya ka fice koh nace maka".
     Sumi sumi ya ja jiki yayi hanyar waje yana waiwayan Aysha ta faki ikon mum ta kashe mishi ido d'aya ya ja kwafa ya fice a zuciyan shi yana cewa zan kama ki ne yarinya zaki shiga hannu".
      Bayan fitan shi mum ta riko hannun daughter d'in ta ta taya ta d'auko troley d'in suka fice suma, su duka suka shige motar sai hanyar Dengi *garin mai dangi wanda bashi da dangi dangan k'ara ya fi shi*
    *Ni eedatou nace*"''' tabbas hakan take domin cikakken dangi sai mutan Dengi'''.
      Sai misalin k'arfe goma da rabi suka samu suka iso nan suka ga su gida ya cika makilll da jama'a ana shagulgulan d'aurin aure koh wa a wurin sai kai kawo suke yi ciki kuwa har da ummi Sumayyah da kuma tawagan ta sun cab'a ado suma suna ta safgan buki.
       Suna jiyo sallamar su dad hantar cikin su ne ya kad'a kulukuluuuuuuu alamar rashin gaskiya, abban Aysha ne ya taho gurin su da tsantsar murna yace" oyoyoooo maraba da zuwa babban yaya ashe kana tafe baka fad'a mana ba ai ca aka yi ba zaka samu daman zuwa ba".
       Duk da dad bai gane maganar shi ba yayi faram faram da fuska yace" ah toh ba gashi nan ka ganni ba ai aikin alkhairi ne ya kawo mu game da auren d'an ka da kuma y'ata.
      Tabassss haka ne ai koh nayi farin ciki matuk'a yanzu mu shiga daga ciki ku huta kafin lokacin d'aurin aure yayi, tsammm bai gane Aysha ba ya zo zai wuce ta gaban ta tace" Abba !!!, cakkkk ya tsaya wuri d'aya lokaci guda ammon muryar ta ya soma tace a wurin.
       Idan ba k'arya kunnuwan shi ke jiyo mishi ba toh babu shakka muryar   Aysha ce, bai gaskata ba sai ya juyo da fuskan shi direction d'in da ya jiyo muryar ta yana had'a ido da ita ya ga hawaye sharo sharrrrr na bin fuskan ta, ta tak'o a hankali zuwa wurin shi cikin muryar kuka tace" har yanzu kana fushi da ni koh abba na?.
     Bai iya ya amsa mata ba ya kawar da kan shi gefe a sakamakon hawayen da suke son zubo mishi, ga kuma uban mamakin da ya gama kama shi saboda ya san a baya y'ar shi makauniya ce yanzu kuma sai ya ga sab'anin hakan, "Allahussamad" ya fad'a a zuciyan shi.
      Bai san sanda ya rungumo ta ba suka fashe da kuka, ganin yanda hankalin mutanen da ke wurin dad ya ja su d'aki yayi ta kwantar musu da hankali, tare da shan alwashin zai sanar da abba halin da ake ciki idan aka gama taron.
      B'angaren ummi Sumayyah kuwa bayan barin su wurin tsamo tsamo ta tattaro kan mutanen ta suka keb'e a d'akin da aka bata ita da zee ta hau bin su da kallo d'aya bayan d'aya tana jin wani irin d'aci a zuciyan ta saboda zuwan ba zata da dad yayi musu,,
     Cike da tashin hankali ta zagaye hannayen ta a bayan ta hau kai kawo tana zagaye d'akin suma suka bi ta da kallon takaici suna saka abubuwa da dama a zukatan su.
      Sun jima a hakan tana tunanin mafita kafin ta yi murmushin yake tace" hmmmm Kabeer k'iris ya rage ka fad'a tarkon da na nad'a maka amma kuma sai ka k'etare, ka shammace ni da yawa ban zata hakan da wuri ba".
     "Ummi what's our next plan wallahi tun da naga su abba sun so hankali na ya matuk'ar tashi, I can'at afford to loose my choice, ta k'are maganar tana fidda kwalla".
     Suhaib ya dafe kafad'an ta yace" stay calm sis she knows what to do and i belief ummi can do better than this, ki kwantar da hankalin ki ai bai riga ya gano ba tsoro na ma kar abba ya fad'a mishi komai ne".
     Ummi ta maida fuskan ta kan Suhaib tace"ya zama dole muyi musu tufkan hanci a cikin mintuna kalilan a yi d'aurin auren nan idan ba haka ba komai kwab'e mana zai yi".
     Sai yanzu malam D'ahiru ya samu daman yin magana dan tun d'azu ya shiga b'oye fuska a bayan mutane baya son su dad su gano shi amma abunda bai sani ba tuni suka gan shi, kukan su abba da Aysha ne ya d'auke musu hankali har suka manta da shi a wurin.
      Fuzar da iska yayi yace" ai kuwa da gaskiyan ki  gara ayi abun da gaggawa dan na tsorata da ganin Alhaji Kabeer".
       Da wannan shawaran suka yi amfani da shi suka samu abban Aysha da maganar Allah ya taimaka ba dad a wuri ya ammince musu.
       A zaton abba koh dan maganar d'aurin auren Suhaib da Aysha ne ya kawo su dad.
      Inna Larai kuwa tana uwar d'aka bata san wainar da ake toyawa ba labarin zuwan Aysha ya iske ta har ma aka ce mata da idanuwanta tangaras ta shigo gidan, hanalin ta ya bala'in tashi a take ta fara jin zuwa ya k'aryo mata saboda ta san cewa kashin ta ne ya bushe, haka ta mak'ale a ciki ta k'asa fitowa.
      Bayan abba sun gama magana da su ummi Sumayyah aka fara shirye shiryen d'aurin aure suna gamawa suka nufi masalacin unguwar da gudanar da d'aurin auren.  
       Bayan fitan su Aysha ta nufi d'akin ta na da wanda tayi rayuwar ta a ciki a lokutan baya, tana isowa ta samu an danna lock ma k'ofan, ta nemo babban dutse tayi ta buga kwad'on tana mai da numfashi da kyar ta iya bud'ewa ta shige ciki tana dube dube, duhu ta fara gani a idon ta kasancewar daga rana ta fito hakan ya sa bata ganin komai sai wani uban duhun da d'akin yayi mata. 
       Dafa wuri ta yi ta rakub'e a wuri d'aya har Allah ya taimake ta duhun ya dusashewa a idon ta haske ya fara bayyana nan ta shiga kare d'akin kallo tana mai jin tausayin kan ta da kuma rayuwar da ta yi a baya.
      Abunda ya fara fad'o mata a rai shine yayan ta wato ya Abdallah a take ta soma tunano irin rayuwar da suka yi a baya tun tana da kuruciya har lokacin da k'addara ya afka mata ta bar gida , da irin taimakon da ya Abdallah yake ta yi mata.
       A take ta ji zuciyan ta na son ganin shi duk da dai cewa a baya ya guje ta amma baza ta manta irin tarin halaccin da yayi mata ba, zama ta yi a kan madaidaicin gadon ta na k'arfe hawaye ya shiga bin kuncin ta.
      Haka dai ta zauna kusan rabin awa a d'akin ita kad'ai tun mum na neman ta har ta gaji ta daina mutane kuwa sai gulma suke k'asa k'asa wai Asha ta waye ta koyo fitsara wai ace amarya da kan ta tayi ta keta cikin mutane babu alamar kunya a tattare da ita.

WAYE MACUCIWhere stories live. Discover now