13

1.3K 110 1
                                    

Wurin k'arfe 1 na dare ya isa  rugai wuro chekke, gidan kakannin shi ya nufa bai wani sha wahalar k'wank'wa sawa ba, saboda Dad ya fad'i ma Modibbo zuwan shi.

Cikin gida ya nufa ya iske Nene da Modibbo zaune suna jiran isowar shi, da sallama ya isa ciki.

Cikin murna da jin dad'in ganin jikan nashi ya taso yana cewa,

"sannu da zuwa babana kasha hanya"

Duk da harshen fulbi yake Mashi magana, murmushi Nurain yayi ya gaida shi cikin girmamawa. 

Da yake Modibbo bai cika janshi wasan jika da kaka ba, saboda sunan mahaifin shi gare shi, nan Nene tayi Mashi sannu dazuwa, ta kawo Mashi fura mai sanyi da tuwo yaci 

            Yana gama wa yai masu saida safe ya wuce sashenshi, ya watsa ruwa ya kwanta, yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi.

Ya k'agu Safiya tayi yaje yaga Lailaar shi da wannan tunanin bacci ya kwashe shi.

                 ****************
Abeer ce ta shigo gidan da gudu kamar zata tashi sama, motar bata gama tsayawa ba ta bud'e kofar motar ta fito.

Da gudu naga ta shiga cikin gidan, tun a falo ta fara k'wala kira, Grandpa! Grandpa!! Muryan wani naji yana magana da larabci.

           juyawa nayi dan Inga wanene, wani tsoho nagani, fari kanshi da hula, amma da ka kalli sajen shi zaya tabbatar maka da babu bak'in gashi a kanshi.

Duk da  jikin tsufa, baisa tsantsar kyawun shi ya gushi ba. Kyakkyawa ne na gaske, wani farin glass ne a idon shi, hannun shi rik'e yak'e da waya tana kange a kunnen shi, cikin harshen larabci ya kammala wayar, ya ida sauko wa daga bisa matakalen benan.

Da gudu tayo wurin shi ta fad'a jikin shi tana kukan shagwab'a, cikin harshen hausa naji yana cewa,

"mamana waya tab'a man ke"?

Cikin shagwab'a tace

" Ba yaya Manan bane, yak'i yiman approven project d'ina ba"

D'ago ta yayi, ya share mata hawayen dake bin fuskar ta, yaja ta suka zauna bisa kujere, sannan ya dube ta yace.

" Abeer! naga project d'in but ina gudun kizo ki fara a samu matsala! are you sure zaki iya?"

Fuskar ta d'auke da murmushi tace 

"Allah Grandpa zan iya"

Yace

"Ok amma fa kika zo kika kasa ba ruwa na, keda Manan kuma kinsan halin shi"  cikin sauri tace "eh, naji"

ok I'll talk to him.

Wani murmushi ta saki najin dadi, tace " thanks Grandpa I love you so much"

fuskar shi d'auke da murmushi,

yace 

"I love you too mamana" tashi tayi, tayi cikin gida da gudu tana murna, binta yayi da kallo har ta bac'e mai.

Wasu zafaffin hawaye suka cika mai ido, baisan sanda suka zubo ba, saidai yaji ana share mai, kallon mai share mai hawayan yayi.

Cikin sanyin murya yace,

"kana tunanin aunty Sofia ne, in'sha'Allahu zata dawo. Jiki na yana bani, a duk inda take, tana lafiya kuma ta kusa dawo mana,"

Murmushi yayi yace "Allah yasa Manan, Allah yasa ina da rabon k'ara sa d'iyata a ido kafin in mutu". 

Ameen yace d'auke da murmushi a fuskar shi. Yace,

"wai sosai suke kama da Abeer ne? Ni bazan iya tuna kamannin ta ba yanzu",

Murmushi Grandpa yayi yace "ina zuwa" sama naga ya hau ba'ai 2 minute ba naga ya dawo da wani d'an k'aramin box, ya mika ma Manan.....

                  ****************

BAK'UWA  (STRANGER ) COMPLETEDWhere stories live. Discover now