31

1.2K 93 10
                                    

A gurguje

Numfashi ta sauke, a hankali taci gaba da Basu labarin gwagwarmayar da suka Sha da ita da Lailah harma da manager din.

Falon yayi shiru kowa na jimamin wannan Al'amari, mahaifin Lailah ko babu abun da take Sai share hawaye, idan ya tuno wa'innan sukai sanadiyar rabuwar shi da matar shi da tilon diyar shi ba karamin bakin ciki da takaici take ji ba duba da yanda suka rinka nuna damuwa alokaci. Batan nasu.

Sallamar manager ce ta katsen shirun, ya shigo da wasu takardu da laptop ha hannun shi, fuskar shi dauke da murmushi, ya durkusa ya gaida manyan dake falon sannan ya Mika ma mahaifin Lailah takardun dake hannun shi na evidence din komai da ya hada.

A hankali mahaifin Lailah ke kallon komai, bacin Rai bayyane a fuskarshi, rufe laptop din yayi, ya fiddo waya ya Kira wani babban Dan sanda abokin shi yace Dan Allah Yana son ganin shi Nan gidan surukkan shi, da yake yasan gidan, Dan shine ya handling case din batan su Sai gashi ya iso cikin 30min saboda shi azaton shi ko anji wani labarin matar abokin nashi ne.

Da sallama ya shigo falon, baiyi mamakin ganin falon cike da mutane ba Dan dama don kusan lokacin da zaizo a can baya haka take tadda su. Yana gaisawa da su modibbo  ne da suka kasance mashi bakin fuska, idon shi yayi arba da Mama da ke zaune can kusa da grandfa, da mamaki a fuskarshi ya dago Yana kallon ta, kafin yace Alhamdulillah Allah abun godiya ya juya ga Mahaifin Lailah Dan Taya abokin nashi murna Nan ya kwashe komai ya Fadi Mashi sannan ya nuna mashi evidence din da suke dashi. Ba karamin mamaki yayi ba, Amma idan akai la'akari da wasu abubuwan wannan ba abun mamaki bane, Dan uwanka da kuka fito ciki daya ma na iyar cutar ka balle wasu can bare.

Daddanan ya Kira yaranshi dake Lagos ya Basu order Kama duka wani Mai Hannu acikin Al'amarin kafin ya iso gobe.

Hannu ya Mika ma mahaifin Lailah fuskarshi dauke da murmushi ya Kara mashi murna sannan yayi masu sallama yabar gidan da niyyar barin garin zuwa Lagos Dan hukunta wa'innan azzaluman mutane.

Alhamdulillah rayuwa na ta tafiya, ankama stepmother din mahaifin Lailah da yaranta an yanke masu hukunci daidai da laifin kowa.

Gata babu irin Wanda Lailah Bata gani daga family dinta, kusan yanzu babu Wanda Bata sani ba a suka side din mahaifiyar ta an kaita wurin kakanta na wurin Ina shima. An Kara daura auran maman ta da baban ta, rayuwa take ta gata, ga masoyin ta a gefe da yanzu Bai wuci Yan satittiki bikin su ba.

Yau Friday, biki ya Kama saura kwana biyu, duka gidajen biyu cike suke da yan'uwan da abokan arziki, ita Lailah dama sunanan Abuja. A ban garan Nurain kuwa, komai na tafiyar mashi yanda take so, yanzu haka sun kulle sosai da Manan abotar su gwanin burgiwa. Gashi Kuma duk zasu angwance Rana daya inda shi Manan zai auri Abeer. Shirye shirye suke sosai duk wani Abu da ya kamata sun kammala hada shi.

A bangaran amaren ma haka ta kasance, komai sun tanada, daga dinkunan da zasuyi kwalliyan biki, sarka da takalma da sauran tarkace dai dun sun harhada, part daya aka Ware masu suda kawayen su, dukda ma ba wasu kawaye da yawa suke dasu ba

Haka biki yaita gudana cikin tsari da wayewa, anyi event guda biyu Sai wa'azi da akai.

Toh Alhamdulillah masu Karin managa na cewa Rana Bata karya saidai uwar Diya taji kunya. Yaudai an daura  Auran Nurain Sulaiman modibbo da masoyiyar shi Sukainat(Lailaah) Sai Manan da Abeer. Daurin auran ya samu halartar manyan mutane da Yan kasuwa hardaga kasashen ketare mahaifin Lailah Kam bakin shi yaki rufuwa Dan murna jinshi take kamar babu Wanda yakaishi farin ciki a ranai.

MashaAllah Amare sun tare a gidajen mazajen su, taro ya watse lafiya, bayan kwana biyu da bikin ko wane ya dauki matar shi suka bar kasar danyin honeymoon dinsu. Tammat bihamdullah. Anan na kawo karshen littafi na Mai suna Ba'kuwa, kuskuren dake cikin Allah ya yafe man.

Kuma Ina Mai matukar Mika godiya ta ga mabiya littafin, da hakuri da sukai Dani. Nagode Allah yabar zumunci.

Sai mun hadu a sabon littafin na Wanda muke rubutawa nida kawata Mai suna Akan Y'ATAH. Nagode taku har kullin

Yar'adami✍🏻

BAK'UWA  (STRANGER ) COMPLETEDWhere stories live. Discover now