CHAPTER TWENTY ONE

1.5K 98 9
                                    

WACECE ITA?
NA UMMU ZAID

S

alam good pm to u all WACECE ita lovers,kunjini kwana biyu shiru pls ku gafarceni, na tafi wata seminar kwana biyu bansamu time din update ba.
I will be very brief inshallah Allah littafin WACECE ITA yakusa zuwa karshe.
Show ur love by commenting and voting thank. Love u all.


             Cigaban labari

Bayan isarsu gidan su muqaddas din dirrect parlourn abbah suka wuce lokacin duk wani Dan uwa dayakamata ace Yana wajen ya hallara sosae gaban ummi ke faduwa don Bata San tayaya zata ga zeenatun dayau shekara 6 Bata saka ta a Ido ba.

Luby ce tafara sallama ta shiga parlourn tana rike da hannun zeenatu dake tirjewar bazata shiga ba, dakyar ta ja hannunta suka shiga parlourn Wanda dasauri ammy din  tareda ummee dinta suka tashi suka riketa,itaedae kallon su kawae takeyi don kanta wani nauyi yayi mata Kamar ba nata ba, abbuh daya kasa dauke idonsa a akanta yakira sunan ta cikeda farin ciki da dokin ganin diyarsa data fi soyuwa a ransa fiyeda kowa, alhamdulilah mamana zo kusa da abbunki, kur ta kura masa Ido tana kallonsa yayinda Kamar wacce kwae ya fashewa ta fada jikinsa tareda fashewa da wani irin gigitaccen Kara sosae hankalin duk Wanda ke wajen yatashi abbuh ne yakara riketa tamau don wani ihu datakeyi, yashiga tofa Mata adduar da duk tazo bakinsa, muqaddas dake gefe zaune kuka kawae yakeyi Kamar mace yayinda Bawan Allah keta kuka kiran mammynsa, bawanda ya lura da cewa yaron na dakin don haka dasauri ammi ta daukesa tareda shigewa cikin gida dashi.

Bayan abbuh ya gama tofa Mata ayatul ibdalul sihr da ayoyin ruqya akasamu ihun ya lafa,lamo tayi jikin abbuh Wanda dakyar ta iya dago Kai ta kallesa "abbana Ashe zan sake ganin ka a duniyan ina ummina ina haseen da lily? Abbuh ya Bata amsa cikin farin ciki" ga umminki Nan ae dasauri ta mike tafada jikin ummi tareda fashewa da wani irin kuka me cin Rae ummi tacigaba da shafa bayanta,"ya Isa bar kukan Nan zee kada kanki yayi ciwo,addua yakamata kiyi ba wae kuka ba kinji ko, yi hakuri.

Sosae takara shigewa jikin ummin sae kace wani zae rabasu,bro haseen dake gefe Yana murmushn Jin Dadi yace wato sis ni bazaki zo wajena ba kenan bayan kinsan I was forever dying missing my sis,dagudu ta fada jikinsa tareda Bashi hug,Wanda muqaddas yayi saurin janta tareda fadin haba madam take it easy kinsan dae yanxu kin girma,kallon haseen yayi tareda daga masa gira kowa a dakin sae dayayi dariya sae a lokacin ta lura da ummin muq da abbuh Wanda cikeda kunya ta janye daga kusa da muq.

Gyaran murya Abbu yayi tareda Fara adduar godia ga Allah" Alhamdulilah Rabbil alamin komae a dunia Yana da iyaka Banda ikon Allah,ubangiji muna rokonka daka cigaba da karemu ka karemana zuriar mu daga sharrin dukkan wani abin ki duk Wanda ya nufemu da wannan mummunan sihiri Allah Kai kadae kasan abinda zaka masa Allah ya maida masa mugun aikinsa akansa" kowa a dakin yace ameen, sannan yacigaba, yanzu tunda komae ya lafa yakamata abama zeenatu damar tahuta tukuna, sanan general yakamta ka hakura da tafiyar Nan yau Dan Allah zuwa jibi inyaso sae ku wuce da zeenatu din taga danginta shekara 6 ba yau ba, muqaddas dake gefe yadago Kai dasauri yakalli abbuh suna hada Ido abbuh yajefa masa harara dasauri ya sunkuyar dakai,Amma yazaayi abbuh yamasa haka shi ae yafi kowa bukatar son ganin matarsa.

Amy ce tashigo dakin rike da hannun bawan Allah "ehmm abbuh saboda kishi ko takan sabon angonmu bakayi to gashinan yazo yagaydaku, kowa a dakin kabbara ya dauka ganin kyakyawan yaron dake rike da hannun ammi,lallae duk zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sae yayi,ummin muq dae kauda Kai tayi abinka da Dan yaron ta na fari,Amma cikin zuciar ta kallo daya tamasa taji son yaron ya kamata, general ne ya Miko masa hannunsa da gudu abdallah yafada abinka da dama akwae son jamaa,tuni ya Fara surutu "Kai yasunanka,kowa a dakin sae da yayi dariyar tamvayar da abdallah yama General," ni kakan ka ne baban mamanka, yanuna masa abbuh wann ma kakanka ne duk dae dae da dae dae yake ma yaron bayani iya fahimtar sa,nuna muqaddas yayi tareda cewa yaron kaga babanka Nan,kur abdallah ya kura ma muqaddas Ido, " ni babana sunansa baban Abdulshakur wannan ba babana bane, dasauri zee ta ce abdallah katuna nafada maka babanka yayi tafiya me nisa ze dawo ko? Da sauri yaron ya girgiza Kai, sannan tacigaba,to gashi Nan yau yadawo shine babanka,dasauri ya janye daga jikin general yashige jikin muqaddas" yeah daddy oyoyo" kowa dakin saeda abdallah yakara sakashi dariya yaron akwae van dariya Wanda a hankali yafara shiga zuciar danginsa kowa awajen saeda yabi yama magna,addua aka yi sannan aka ce kowa ya watse tunda yan biki suna Nan yau ne daurin aure a haka kowa ya watse ammi taja lubabatu da zee dakin ta inda Nan amaren suke sosae su Nadiya suka shiga murnar ganin auntynsu cikin Jin dadin ganinsu zee tasake dama sun Saba tun bayau ba aranta tana mamakin ganin girman da yaran suka Kara lokaci daya, luby ce tama zee sallama tareda cewa kinsan abin biyu ne dole inkoma gida mufara Shirin
Tarbar amarya kizauna Nan tunda bikin dangin mijinki ne.

Har kofar gida zeenatu tarakata sannan aka nuna Mata bangaren da umminta take tashiga suka Kara rungumeta juna Nan Hira tasake barkewa na tsakanin uwa da ya duk da haka yan biki Basu barsu ba sae shigo wa ake ana taya murnar ganin zee.

Washe gari zeenat da su Gen suka kama hanyar Lagos sosae ran muqaddas yabaci ko ganin matarshi yanda yakamata baa barshi yayi ba, hakanan dae ya hakura, lokacin nafeesa ce a gida tadawo hutun semester dinsu ta karshe a Oxford uni, sosae tayi murnar ganin yaruwarta Abdallah ko tun dayaga nafeesa ya tattara yakoma dakinta jininsu bakaramin haduwa yayi ba, kullum sae sun fita wajajen shakatawa a lagos.

Yanuwa daga bangaren ummi da gen sae zuwa ake barka da arziki sae gidan yazama Kamar gidan biki kullum cikin Baki.

Da wani dare family din ana zaune ana Hira time din har matar haseen tana nan,Nan zeenat ta Basu labarin rayuwar datayi cikin kaskanci kowa a dakin kuka yake banda abbu da haseen da idonsu yayi ja jazur alamar bacin rai musamman dasukaji wani yayi ma diyarshi fyade.

Ummi da ta idar da sallar ishai ta juyo ta dubi zeena, "inace wayarki ce tundazu ake ta Kira kinki dauka ko? "Wlh ummi Dr zaid ne ummi bansan ya zanmasa bayani ba Sam, ummi ce ta cigaba"haba zee ae baa haka yakamata ki masa bayani bae kamata kuyi rabuwar haka ba maza Kira shi"
Cikin rashin son Kiran tayi dialling number dinshi don har ga Allah tausayi yake Bata matuka don ita tasan son da zayd din kemata.

"Hello haba dear menayi ne aka ki picking calls Dina nayi text ba amsa, in wani laifin nayi forgive me pls" shiru tayi taraeda kokarin tattaro maganar datake son fada masa tace, babu laifin dakai min dr, na hadu da family na, cikeda tayata farinciki yace" oh Masha Allah Alhamdulilah I'm very much happy for u dear,kice yanzu Zaki bani chance din fitowa don nakosa muyi auren Nan

Am sorry Dr inada miji uban Dana Abdallah, shiru yayi daga bangaren shi Kamar wuta ta cinye shi dakkyar ya iya hadiye wani mugun miyau a makoshinsa,Allah yasan ba karamin so yakema zeena ba saedae bayanda zaeyi kaddara ta Riga fata, dakyar ya iya fadin" congratulations zeena am happy for u" kit ya cutting din call din,cikin sanyin jiki haka na ajiye wayata kusa Dani gaskia naso muyi rabuwar mutumci da fahimta nida doc zaid, ranar kusan a haka na yini Sam ba walwala a tare Dani, Koda abban abdallah yakirani Shima yaji canji a taredani juyin dunia yatambayeni naki bashi amsa karshe dae hakura mukayi da wayar Baki daya.

Washe gari ummi tace to zeenat yakamta muyi Shirin maidaki dakinki tunda kinyi two weeks nasan yaron Nan alkunya kawae yake Mana inshallah Nan da wani satin Zaki Koma tunda kusan yanzu Kinga an gyara Miki komae na dakinki anfitar an siya sabo komawarki kadae yarage, ki shirya anjima zamuje asibiti a dubamin lafiarki,da sauri na dago Kai na kalli ummi, ummi lafia ce vanda ita? Ba dole ba zee kin hayhu hayhuwar fari ke kadae wayasan abinda yafaru da wajen ae yazama dole muje a duba in akwae matsala a magance ta don tuni nasaka hajiya shaawa tazo tafara aikin gyaran ki,cikeda kunya na sunkuyar dakaina.

Da yamma muka shirya muka ziyarci wani babban private hospital da shine family hospital dinmu, gynae doctor ummi tace mukeso mugani don haka aka mana iso wajen babban consultant din gynae, bayan yan tambayoyi ya umurceni da in kwanta bisa couch din office din cikeda Jin nauyi na kwanta, Safar hannu yasa sannan ya Fara examination din wajen,bayan yagama yace na sauko haka na sauko, yan rubuce rubuce yayi tareda fadin, maa gaskia tasamu tear sosae sanda zata hayhu,Wanda har yayi healing a haka saedae yanzu abinda zamuyi shine zaa Mata minor theatre(karamar tiyata) a dinke wajen inkun shirya ki dawo inkuma yanzu zaayi toh we can make the arrangements.

Cikeda tsoro na kalle ummi inajiran inji me zatace don har ga Allah banso a taba min lapiyar jikina, ummi ce ta ta tsinke min tunanin( is ok you can go ahead and do it now bamuda lokacin Bata time, haka inaji in gani aka tura ni theatre bayan nasha anaesthesia aka min dinkin nan, bayan wasu awoyi aka sallamemu, tareda magunguna dazan dinga Sha, sanda allurar tasakeni kuwa sosae na dinga jin zafi Kamar me sabuwar hayhuwa haka nake zama dakyar tashi dakyar,ummi kuwa tasani agaba take da shiga ruwan zafi da gishiri, daga baya nadinga shiga bagaruwa kan kwana 5 har wajen ya Fara hadewa.

Ko ina labarin mardiyya? Kubiyoni chappy nagama muji yanda zaa Kare inshallah it will be second to the last page. See yah

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now