05: Extraordinary

957 84 10
                                    

       🌠Zuciyar Tauraro🌠(Adams story).
  By Bilkisu Muh'd.

      05: Extraordinary

Gdan Baba soja: Gdan su ya ci wannan sunan neh tun kafuwar Malik empire sabida duk wani ɗa namiji koh in ce yawancin mazan wannan gda Force suke joining, duk da sunan ya bisu hakan beh hana wasu zaban wani aikin bah, haka wasu gdajen Malik family zaka samu akwai masu aiki a force din.

    A hankali take saukowa daga saman stairs, kafarta sanye da flip flops , gown ce meh tsantsi navy blue da kwalliyar kananan  stars red da yellow a jiikinta tayi rolling da black veil.
  Tana kaiwa karshen stairs din aka kira sunanta, "Fariha"
   a hankali ta amsa da  "Gani nan na fito" tana dan shafa wuyanta koda ta karasa cikin makeken falon sai mamanta ta mike tsaye tana cewa "Farha barta tayi wannan aikin"
   Fariha ta kalli abinda Farha keyi taga ruwa da drinks ta kawo ma bakon su sannan ta hau zuba mai snacks a plate, da Farha ta dago tayi wa Fariha kallon sama da kasa sannan tayi tsaki can kasan makoshinta kafin ta bi bayan Maman su.

      "Ba gaisuwa neh Fariha?"  Bata kalleshi ba tace "Meh ya kawo ka?"
  Bata san ya mike bah sai jin dumin jikin  shi da tayi daf da ita.
   "Sa'ad meh ye haka?" Tayi maganar tana mikewa tsaye, mamaki kwance a fuskarta, "Anya kasan meye kunya Sa'ad, kasan abinda kayi min kuwa"
   Yace "Kema kin san abinda kikayi shi yasa baki fadama ƴan gdan ku abinda ya faru bah"
  Ta bude baki zatayi magana yace "Tunda har magana kina yi lfy lau sai ki shirya_"
  Tace "Ba in da zanje"
   Yayi yar dariya sannan yace "Bari muji abinda General zece"
   Da sauri ta dago ta kalli Saad sannan ta tambayi kanta 'wai dama a duniya akwai marasa kunya haka, Baffa Ali fah abokin shine, amma yake barazana dashi bayan yasan abinda ya aikata'
  
     Kaman yana jira a ambaci sunan shi sai ga Baffa Ali,Kanin babansu kuma autan Kakan su, daya bayan daya ƴa'ƴunta maza suka shigo falon har su shida duk sanye da Khakin sojoji. Dama tasan yau zasu dawo dan tun da accident dinta ya faru basu samu zuwa bah.
   Hamma Asad babban ƴa'ƴansu kawai ke gda kuma shi kadai neh bebi sawun Baban su bah da  sauran uncles dinsu ya zama soja bah, instead sai ya zabi likitanci.

    Tunda suna da yawa kawai sai ta duka kasa tace sannun ku da zuwa, Baffa Ali dake gaba ya fara tsayawa gabanta, yayin da Sa'ad ya kame yana sarawa.
   "Salihar Baba" ta amsa da na'am. Babu mai kiranta da Saliha sai shi saboda shiru shirunta tin tana karama ya sa mata wannan sunan.
  "Ya na sameku?"
Ta amsa da lafiya lau"Kun dawo lfy?"
  Shima ya amsa da lafiya lau,sannan ya tadata tsaye, kafin ta ankara ya janye gyalen da tayi rolling meh rufa ma wuyanta asiri, bata da wani tsawo sosai shi yasa  idonshi ya sauka daidai kan ciwon.
   "Saliha ana wasa da rai neh?"
A dan tsorace tace Aa, yace "Shine kika bari aka ji miki ciwo haka"
  A dan daburce tana in-ina tace "A-aaa Baffa Ali, -ni_i ban kula bane bah"
   Ƴa'ƴunta sun rigada sun zauna shine suka taso suna duba ciwon.
  "Ya akayi hakan ya faru?"
Kuka neh ya tokare mata a makoshi, a ranta tana cewa 'Ba kun sani bah, ni dan Allah ku bar tambayata'
   Hamma Sadiq yace "Baki ji bane bah?"
  Ta dan ja baya duk da sun rike mata hannu tana cewa "faduwa nayi" ta karasa maganar tana jan hanci dan kar ta fashe da kuka.
   Auta cikin maza wanda suke kira da Yaya BB saboda yana da sunan Kakan su yace "Dan Allah nuna min yadda ake faduwa bisa glass aji ciwo haka"
   Kara dabircewa tayi,jikinta ma ya hau kyarma, idanunta suka firfito, kana ganinta kaga marar gsky.
   Sa'ad yace "Tsoron shi kike ji?"
Da sauri ta dago kanta zata kare shi' dan tasan Adams suke nufi
  "Aa-aa ,A-ii sh - shii shi taimako na yayi"
   Baffa Ali ya kara kallon ciwon da kyau har da daga mata haɓa, "I can't believe Asad da Babanku ya yadda da labarin faduwar nan"
   Bata kai ga cewa wani abu bah Farha ta fado Sitting room din a guje tana kiran sunan ƴa'yun nasu.
   Yaya BB ya katse mata murna da "My friend kneel down there" da sauri ta ja birki tana shagwabe fuska "Kai Yaya BB daga dawowa sai cin zali"
   Yace "Ke!" Da karfi sai tayi baya tana dan cuno baki, kafin ta kai gwiwowin ta kasa.

Zuciyar TauraroWhere stories live. Discover now