14: Agreement

736 80 1
                                    

🌠Zuciyar Tauraro🌠(Adams story).
By Bilkisu Muh'd.

                

 'If you don’t like a person it’s because they remind you of something you don’t like about yourself'. – *Sigmund Freud*

              14: Agreement
    
     
Inaya ce ta fito tana mika dan sabo da tashi da wuri yasa koh baccin safen weekend din ta kasa yi.  Kafin ta bar corridor din dakinsu ta shiga falo taji wani beat meh dadi na tashi, sai kuma aka kashe aka sa wani. Tun kafin ta shiga falon ta gane waye a wurin.
   "Good morning "
Dago da kanshi yayi yace mata morning shima da dan smile a fuskar shi .
"Zamu yi sabon waka neh?"
   Ya amsa da "Eh, Karami zeyi producing video din" dariya ta fashe dashi sannan tasamu wuri tazauna.
  Idanunta neh suka kai kan flask da coffee a kusa da shi. "kwana kayi kana wannan abin?"
   Wuyan shi ya shafa sannan yace "Na tashi da dare neh na fara"
  Tace "Yayi kyau, ya kafan?"
Yayi dan karamin tsaki yana shafa kafar "Am sure harda shi ya hanani bacci, sai wani kumbura yakeyi"
  Tace "Kasa ice pack din akai" ya daga mata kai.
   Bata ce komai bah ta tashi tsaye ta nufi kitchen, bayan ƴan mintuna ta dawo da ruwan zafi da towel. Aje wa kawai tayi ta wuce dakinsu. Karami ma ba ma'abocin baccin safe bane bah shi yasa taje tafito da shi.
   "Amyr ya duba maka kafan manah?"
Inaya tace "Fushi yake da shi"
Da sauri yace "Wa yace fushi nake da shi?"
   Ta amsa mai da sauri itama "Wasan jiya  ya fada mana komai ai"
   Ya hura hanci sannan ya kauda kai.
"Yanxu fada kake da kowa, Amyr Fariha_"
  "Ya zaki sako wannan ana maganar mutane"
   Tace "Ka gani" Karami ya girgixa kai kawai ya tsugunna ya daga kafan.
   Yana farawa Inaya ta hau nuna mai yadda zeyi, da ya gaji sai ya mika mata towel "Meh yasa kika jawo ni tunda kin iya"
   Tace "Sorry" dan tasan hakan da cin rai.
Bayan an gama komai ta kwashe komai taje ta aje. Da ta dawo ta samu Karami baya nan sai shi kadai yasa headphones yana cigaba da composing wakarshi.

   *************************

Headphones din kawai ya sa amma be iya karasa abinda ya fara bah dan tunanin shi yakoma kan abinda yafi tsaya mai a rai.
  She was chatting endlessly. Tunda yasanta rana ta farko kenan da ta saki ranta ta kuma fitar da duk abinda yazo  bakinta ba tareda wani filter bah. Kishingidawa yayi yana hango 1st day daya ganta. Tun lokacin ya fahimci akwai wani muhimmin abinda bata da shi watau confidence. Komai nata na wallflower neh, yanayin shigar ta, rayuwarta da maganarta duk babu confidence a ciki.  A gaskiya baya da niyyan bata time dinshi akanta dan ba taba yin wani interview zeyi bah, saidai yaga wannan neh hanya mafi sauki da ze iya fiddo ta daga cikin shell dinta a matsayin shi na guardian dinta ya kuma tabbata koh nan gaba bazata kara  tunanin daukan ranta bah.

   ***********************
Sha daya ta kusa yaji tafiya da magana yayi yawa ma'ana da yawan ƴan gdan sun tashi daga bacci. Yana living room zaune yana aikin shi saura kuma suka fara piling a dining area.
   Tare Fariha, Farha, Baffa Ali da kuma Sa'ad suka shigo gdan. A dining table suka fara tsayawa suka gaida ƴan gdan, sannan suka karaso inda yake. Farha ta zauna daga hannun kujera dan bisa one sitter ya zauna. Sa'ad yace "Samu wuri ki zauna manah" ta dan hade rai kafin tace "am comfortable here" tana gamawa da Sa'ad takalli Adams cikin shagwaba tana cewa "My hero ya kafar ka?"
  Murmushi yayi kafin yace "Lfy lau fah. Sa'ad na dan hade rai da cije baki yace "Sorry man" Adams ya girgixa kai"Ai wasa ya gaji haka, at least dai we won" Baffa Ali yayi dariya shi kuma Sa'ad ya kakalo murmushi ta hanyar washe hakora.
Farha ce ta sako matsalar ta na rashin hotunan su tare dan tana so ta kafa tarihi, gashi kuma zai kara mata followers a insta.
"Baffa Ali yace kai da Allah share wannan, ku tashi mu tafi"

  Jiki ba kwari Fariha ta mike tsaye, dan yanxu zata koma gda ta zama witness na fada da kuma shirin Farha da Sa'ad.
  Ta mike Yarima yace"Fariha ya aikin mu?" Tace "Munayi"
  Fuska daure Sa'ad yace"Mu je"
Lura da hakan da yayi yasa yace "Mun fasa na yau neh?"
  Baffa Ali yace"Ai dama wannan magajiyar zata tashi mu tafi"
   Farha ta turo baki tana cewa "Nima nan zan tsaya"
Yace"Mamanku da ke jiranki fah?" Ta daga kafadu tana cewa "Ni na fasa zuwa" Hade rai Baffa Ali yayi sai ta fara gunguni tana kallon inda Yarima ke zaune. Beh kallesu bah yace "Farha aje kar abar Mama da jira, in kun dawo sai kizo ki yini manah"
   Baki zumbure ta tashi ta tafi. A ganinta da Fariha neh  da yace ta tsaya.
  
Suna tafiya Fariha ta samu Inaya tayi requesting pen da paper, sama suka haura ta dauko laptop ta bata.
   "Wannan baze fi sauki bah,in kin gama kawai sai kiyi emailing kanki koh?"
   Fariha tace "Yes haka yafi sauki thank you" ita ta fara sauka amma ta tsaya data kusa isa kasa har Inaya tazo ta sameta a wurin. Hannuwa ta dora mata bisa kafada sai ta dan tsorata. Sorry Inaya tace"Komai lfy?"
Fariha amsa mata da Eh.
   Har Inaya ta wuce kuma ta dawo "He's mean to you ryt?"  Fariha tayi saurin girgixa kai tana so ta kare Adams sai Inaya tace "Karki batawa kanki lokaci Fariha, nasan Adams kuma nasan abinda ze iya yi. Amma ki sani Adams is very nice bansan abinda yasa yake daure maki fuska haka bah" Fariha ta dan sadda kanta kasa. Inaya ta dafata sannan tace "Bari in baki wata shawara"
   "Just be yourself, karki yi wani abu da baki so saboda shi. Karki manta If you don't like a person is because they remind you of something you don't like about yourself kenan ba kece da laifi bah damuwar tashi ce"
  Dan tapping dinta tayi a kafada ta kuma bata thumbs up kafin ta wuce.
  Ƴan seconds ta kara a wurin kafin ta wuce ta sameshi a living room, kujerar dayake facing ta zauna harda yar sallamarta amma taji shiru ba amsa. Sai ta kara da gaisuwa, beh koh dago kai bah balle yasan da mutum a wurin.
   "Na shirya. Zamu iya farawa?" Nan ma shiru sai ta kyaleshi. Saida tayi shirun ma sannan ya dauki headphones ya toshe kunne.
   "You should always be prepared" ta dago kai da sauri tace na'am. Dago idanu yayi ya kalleta ya koma aikin shi.
   "A good reporter should always be prepared,baki san sadda zaki samu labari meh jan hankali bah"
  Tace "Ban san ka amince bah ai"
Yace "Duk da haka, a good reporter ze san yadda ze yi yayi convincing target dinshi, ya kuma tattara abinda ze samu"
   Tace  'Ai fa ya fara, kai bana taba daidai a wurin ka'
   Idanu ta zuba mai, shi kuma ya cigaba da aikin shi kaman bata wurin. Saidai tayi ta taba keyboard dan kar ya mutu.
   Yana kallon screen din gabanshi  taji yace "gashi na gama"

Zuciyar TauraroDonde viven las historias. Descúbrelo ahora