💄 Meryerm Abdool 💄 [5/20, 6:22 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇 🍇🍇🍇🍇 *_HA

327 16 5
                                    


💄 Meryerm Abdool 💄
[5/20, 6:22 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇 *_HAD'UWATA DAKE_* 👉🏻🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇

( _Based on love story_ )

'''Written'''
            '''By'''
💄 Meryerm Abdool

© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
                ( *P.M.L* )




*Wani mutum ya tabayi Manzon Allah tsira da Amincin Allah a gareshi yace, ya rasulillah mezan aikata Allah ya soni kuma mutane su soni?*
*Manzo Allah yace: ka guji duniya Allah zai soka, ka guji abin hannun mutane zasu soka.* (hakkun mubeen).





            *Page* 44&45


Su Fauziya sun iso Bk cike da burin samun nasara ga k'udirinsu, sakin jiki sukayi kaman komai ya wuce sai yak'e sukewa mutane, ganin haka yasa Mummy ita sakin jiki dasu dan dama ita batada matsala, gida ya cika sai hada-hada ake dama Inna bata koma ba Aunty Salma ce ta koma saboda kara2n yara yanzu kuma ta sake dawowa.

Fauziya cikin k'awayen Zarah ta tare da ita akeyin komai amma itakam Zarah bata wani saki jiki da ita ba saboda sam batayi mata ba duk kuwa da 'yar uwarta ce, fitowa harabar gida tayi da sunan shan iska ganin ba mutane a waye inba gateman da security ba kuma suma sha'anin gaban su sukeyi, lallab'awa tayi zuwa part d'in Haiydar ta dauko kullin maganin da Uwarta ta bata barbadawa tayi hanyan shiga kaman yadda Maminta ta gayama sannan rai saurin ficewa murmushi tab fuskarta ganin burinta na mallakar Haiydar ya kusa cika.

Haiydar da dawowarsa kenan daga gurin friends d'in sa da suka dameshi da son zuwa Argungu suga Amarya haka ya d'aure sukaje, ba wanda ya fahimci yanayinda ma'auranta suke ciki face Saleem da Shamcy da yake sunan komai suna kalle da sak'on hararan da suke aunawa juna, kafin aka gama gaisawa sukaji tsarensu kudade masu yawa suka basu, sannan sukayi musu sallama da sunan sai ranar d'aurin aure in sun dawo.

Dama Haiydar irin mutanen ne masu sakaci da Addu'a wucewa kawai yayi ba tare da yayi Addu'a ba ( sihiri gaskiya ne amma kuma Addu'a garkuwar musulmi Addu'a takobin mumini mu daure mu kula rik'a Addu'a domin kare kai da samun yardar Allah, Allah yasa mudace).

Wanka yayi ya sauya kaya zuwa k'ananan kaya yayi kyau sosai dake ya kware a fannin, fita yayi zuwa part d'in Mummy domin gayamata sun dawo.

Su Zarah ne Zaune a parlor ita da k'awayenta me lalli tana zana musu, gaida shi sukayi sannan ya tambayeta Mommy ta gayamai sun fita, har juwa zai fita yaji ana fad'in "Yaya Haiydar barka da wuni" cikin wata murna wadda aka matse k'arfi da yaji wai ana yanga, juyowa yayi don ganin mai magana karaf idonsa suka had'u da Fauziya.

Samun kanshi yayi yana ansa mata harda tambyanta yaushe sukazo ina Goggo?.

K'ara narkewa tayi cikin fi'ili ta ansa masa, mamaki ne ya kama Zarah ganin wainar da ake tunawa amma bata iya furta komai, ficewa yayi kwakwalwarsa na ruwaito masa fuskarta da shigarta Wanda ada yafi tsana, amma yau yaji ta bala'in burgeshi, jiyake kaman ya koma yayi ta kallonta. _tabdijam_

***************

Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, ayau ne aka daura Auren *Aleeyu Muktar Sadauki (Haiydar)* da *Maryam Muhammad lll (Siddiqa)* bayan saukowa daga masallacin jumu'at kan sadaki mafi sauki, sannan suka garzaya Bk aka d'aura na *Mubarak Muhammad lll* da *Fertemarh Muktar Sadauki (Zarah)*.

Waleema kawai suka gabatar inda aka gayyaci *Malam Aminu Ibrahim Daurawa* yayi lacka mai kashe jiki Wanda ba Amarya dai ba hadda sauran mutane saida zukatansu suka tsinke, ba abinda takeyi bayan kuka sanye take da Shadda fara gown akayi mata wacce tasha stone work Ja, alkebba ja, takalmi, post, har sarkar da d'an kunnen da abun hannun duka stone nasu jane, just guess readers. Lolx.

Shamcy na gefenta itama taci kwalliya sosai, su Aunty Ramla da Aysha guzame suma sun sha nasu wanka, an raba kayayyaki masu d'inbin yawa Wanda baije bane kawai bai samu ba amma kowa yasha kaya sai Sam barka, can hango member of pure moment zuwa guda sun kwashi kaya sai washe baki sukeyi musamman su o.o ban fad'i suna ba.lol

Aa Ashe hadda su Maman USSEY novella, matan kirki masu nagarta, Ameenan juna, online Hausa writers, jannart mai watch novella, kai walle abin da yawa duk sun hallara, ( hadda wadanda ban fad'a ba duk ina sonku).

Can na hango Ango Haiydar cikin taro yasha wankan fari 4rm up 2 down hadda su malun-malum sai gaisawa yake da mutane cikin sakin fuska, duk da bayason aure haka ya tsinci kansa da farinciki a ranar.

Naseeha sosai Mai martaba yayi ma Siddiqa inda yake cewa " Uwata nasanki ke 'yace ta gari wacce kowanne uba zaifi farinciki da samunta to in fatan ki dore da halinki na kirki a gidanki, ke mai hakuri ce to inaso ki d'ora wani kan Wanda na sanki dashi, danshi zaman Aure gaba hakuri ke in miki na mahaukaci duniyar gaba daya zaman hakuri ne, in kika rike hakuri zakiyi alfahari da hakan nan gaba"  haka yayi ta mata nasiha mai ratsa zuciya ta kuwa shige ta sosai dan ba abinda takeyi sai hawaye, daga k'arshe yayi masu  fatan Alkhairi acikin zamansu.

Haka itama Mama da Aunty da sauran 'yan uwa sukayi nasu nasihan, dakyar aka banbareta jikin Aunty da Mama Wanda itama Aunty sai kukan take tayata saboda shakuwarda ke tsakaninsu.

Haka aka saka mota aka wuce da ita, tanaji tana gani, (Aure kenan! Mai raba 'ya da gidansu) bangaren Momy aka fara kaita aka danka amanarta hannunta, tarba ta mutunci suka samu daga gurinsu inda Mommy tace.

"Ai Siddiqa 'yata ce koba Aure balle da Aure, inshaa Allah zan riketa kaman Zarah ina matan Alkhairi a Aurensu" daga tayi mata 'yar nasiha sannan aka wuce da ita part d'inta.

Nan dai part d'in Haiydar nanne zasu zauna da yake dama Dady yayi tsarin ne na matar Aure da kitchen da komai, d'aki biyu a k'asa da babban parlour sai k'aramin parlor sama da d'aki biyu suma, an gyara gurin sosai inda aka k'awata falon k'asa da purple color dark and light, su kuma d'ankunan aka gyara d'aya da white and black d'aya green, sai sama d'aya na Haiydar already ya gyara abinda dayan kuma nata akayi pink, dinning na parlon k'asa yayin coffee table ke parlor sama, kitchen ma na k'asa an gyara sosai abin sai Wanda ya gani sai fatar samun zama lafia mai dorewa.

Itama Zarah an wuce da ita Argungu inda zasu zauna na sati kafin su wuce Kaduna inda Ya Mubarak ke aiki.

*10:00pm....*

Su Shamcy akayi shirin zuwa dinner wacce su Saleem suka shirya ba yadda Shamcy batayi da ita ba tace ba inda zataje k'arshe ma toilet ta shige tayi wankanta tai shirin bacci tabi lafiyar gado, dole ta kyaleta suka shirya tare da sauran k'awayenta suka wuce.

Shima Haiydar zaman shi yyi d'akin Saleem  yana waya da Fuu fashion wacce yanzu wata shakuwace ta shiga tsakaninsu.

Su kadai sukayi dinner ba Ango ba Amarya zuwa 11:00 suka tashi suka mayardasu gida inda suka koma suka d'auki Ango suka rakosa, suna zuwa bakin kofa ya sallamesu yana musu gwalo, tsiya sukayi masa sannan sukace suna hanya suma.

Su shamcy bangaren Momy suka yada zango suna maimata tsaruwan dinner duk ba Ango ba Amarya, abokansa basu d'auki rashin zuwan su komai ba dan yace Amaryarsa ustaziyace bata zuwa irin guraren dama.

Yana shiga sama ya haura d'akin sa ya fara sauka yayi wanka ya kimtsa sannan ya wuce d'akinta taji shigowar  sa don batada nauyin bacci amma tayi kaman mai bacci.

Saida ya k'arema d'akin kallo ba laifi ya mishi kyau sannan ya aje mata Leda kan bedside drawer sannan ya yatsina fuska yace "nasan ba bacci kikeyi ba, so gwanda ki tashi ga abinci nan kici in zaki iya, inba zaki iyaba can ta matsemiki" yana kaiwa nan ya fice daga d'akin....



_Still on buki fans, lobe yo all_ 😍








✍🏻

💄 Meryerm Abdool 💄

HAD'UWA DAKEWhere stories live. Discover now