[5/20, 6:22 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇 🍇🍇🍇🍇 *_HAD'UWATA DAKE_* 👉🏻🍇

369 13 1
                                    

[5/20, 6:22 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇 *_HAD'UWATA DAKE_* 👉🏻🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇

( _Based on love story_ )

*Written*
            *By*
💄 ~Meryerm Abdool~ 💄

© *_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_*
                ( *P.M.L* )


'''Bazan tab'a mantawa daku ba my mentors da bazarku nake rawa wollah🙄'''

ABDUL AAJ
           &
MAMAN USSEY.

JINJINA GAREKU MEMBER GIDAN KWARAI IRIN ABARKA, KU KAM HALIN KU DABAN NE, KAMAN YADDA KUMA KUKE NA DABAN A GARENI MEMBERS OF PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S, NA GAISHEKU, ALL ILY 😍





      *Page* 48&49


Juyawa juna baya sukayi kowa ya kama hanyar Dept, nasu sun d'an yi nisa da juna sai suka juyo same time, karaf idanunsu suka had'u a tare  suka sakawarwa juna murmushi mai kayartawa.

Ihu students sukayi suna shewa saboda abin ya burgesu, ihun ne ya dawo dasu, juyawa sukayi suna mamakin wannan murmushi da basusan ma'anarsa ba, (ni kuma nace na love oo).

Menat dake gefe tazo wucewa taji ana ihu, tsayawa tayi tana kallonsu baki sake sannan tace da wata dake gurin tsaye "me wadannan suke yi haka?" Cewa tayi.

"Baki san meke faruba halan? Ai aure sukayi shine suke b'arar da love mu kuma muna ganin sha'awa"

Tabe baki tayi tace "Ayya" amma cikin ranta sai tsinewa D one take tana cewa "Tsinanne dama sonta yake yi, amma yasa nayi mata wancen abu? Shege dan iska daga yau na daina kaunarka a raina wallah, itama shegiyar sumi-sumi kam ta Allah" ta buga tsaki tana wucewa (ni kuma nace kin samu aikinyi).

Ba wani lec, ne da yawa tayi ba dake ba'ayi resuming gaba d'aya ba, ga Shamcy tak'i ta dawo tayi nacin harta yi fushi da ita.

Bakin titi ta isa harta tari me napep zata wuce, sai kuma taga rashin dacewar hakan, wayanta ta ciro ta kirasa saida ya tsince.

Siririn tsaki taja zata shiga saiga kiransa ya shigo, d'agawa tayi jin yayi shiru tasan kuma ba maganan zaiyi ba yasa tace.

"Na k'are lec, nawa zan wuce gida"

Saida yayi yangarda ya saba sannan yace "wazai kaiki?"

"Napep zan hau mana, gashi har na taresa".

"What!! Salon a renani kenan! To jirani yanzu zanzo nayi dropping naki" ya katse wayar.

Tsaki taja tace "ko meye nashi a ciki, wai a renani! Son girma sai kace dawo mtsss".

Ba me napep hakuri tayi tare da bashi 200 ya wuce, minti kadan ya iso, shiga kawai tayi har ya kaita ba Wanda ya cewa d'aya uffan, fita tayi tare da cewa " thanks" cikin makoshi.

Ya jita amma yayi banza, motar kawai yaja ya fice ya koma skull, saboda research da yake na project d'insa.

B'angaren Mommy ta wuce direct, tana shiga Hanan da dawowanta kenan daga skull ta taso tana mata oyoyo, d'aga ta tayi tana tambayan ta skull sannan ta k'arasa ciki suka gaida da Mommy inda ta tambaye ta skull ta ansa da "Alhmdllh".

Tace " ina son d'in?"

"Yanzu ya ajeni ya koma ne".

"Ayyo" da murmushi a fuskanta, alaman taji dad'in hakan, saboda dama ta gayamai shi zai rinka kaita da maidata muddin yana gari ya ansa da to.

Nan ta zauna suna d'an tab'a hira da Mommy sai da taji kiran sallah sannan taja hannun Hanan ta wuce part d'inta.

****************

HAD'UWA DAKEWhere stories live. Discover now