Dand'ano

113 1 0
                                    

*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*

*HASKEN RANA*(meeesherh lurv)
*SARA DA SASSAK'A*(Qurratul'ayn)
*DUHUN DAMINA*(Kwaiseh
*SHAUK'I BAYAN MUTUWA*(Oum samha)
*MAFARKINA*(Munay)
*CIKIN DUNIYARMU*(Bebe'arth)

Alk'aluman nagartattu na siyarwa ne gamai buk'atar dukkaninsu zai biya 700, idan d'aya kake buk'ata zaka biya 200, in biyune 300, in ukune 400, in hud'une 450, in biyarne 550.

Zaki tura kud'in ta Accaunt number kamar haka.
👇🏼l
Firdausi Salisu Aliyu

0430001991

GTbank

Ki kuma tura shaidar biyanki ta wannan number.
👇🏼
07067364721
In katin wayane shima zaki tura shi ga wannan number.
07067364721.
Babu wani ja'inja zakiji kin tsunduma inda zaki samu novels d'in cikin kwanciyar hankali, Alk'aluman nagartattu sabon salo, sabon yanayi zaku fad'aka zaku soye za kuma ku nishad'anta haka zalika zuciyoyinku zasu tab'u domin dukkanin labaran akwai su da tab'a zuciya, kedai yi k'ok'ari kiga kin mallaki naki a hannu kada ki bari a baki labari.

_*HASKEN RANA*_

_D'and'ano daga littanfi HASKEN RANA_

_"Me ya sa rayuwa ta take tafiya ne a haka? Me ya sa kowa ba ya so na? Me ya sa mutanen gidan ba su k'aunata? Kowa na walwala amma ban da ni? Rayuwa me ya sa take yi min tafiyar wahainiya?._

_Inna duk duniya bani da kamarku keda Abba” miyasa kuka tafi kuka barni?, lokacin Dana fi buk'atarku a rayuwata?, inajin dad'i na k'alleku, ko baza ku fad'amin komai ba, inajin dad'i naganku koda andakeni baza kuyi magana ba, inajin dad'i na kalleku,lokaci da ake dukana da zagina da aibantani ku nuna baku sanni ba, inajin dad'i naganku, inajin dad'i naganku ko da Iya jimmai zata hanani abincin ci idan nazo wajenku, inaso! inaso! inaso!, Miyasa kukayi man nisa?, kuka barni cikin duniyar Mai cike da abubuwan wahala da nadama?._

_Bata aikare ba ta d'au lokaci Mai tsawo wajen siyar da abincin nata, Wanda ba kowa wajen Kuma Bata aikare da haka ba har lokaci ya jamata, gashi Bata siyar da ko d'aya ba ga yamma tayi._

_jin muryar Jamila tayi kanta tana magana cikin tashin hankali "Sultanah shine kikayi zaune Nan Kika k'i tafiya tallar ko kwano d'aya Baki siyar ba?"_

_"Wallahi a kunne iya jummai yanzu zanje na sanar Mata, Kuma kin San sauran" kafin Sultanah tasamu zarafin yin wata magana tuni Jamila tayi gaba cikin sauri da son isar da gulmarta._

_cikin tashin hankali ta suri tiren abincinta tana kuka tayi tashar isiya da abincin ko ta samu ta siyar, kuka take ba kad'an ban Dan tasan yau sai Allah idan iya jummai ta kamata._

_Wallahi tallahi iya ko sama da k'asa zata had'e sai kin samomin miji irin na Sultanah, Wallahi bazai yo ba, ba k'arya da bakiyimin ba Sultanah baza ta tab'a aure ba, ko tayi sai dai ko d'an shaye shaye ko d'an caca, Amma yanzu kiduba kiga kyauwun mijin Sultanah da kud'insa kiga fatarsa.
_kowa a garin Nan miyake cemin game da sultanah?, Ita d'in HASKEN RANA ce tafi baya kareta, wai ni kuluwa nice nazama a k'auyenan abin tsokana da izgili, ni d'iyar Iya Jummai da kowa ke shakka da tsoro, Kuma duk kina zaune wani irin kuka tasa sannan taci gaba da maganarta._

_"Wallahi bazan amince ba, sai dai kisa ya sake ta ya aureni, idan kinaso kwanciyar hankali a gidanna, wani irin kuka ta k'ara sawa Wanda yasa iya cikin tashin hankalin da k'arin bak'in ciki irin mijin Sultanah Amma ba kowa ya cuceta ba sai d'an ladi Wallahi ko zatayi yawo tsirara sai ta raba auren._
_ita bak'in cikinta duk yadda ta lalata rayuwar sultanah ta kashe Mata ita Amma wai itace yau da d'aukaka haka Wallahi da sake bazata tab'a yuwa ba da sake Dole ta tashi ko d'an saboda da 'yarta tayi farin ciki._

_zaune yak'e gaban swimming pool d'in dake malale a filin gidan daga baya shak'atawa yake k'afafuwa sa na cikin ruwan Yana Wasa dasu, dutsina nane k'anana a hannunsa Yana jifa dasu cikin ruwan, ba zato yaji a rumgumosa ta baya, kukanta yaji kawai, hannuta ya zare daga jikinsa sannan ya fito daga cikin ruwa rugumeta yayi ya fara bubbuga bayanta cikin salon lallashi, Amma ko kad'an baiyi magana ba._

_jin kukan da take Kuma yasan lallashinshi take buk'ata da tarairayarsa tare da ansa buk'atarta, saboda tasan ko kad'an bayason kukanta, Amma dan wulak'anci yayi shiru ya k'yaleta sai wani buga bayanta yake, kawai sautin kukanta ta k'ara sannan ta fara magana da cewa "Wallahi Salim nagaji ko ka amince da buk'atata ko na bar maka gidanka yanzu da me zanji?, Da halinka zanji ko da buk'atar Hajiya kasan Wallahi bazan tab'a amincewa kayimin kishiya ba ko sama da k'asa zata had'e nabaka zab'i biyu ciki kuwa Dole kayi d'aya ko na farko ko na biyu idan har kanaso, nacika burina na samu 'ya ko d'a ko na huta da jarabar Hajiya idan ba haka ba Wallahi yau d'innan Zan bar gidannan."_

_jin yayi shiru yak'i magana gashi yak'i sakinta ya wani mak'alk'aleta, ji tayi ranta yayi masifar baci cikin sauri ta hakad'e sa tayi cikin gidan cikin kuka Mai tsanani, ganin haka da yayi yasa bakinsa bud'ewa cikin wata irin murya Mai amo ya hau kwala Mata k'ira "Safnah! Safnah!"_

_jin kiran yasa ta k'ara sauri cikin parlour ta shige dama tuni tayi parking kayanta ta kawo parlour, cikin sauri ta suri gyalenta, sannan taja trolling d'inta ta fito tayi hanyar parking space, ganin haka cikin sauri ya bita Amma kafin ya k'arasa har ta shige motar ta ja tayi hanyar fita agidan._

_*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*_

Dand'anoWhere stories live. Discover now