dandano

76 3 1
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
Alk’aluman NAGARTATTU

DUHUN DAMINA...
           Maganin mai kwad’ayi!

Alk’alamin MaryamerhAbdul (Kwaiseh)

Rayuwar Abdulwahab ya samu tangard’a tun lokacin da ake iya tankwarashi, sai dai rashin mafadi ya kawo masa gib’in da har aurensa da Juwairiyya bai samu saiti ba. A rashin saninsa, rayuwarsa da ta Juwairiyyar, suna kamanceceniya, duk da nata salon tangard’an ya banbanta da nashi matuk’a. Labari ne, mai d’auke da zallar ilimi, mai nuni da illar matsalar da ni da ku zamu iya yak’i da ita. Matsalar dai bai wuce istimna’i ba, wato masturbation. Ku biyoni don jin b’oyayyar al’amarin da ke yawo da rayuwar matasan nan biyu, wanda Istimna’i ya d’aukesu, yake yawo dasu yana sadasu da wahalolin rayuwa.

MAFARKINA

MUNAYSHAT

Ko wanne bawa da irin baiwar da Allah kan azurta shi da ita, sai dai ni bansan baiwata ita zata zamto abar ruɗu a gare ni ba.

Baiwar da ta yi sanadiyyar zamtowa ta wata aba acikin duniyarmu da ban yi tsammani ba, ashe hakan wata ƙaddara ce wanzazziya da zata zamto sanadiyyar haurawa dani matattakalun girma na har abada.

Duk da cewar ban yi zato ba, amma ƙaddara ta riga fata, shiyasa a koda yaushe na kan ritsa kaina da tambayoyi shin MAFARKI gaskiya ne??

Lallai akwai lauje cikin nad'i.

Ku dai ku nemi naku akan farashi mai sau'ki dan jin ya zata kaya.

SARA DA SASSAƘA...
        Baya Hana Gamji Toho.

Daga alƙalamin:-QURRATUL-AYN

  KO wacce rayuwa tafiya take da juyawar alƙaluman ƙaddara, idan akwai abin da ya fi wahala a cikin wannan duniyar tamu shine jure ƙaddarar da ke cike da wahala.

  Sumar kansa ya shafa da hannunsa mai lafiya, tare da da daidaita numfashinsa ta hanyar dafe ƙirjinsa "ME YASA RAYUWA TA FIYE ƘUNTATAWA?"
Yana fidda sautin maganar tasa ne da rauni, yayin da hadarin idanunsa ke kwaranyar da ruwan hawaye.
 
Tabbas idan ya ce ba ya tausayin DEEN ya yi ƙarya, asalima yana kallonsa a matsayin namiji tilo da ya sanya hannu bib-biyu ya amshi ƙaddarar rayuwarsa cikin jarabta mai wuyar cinyewa.

Ku shigo littafin Sara da sassaƙa, domin ilmantuwa tare da ɗaukan darasin tafiyar da rayuwa cikin ko wanne irin halin da ka tsinci kanka a ciki, ka shiga babban jigon rayuwa wato HAƘURI.
 
_*HASKEN RANA*_
      _Tafi baya karewa.._

_*Daga Alk'alamin*_

_*AISHA MUSA MAHMUD*_
        _meeesherh lurv_

Ita Duniya juyi-juyi ce, haka rayuwa take tafiya kamar hawainiya, k'addara na fad'awa mutum mai kyau ko akasin haka, sai dai ana fatan samun cin jarabawar da ubanjiki yayi maka.

Rayuwa tana tafiya kan tafarkin k'addara tun bansan miye duniya ke ciki ba, sai dai ina godiya ga ubangijin da ya jarrabceni da hakan.

Yau gani ga mijin da duk kauyen ke cewa nayi dace, ni din HASKEN RANA ce, sai dai kash, a wajensu maganar take haka, don ni Sultanah ban san yaushe rayuwata zata daina zubar hawaye ba.

Ku biyoni cikin labarin HASKEN RANA dan jin ya rayuwar Sultanah ke warwarewa. Akwai darasi tare da sark'ak'iya, k'angin rayuwa, soyayya duk sun had'a cikin HASKEN RANA.

*BEBE'ARTH*

              *CIKIN DUNIYARMU*
           

Duniyar TEEMA NAZZ zagaye take da mutane uku amma sai da bak'in ciki da hassada gami da son kai sukasa aka ruguza mata dukkanin duniyarta, tun lokacin farin ciki ya d'auke daga kan fuskarta har sai da REESAH ta shigo cikin duniyarta, a b'angare d'aya kuma  MIQDAD Duniyarsa zagaye take da mak'iya, mutum daya ne ya zamo masoyinsa na gaskiya shima kuma sai da suka san yarda sukai suka cire shi daga CIKIN DUNIYARSA.

  Akwai zallar rashin imani, bak'in kishi, hassada da son kai.

Labarine wanda da ni da ku zamu d'au babban darasi a ciki.

Zai zo muku k'ark'ashin jagorancin ALK'ALUMAN NAGARTATTU.

GASKIYA ĐAYA

NA

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

MAHAIFINTA ya mata tabon da bazai taba warkewa ba.
Mahaifinta ya dasa mata bishiyar bak'incin dake yađo akowani dak'ik'a na rayuwarta.
Soyayya ce mai k'arfin gaske take tsakanin wannan ahalin.
Suna cikin matukar farinciki da samun dukkan wani abu dasuke buk'ata kwasam alk'alamin k'addarar su yazo musu da salon dayazamo tilas su wargaje wannan farin cikin.
Kamar yanda Abokin rayuwarta ya kasance da irin wannan tabon a zuciya.

Rayuwarsu da k'addarorinsu suna matuk'ar kamanceceniya.
Sai dai suđin suna yiwa junansu kallon Sam basu dace da juna ba.

Littafin Gaskiya đaya littafi ne da zai zo muku da sabon salo na musamman.
Abubuwa ne birjik da suka shafi al'umma, cin hanci da rashawa, amfani da talakawan matasa dan cimma buri, amfani da raunin mata domin samun wasu buk'atun rayuwa.
Zaiyi wahala kace Allah zakabi baka hađu da k'alubale ba.
Wannan k'in rashin gaskiyar ta Jaluddeen ta sanya shi fađawa mummunan hatsari wanda ya jawo masa rashin masoya makusanta.

Zamansa Hukuma mai kare hak'k'in đan adam da gaskiya ya zame wa rayuwarsa barazana takowanne b'angare bayan matsalolin da suke birjik a k'asan kirjinsa.

Kubiyo alk'alamin basakwkwata Asisi domin jin cikakken wannan labarin

K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa.

Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam.

Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi.

    Zaki samu dukkaninsu akan 700, d'aya 200,biyu 300, uku, 400, hud'u 500, biyar 600.

Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:-
07067364721

Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:-

Firdausi Salisu Aliyu
0430001991
GTB

Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:-
07067364721

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 06, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Dand'anoWhere stories live. Discover now