Babi na biyu (Sabon AlAmari)

170 13 8
                                    

Shuru ce ta biyu bayan gama bayanin Engr Umar.yayinda kowa yake saqa abubuwa daban a cikin Zuciya.

"It's been an hamazing journey,hand as hard as it is for hus to believe you are leaving,we will be assisting Hinjiniya Habib just as we did with you" group leader dinmu Osawaru dan Asalin jihar Anambra kenan na design project ya miqe daga kujerarsa ya fada ya karasa zancen sa yana duban Engr Habib.aikuwa salma daga kujerarta ta juyo mukayi dan murmushin gulmar over sabi irin ta osawaru...gashi dai shi maganar sa ba wani ganewa akeyi kasancewar yadda yake furta 'a' a matsayin 'h' Amman se ya dage lalle shi koyaushe sai anji ta bakinsa.

Nayi kokarin Chige bakina Ina dan murmusawa dan hana kaina dariyar emotional comment din Osawaru aikuwa nan take murmushi na ya tsaya cak yayin da idanuwana suka sauqa akan wasu idanuwa masu tsauri.

Na 'yan sakannin da basu wuce biyar ba idanuwa suka hadu dana Engr Habib ..amman haka naji kamar wani wanda aka watsa mun ruwan sanyi.
He's already intimidating me!

Engr Umar ya cigaba da magana na wajen tsawon minti goma yawanci shawara ce da words of encouragement akan mu cigaba da kokari tunda already mun kusa Kammala course work gabadaya abinda ya rage mana bawani me yawa bane.daga haka ya juya kallon sa zuwa ga Engr Habib don shima ya tofa albarkacin bakinsa.

Aikuwa idanuwa suka juya zuwaga kallon Engr Habib don sauraron abinda zai fada.

Ya gyara zamansa tare da miqar da kafadu looking all confident and assured ya furta "Looking forward to work with you all..,ya danyi wani guntun murmushi me cike da kasaita..:da haka dai Meeting din ya qare.

Maganganun Engr Habib were Brief ba kamar na Engr Umar.

Wasu daga cikin 'yan ajinmu suka fice domin ci gaba da lamuransu na ranar yayinda wasu suka tsaya.kamar ni na tsaya ne domin sake tattauna matsayar dissertation dina da Engr Umar kasancewar har yayi mun approving chapter one and two har na fara aiki akan chapter three ( methodology dina )kuma har nayi making inquiry on all necessities danake bukata a lab...

Na hango su Grema dasu osawaru tsaye gaban Engr Umar suna masa 'yan tambayoyi tare da fada masa zasuyi rashinsa
Some were even trying to get emotional a total unnecessary act if you were to ask me...haba jamaa se kace wasu yara 'yan undergraduate.

Salma kawata ta dan zungureni na juya nakalleta...da dan mumurshi a fuskarta take tambayata

'How did you find our new supervisor?'ta fada tare da kallo Engr Habib.

"Well...zamu gani dai idan yafara duba mana thesis." Nafada a takaice without giving my personal thoughts gudun kada nazama too judgemental tun kapin mu fara aiki.

"It looks like he can handle all of us..he seems to have a lot of self confidence" gyada mata kai kawai nayi alamun yadda.

"The confidence part is definitely true"

"Zaki fito ne?"Salma ta tambaya tare da nufar kofar fita ..batare da musu ba na rataya 'yar Jakata na rufa mata baya...da qudurin cewa yazama dole na samu gamawa da Engr Umar domin sanin makomar dissertation yayin da ya samu kebewa a office zuwa dan anjima.

Da saukowar mu muka shige libry domin inada bukatar duba "process selection" na design thesis dinmu kuma yaune deadline...a haka a haka har rana tayi Salma ta bukaci muje restaurant don ta fara jin yunwa amman nace ta bari kawai don gabadaya banida appetite...munada class din Engr BG Idris 2-4pm daga nan angam

Muka kwashi books dinmu muka fito daga libry yayinda na wuce Masjid domin sallah ita kuma ta wuce restaurant. 

Anan me kuwa bayan dawo wata class domin jiran Engr BG na dinga tsintar zancen 'yan ajinmu sunata gutsutsutsura labarin Engr Habib anan nagane cewa shima Sabbatical yazo tun daga Kano State.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 17, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Qawaa Zuci......(Labarin Zuciya)Where stories live. Discover now