Page 1&2

960 38 4
                                    

🤍🥌🤍             🤍🥌🤍

            *ᏚᎪᏞᎾN ᏆᏃᏃᎪᎻ*

    *🤝🏻ᎪNᎪ ᎢᎪᎡᎬ ᏔᎡᏆᎢᎬᎡᏚ ᎪᏚᏚᎾᏟᏆᎪᎢᏆᎾN*✍🏻📚

     _Written by✍🏻_
                Sཽaཽ'aཽdཽaཽtཽ Aཽlཽkཽaཽlཽiཽ Dཽ/tཽsཽaཽfཽeཽ
                      🅢🅐🅓'🅐🅢🅗

https://m.facebook.com/Anatarewritersassocian/?ref=bookmarks

_*BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM*_

*1⃣-2⃣*

Shiru kakeji, bakijin k'arar komai sai na saukar Ac sai kuma tsuntsayin dake cikin gidan, gaba daya zaka dauka tamkar ba kowa a cikin dakin bayan kuma ga Alamar mutun nan kana gani a kwance a kan gado, dik da kuwa irin girma da gadon yake da shi, numfashin sa kawai kesauka shima idan ba k'ura ido kayi sosai ba" bazaka dauka wanda ke lulube cikin had'ad'in blanket mai matuk'ar laushi da tsada kayi tinanin wanda ke cikin sa yana numfashi ba.

gefin ma'aikata kuwa kusan mutun yafi a K'irga suketa faman kara kaina acikin gidan, kai da kawowa suke tayi su ajeyi wancan su dauke wannan, yawancin su duk turawane, kad'an daga ciki ne bak'ak'in fata.

tako ina sai daukar k'amshi yake kasancewar mamallakin mai gidan ma'abocin son k'amshin ne sosai, bayan sunkammala komai sun tsaftace ko ina, nan dai kowa yafita sukabar masu hada barkfast kawai..

Wani dai daga cikin su naga ya duba agogon hannunsa kafin ya zarce zuwa cikin wannan haddadin daki danaga mutun kamar a kwance akan gado.

Murda k'ofar dakin yayi a hankali yanda bazai tada wanda ke bacci ciki ba, tare da shiga ciki yana takawa a hankali tamkar mai sand'a bai zarce ako,ina ba" sai a cikin bathroom d'in dake cikin dakin, ina biye dashi niko dan kawai daukar gulma, ho-ho-ho ido nazaro da k'arfin tsiya sakamakon tohzali danayi da dakin wanka tamkar ba'a duniyar nan ba, saboda gurin 'yan tsarashi yatsaru matuqar tsruwa, ruwan wanka ne" naga wannan guy na hadawa sai zabga turaruka yake kamar hauka ga wasu flowers dake cikin ruwan wankan masu matuqar kyau gwanin sha'awa da burgewa, a gaskiya bathroom dinnan yashani sosai tamkar nayi kwanciya na" aciki karna fito.😜

Bayan duk ya kammala abunda yakamata yayi amatsayin aykinsa yafito kamar yanda yashigo a hankali haka yafita batare da yatada wanda ke cikin dakin ba.

11:30 agogon dake cikin dakin yabuga dai-dai lokacin tashin sa kenan....

     ********************

Wasu 'yan matan ne masu kama da siffar larabawa ne na hango a zaune sunacin abinci ga dukkan Alama musamman akayo musu order shi daga cikin hotel din da suke kwana, abinci ne mai rai da lafiya sunaci suna korawa da lemo mai matuk'ar sanyi a hankali suke zancin su" na irin 'yan matan nan masuji da kansu da kudi, d'ayar mai suna salmat ce tacewa d'aya wacce ake kira saleemat take cemata wai nikuwa har yanzu *SAFNA* bata dawo bane??

dariya saleemat tayi irin na k'asaita kafin tace haba salmat kamar bakisan kowaye *SAFNA* ba kinfi kowa sanin ko kwana tana iyayi agaban ka'aba🕋 tana Ibada, wannan badamuwar ta bace" ba irin mu ba, tindamu rabun mu da can tun jiya da safe..

Murmushi salmat tayi itama" sannan tace hakane yana dai daga cikin halayan *SAFNA* dake matuqar burgeni uwa uba rashin daukar raini amma tanada matuqar sanyi gata duk matsayinta ba tada girman kai ina matuqar son abubuwan nan nata dama wa'anda banfada ba Allah.

Hakane saleemat tafada koni dika babana sarki ne" amma ina kwatanta halayyarta nayi koyi dasu shi yasa nakejin bayin gidan mu akace suna matuqar ganin kirkina...

dariya sukayi dukan su salmat tace hakane" nima dikda babana governor ne amma bana wani daukar kaina wani abu kamar yanda 'ya'yan wasu governor kiye.....

jin sukayi 'yan murd'a kofa aka shigo cikin wata zazzak'ar murya naji 'yanyi sallama sanye take da wata rantsatsa After dress mai matuqar daukar ido da tsada yayinda take sanyi da wani d'an karamin hijab iya kafad'unta sai nik'ab data sanya sai kuma tas"bin dake riqi da hannunta da kuma al-qur'ani mai girma.

oyoyo sukace dukansu a tare suka rungume junan su, cire nik'ab din dake fuskarta tayi.

K'alu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, anya kuwa wannan mutunce?
nafad'a a raina" saboda gigicewar da nayi har nufashina sai da ya dauke nakusan tsawon wasu seconds Kai tubarkallah masha Allah, ashe duk kyawun nan danake gani nasu salmat da saleemat ashe ga uwarsu nan, wacce ta had'a komai na mace wanda zan iya qarar da dukkan littafinnan gurin zaro muku erin kyakyawan siffar ta, dan haka kawai ku kwatamta da kanku kuga,

*SAFNA* Autar mata yarinyà mai dauke da ilimin addini dana zamani dai-dai gwargwado, ga cikakkiyar tarbiya data samu gaurin magabatanta, hankali da natsuwa da ganin girman nagaba gareta kam abun ba'a magana, rashin daukar raini dakuma maida martanin magana tamkar daga bakinta aka tsinto, tanada kyau nafin k'arfin afad'a, hmm *SAFNA* kenan K'asaitacciyar mace..

bayan tashiga gurin wanka ne tafito tare da shiryawa cikin wata tsadaddiyar atamfa color ja, tamata kyau ta kar6e fatar ta sosai tamkar kasace ta ka gudu,

Kan gado suka hadu su ukku tanacin abinci sukuma su salmat suna dannar waya tare da fira jefe-jefe a hakan har lokacin sallah yayi atare suka tashi dan shirin zuwa masallaci

*Wannan kenan...*

SALON IZZAHWhere stories live. Discover now