Part 5&6

508 26 6
                                    

🤍🥌🤍             🤍🥌🤍

            *ᏚᎪᏞᎾN ᏆᏃᏃᎪᎻ*

    *🤝🏻ᎪNᎪ ᎢᎪᎡᎬ ᏔᎡᏆᎢᎬᎡᏚ ᎪᏚᏚᎾᏟᏆᎪᎢᏆᎾN*✍🏻📚

     _Written by✍🏻_
                Sཽaཽ'aཽdཽaཽtཽ Aཽlཽkཽaཽlཽiཽ Dཽ/tཽsཽaཽfཽeཽ
                      🅢🅐🅓'🅐🅢🅗

Wattpad:saadahalkali20

  5⃣-6⃣

Atare suka fito ko waccen su fuskar ta kunshe take da fara'a yau zasuje gida, saboda sun kammala dik wasu ibadunsu sai fatar Allah ya kar'ba, kayansu kuwa tuni akayi gaba dasu.

Bankwana suka shigayi da mutanin da suka saba musssman larabawan dasuke maqotaka dasu, wasunsu harda kuka saboda sosai suka saba dasu SAFNA mussaman Alkhairin da suke musu kullum idan suka kai musu ziyara kosu, su safna idan sukaje bama abinda yafi birgesu irin yanda suka zama suci abinci atare sudinga raha kasancewar larabawan suna jin hausa kad'an-kad'an haka dai suka rabu ceke da kewar juna.

}{ *Tohhh su safna a sauka lafiya*}{

           ~<><><><><><~

Abince ne wani bature kebawa *SAFWAN* abaki a hankali yake taunawa tamkar mai had'iyar magani idan ma da eko ko taunawar sai anmasa yakeji kwata-kwata bayason duk wani abu da zai wahalar dashi shi yasa komy nashi a natse yake yinsa,
'''🤔ikon Allah sai kallo'''

Kamal ne yashigo cikin sallama yana a tsaye saida aka gama bashi abinci sannan yasame bude bakin yiwa yayansa magana "yaya kai kadai ne ake jira mutafi komai an kammala sai tafiya, ko gefen da kamal yake bai kalla ba illa ma gadonsa daya haye tare da jan blanket ma'ana sai yatashi daga bacci.

wani murmushi ne kamal yayi aransa irin na ciyonnan aransa yace amma ma guy nan ni yamaida d'an iska waton sai yaga bacci jirgin danayi mana booking yatashe abanza kenan?

Kaima Kamal zancin kakarso wata zuciyar tace zaune yaye yana zaman jiran tashin sa, nan dai yana nan zaune har bacci ya dauke sa.

sai da yashafe kusan 30 mint yana bacci kafin yatashi dan kansa koshi kiran da yaji anyine na sallah yasa yatshi dan komai k'asaitar sa dayaji kiran sallah zai aje komai ya fuskance alk'ibla.

Yamutsa fuskarsa yayi da yaga Kamal kan kujera yana bacci harzai wuce sa kuma sai yatsaya sai da ya k'are masa kallo sannan ya wuce toilet din sa.

Bayan yad'auro Alwala ne yaga har yanzu kamal bacci sa kawai yake kuma gashi kokad'a baya iya magana musamman yau ba lokacin ta bane. Ruwan da yayu alwala ya d'an watsa masa kamal saurin bude idonsa yayi kafin yatshi zaune da saure susu kanshi yashigayi da yaga Safwan ya tamke fuskarsa sosai dan ba tun yau yamishi warning akan raini ne zauna masa adaki, tohm ko yau harda bacci da kyakyawan mafarkai🤣

Am sorry yaya yace sannan yatashi a hankali yafita daga d'akin idonsa nakansa kafin ya sake wani d'an siririn tsaki wanda da k'yar yafito bakin sa, zankoyawa yaron nan hankali yace a ransa kafin ya wuce gurinda sallayar sa yake yatada sallah.

Jirgin su Safna yasamu sauka ne da misalin qarfe 2:30pm, a Airport d'in dake cikin garin abuja, zo kaga  d'inbin motocin da sukazo tararsu abin ba'ama cewa komai lallai su Safna 'yan gata ne wannan jama'a haka, babu bata lokaci ko waccen su tanufe motocin da akazo tarar ta daga gidansu tashiga aka nufe gida da ita.

             *****************

Humm abun na manya ne kenan gaba d'ya dik girman Airport dinnan kusan mutanen dake gurin idan kaduba kasake dubawa sai kayi mamaki mutuqa saboda duk wani mai fad'a aji acikin garin Abuja dama wasu garuruwa da dama, sai da sunzo taryar SAFWAN ciki kuwa harda Abban SAFNA wanda hutawarsa kenan daga dawowar taryar 'yarsa kuma yakoma tasowa dan taryar babban d'an Aminin sa, wanda amintarsu tazama tamkar ta 'yan uwan juna kusan nace duk iyalansu sunsan juna Amma baya ga SAFWAN dan shi kokad'an ko dangin Ammin sa dana Abban sa bai saniba bare wasu dan haka shi kowa bai san da zamansa ba, idan ba Abokin sa Amir ba "wanda d'an k'anwar Ammin sa ne wacce suke ciki d'aya da ita koshi dan yakasance sunye karatune atare kuma a k'asa daya, yasa Amir kad'ai yasani sai kuwa kannen sa, Kamal da Fateema su kadai ne zai iya bugun qirji yace gasu 'yan uwan sa ne tohh kuma bare wanda yayi saura irinsu .....😜
haka shima ba'a sansa ba kasancewa dik rayuwar sa ba "a Nigeria yayita ba shiyasa ba komai ne yasane wanda yadan gance k'asar sa ba,

Sai da misalin 6:19pm, sannan jirgin su SAFWAN ya sauka, tabd'i zo kaga yanda 'yan jarida suka cika gurin sai matsotsowar juna suke dan gudun kada abasu labari gaba d'aya gurin yacika ba masaka tsinke, su Abba kam kasa qarasawa yayi yana mamakin yanda SAFWAN yake da masoya haka wanda kokadan shi baiko damu da kowa ba, amma yasan soyayyar da Al-ummah ke masane ya janyowa dansa so daga garesu yaji dadin wannan karamci sosai, da qyar securities dake gurin suka samu tsayarda 'yan jarida dake kaukowa da juna Haquri aka basu akan subarshi yafuta zuwa kwana biyu sai su ayka gayyatar su ta musamman wacce insha Allah zasu same kar6uwa daga garesa, da hakan aka samu nasarar shiga da SAFWAN cikin wata Arniyar mota wacce kyaunta da tsadarta saidai kawai mutun yayi shiru da bakinsa.

         *2 days later*

Amir ne yashigo cikin dakin wanda sanyin Ac yagama ratsa lungu da saqo na d'akin wani ni emtaccin k'amshine kefita kowace kusurwa tamkar anyiwa dakin wankan turare,

tarar da SAFWAN Ameer yayi yana latsa waya gashi yayi kyau tamkar wani Aljani, kai naji dadi harka shirya ashe?

Bai kulasa ba yaci gaba da abunda yake, kai maganafa nake kaman shiru, sai asannan Safwan ya dago kansa tare da watsawa Ameer idanunsa tamkar madara tsabar haske, kafin yace "atinanina kai ba makaho bane ba da har sai kaji nashirya ko banshirya ba, tohh shafa kaji wata kila hannuwanka sunfe idanunka muhimmanci kana yawan shiga gonar da ba taka ba plss kadaina sani yawan magana banaso,

daga haka yaja bakinshi yayi shiru tamkar bashi bane yayi magana, kuma yaci gaba da abunda yake.

Ajiyar zuciya Ameer yayi sannan yace komai zakace kafada, daga kawai tambaya sai cibi yazama kari wannan matsalarkace nidai d'an saqone Abba yace maza mufito mu isa ana jiranmu kasan 'yan media nan da rawar jiki yace bayason su iskomu a gidannan gara mu isacan a Office nasu ayi komai yafi kwanciyar hankali.

Tsabb yake saurarin Ameer sai da yabari dik yagama zancinsa sannan da kamar bazai tanka ba kuma sai kawai yatashi tamkar mai ciyon jiki yayi cikin bedroom dinsa dan kawai shi komenene sai ya6ata lokaci akansa kafin yayi shiyasa yawuce cikin daki ace warsa sai yakwanta yafuta sannan zaya fito sutafi.

Ameer gajiya yayi da jiransa yafita dan kirawo Abba ko Ammi suzo da kansu dan sune kadai zasu iya fitar da SAFWAN daga cikin gidannan ace mutun shegiyar bak'ar kafuwa kamar mutanin farko Ameer keta wannan masifa a zuciyarshi kafin ya isa part din Ammi.

Tsaf tashirya cikin kayan Aykinta amatsayin ta na Babbar 'yar jarida wacce zata wakilce firar da za'ayi da SAFWAN dik atinanin SAFNA wani dattijo ne zatayi fira dashi saboda ba wai gaya mata akayi ga kamaninsa ba, kawai nuna mata akayi wanda zatayi fira dashi babba mutunne shi wanda duniyar nan yanzu akeji dashi shiyasa kokadan bata wani kawo wani abu aranta ba.

fitowa tayi ba kowa acikin parlour sai ma'aikatan da keta faman kaiwa da komowa dakin momyn ta tanufa koda taje ta taddata tana gyaran kaya.

Sallama tayi lokacin da ta tararda momyn ta tana aykin gyaran tufafinta 6ata rai taye kafin tace haba momy da kanki shine ko ki ayka akirawo haba momy ni meye amfanina agidan ni gaskiya banaso tafada cike da shagwa6e fuska.

Murmushi momy tayi kafin yace yi haquri shalele na wllh ba haka bane kinga kinata shirye-shiryen fita gurin ayki kinga bai kamata nasaki kiyi wani ayki ba kedai kawai kije Allah yabada sa'a kuma munyi waya da daddyn ki yana gaidake yace yakira wayarki akashe, kasancewar daddyn Safna baya gari yayi tafiya jiya,

Murmushi tayi wanda yaqawata fuskarta tare da bayyanar haqoran makanta guda biyu saida gefen kuncita ya lotsa kafin tace shikenan momy naji amma nayau kawai kuma insha Allah yanzu zankira daddy nima nayi miss nashi sosai tafada tare da matsowa tawa momyn ta kiss a goshi sannan tafita tana cewa momy saina dawo.

Addu'a momyn ta tamata da kuma fatan Alkhairi sosai sukeji da wannan 'yar tasu etama haka bata had'a komai da iyayin ta ba.

Tana fitowa ma'aikatan gidan suka dinga kai gaisuwarsu cikin raha take kar6a musu wasuma da sukayi kusan jika da ita har tsokanarsu take mutuncin Safna ma'aikatan gida suke gani kamar me, da haka tashiga motar ta dan ta hana driver kaita dan bataso tafison taje da kanta,

SAFNA kenan badai kirki ba, duk dukiya erin wacce Allah yahore musu amma baisamata girman kai ba tinda gashi tafi karfin komai amma da haka take fita take nemu na guminta wani lokacin idan ayki yayi ayki har cikin rana suke zama tamkar batada wani gata Abbanta da yawa yasha ganinta tanata dan neman zufa wataran cikin wahala Amma babu yanda zaiyi tinda takafe ita ayki takeso tafison itama tanema da kanta taji yanda neman Halaka yake kujifa, Allah dai yasa mudace.

Da qyara Ammin sa ta lalla6oshi tafito dashi sai faman shan kamshi yake kamarme da haka da taimakonta suka sanyashi amota suka rankaya securities na biye dasu..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 03, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SALON IZZAHWhere stories live. Discover now