Part 3&4

328 14 0
                                    

🤍🥌🤍             🤍🥌🤍

            *ᏚᎪᏞᎾN ᏆᏃᏃᎪᎻ*

    *🤝🏻ᎪNᎪ ᎢᎪᎡᎬ ᏔᎡᏆᎢᎬᎡᏚ ᎪᏚᏚᎾᏟᏆᎪᎢᏆᎾN*✍🏻📚

     _Written by✍🏻_
                Sཽaཽ'aཽdཽaཽtཽ Aཽlཽkཽaཽlཽiཽ Dཽ/tཽsཽaཽfཽeཽ
                      🅢🅐🅓'🅐🅢🅗

  3⃣-4⃣

A hankali yake motsawa akan gadon sa tamkar wani jinjiri, sannu a hankali yake yaye blanket din dake kansa" idanunsa yafar budewa a hankali kafin ya ida wartsakewa tashi yayi zaune daga kwanciyar da yake.

Wani abune naga dake gefinsa yadanna kafin ya miqi a tsaye ya esa bathroom dinsa sai wani tafiya yake tamkar wani mai ciyon kafafu, haka yayita jan kafafunsa har ya isa dakin wankan tare da rufo k'ofa.

Da shigarsa da kamar 2 mint naga wani guy ya bude daki yashigo cikin dai daga cikin bak'ak'in fata, bai zarce a ko ina ba sai gurin wardrobe dinshi ta tufafi kai subahanallah.. Kayane kala-kala naji da fadi wasu tufafine  naga yaciro masu kyau da tsari, bayan yacirosu naga ya bude wata drower ba abunda ke cikinta sai zallar turarukka haka guy nan ya dinga bin kowace drower yana dauko dik abunda yadace" da kan takalma har zuwa kan zobbansa dan kusan kullum sai ya canza komai.

saida yagama aykinsa sannan yafita.

Ya share kusan 20mnt gurin wanka baisa ranar fitowa ba wanka yake tamkar wanda baya son yinsa

Shirye-shirye su Safna keta faman yi kasancewar gobe gida sukayi tinda sunkanmallah ibadar su.

Salmat ce tashigo cikin dakin dan tadan fita ta idasa sauran siyayyar da batayi ba, agajiye tafada kan gado bayan tayi sallama tashigo" dikansu sannu suke mata, kafin saleema tace ni dad'ina dake Allah ranguwa kike nan da can kawai, asheto ki gaida Safna ita da kusan kullum sai taje ka'aba kuma tadawo a k'afa kinkuma san nisan can danan rabin tafiyar hakan bakiyi ba kinwani dawo wai wash...

saleema taqareshe zancin ta cike da zolaya had'e da dariyar mugunta, salmat wani dan abu tasamu akusa da ita tajefawa saleemat shi sai dai bai sameta ba sakamakon gocewar da tayi, cikin murya irin wacce ta wahala salmat tace Allah naso nasameki nikikewa shaqiyanci ko Allah zanrama.

Sorry dear saleemat tace" tare da matsowa kusada salmat tace bari namiki tausa nasan kingaji, banaso nafutasheki salmat tace, salon kihad'aman da mugunta dama+2 ma safna.

Safna dake ninki kaya ta d'ago kanta erin na ma tarasa bakin magana kafin tace mene? Dama+2 ni ko?
Hmmm tohh kijira asheko Allah da bakiji dadi ba, sa'anki ce ni da zakice namiki tausa kodan kinga kinkai dai+2 dani ina sakaki acikin qawaye na zakiso ki rainani karki kuskura kuma karki soma!

Tafi suka shiga mata suna dariya saleemat ce tace yayi dear dadina dake son girma jiwani yanda kika wani magana sai kace wasu irin shekaru ne kika bawa salmat kwana4 ne fa kawai momy tace ke tsakanin ku amma kin dauke son girma kindaurawa kanki, suka qara sheqewa da dariya bama kamar salmat da mamakin safna yakoma ciki.

Fita iskarsu tayi taci gaba da abinda take aranta kuwa daman iskanci ne tawa salmat sakamakon maganar da salmat tamata ta rainin wayo shi yasa itama tamata...

    ~><><><><><><><><><><><~

Tinda kan k'afafuwan sa har izuwan kan hular dake kansa idona ke aykin kallo gabad'aya lissafina yagama yankewa akan wannan tsalelin saurayi ma'abocin kyau da cikar kamala mai kwarjini a fuska mai sanyi azuciya guy yayi ba'ama magana, lissafin tsarinsa had'eda kyansa zai canye mana lokaci batare da munci gababa, mai karatu nabar maka iya kwatantawa ka kwatanta da kanka mai yuwa lissafina da naka yazo  d'aya wayar sa ce qirar iPhone 8+ ce ta dauke ruri alamar kira yashigo tsaf yakarewa wayar kallo tamkar baisan yanda ake daukar wayar ba, harta gaji ta yanke.

turare yaketa fesa kamar zararre qamshi ne keta kai da komowa mai tsafta ba mai hawan kai ba,

_*SAFWAN ISMA'EL IBRAHIM KENAN*_

cikakkin Handsome maiji da duk wani abun ji aduniyar nan *MAI TSADA* shine sunan da akafi kiransa dashi kenan musamman manyan 'yan matan dake sonsa, a office kuwa anfi kiransa da *K'asaitacce* but.. dik wannan sunan baisan anamasa su ba.

d'ayar wayarsa ce iPhone  itama ta dauke ringing alamar tana neman agaji amma yana kallo yaqi dauka gaba d'aya bakinsa ma yaqi yamotsa saboda kewyar hakan da yakeji,

*{tohhh fa wata sabuwa ankace inji......}*

Knocking akayi bayyi ko motsi ba illah wani Abu danaga ya danna wanda ke  akusa dashi murd'a k'ofa akayi aka shigo wani had'ad'in guy ne idan kaqare mishi kallo zakaga kama sak" da Safwan sallama yayi yagaida Safwan kansa nakan wayarsa bai d'ago ba bare ya amsa, jin shirun da kamal yayi ne yasa yace bro Abba ne "ke nemanka dan nakiraka baka dauka ba, dan harnayi tunanin ko yau Friday ranar da baka daukar wayar kowa sai ta Abba da Mimi, sai naga yau Sunday kuma kawai sai naga bari nazo nasanar dakai saqon Abba shi yasa nace bari nazo nasameka cewa yayi nafad'a maka wai lallai-lallai gobe mudawo gida wai zaman Cairo ya isa haka.

shiru d'akin yayi tamkar kamal bada mutun yake magana ba tsayuwar yaji yagaji da ita sai yajuya yayi fecewar shi dan yasan idan yana kwana anan tsaye yaya bazai tanka masa ba.

      _*Wannan kenan*_

SALON IZZAHWhere stories live. Discover now