MATAR LAMEER

1.9K 65 1
                                    

_____________________________

*MATAR LAMEER*
_30% TRUE LIFE FICTIONAL STORY 30%_ _AND COMEDIANS STORY 40%_

*_LATEST HAUSA NOVEL FOR 2020_*
_____________________________
*Fauziyya Tasi'u Umar*
_____________________________
Pay before read 300 single section VIP 500  recharge card MTN ta  WhatssApp  a wannan number 09013718241 ko wannan 09031307566, ko ta account number:  0255526235: Fauziyya Tasi'u Umar
GTBank.

_____________________________
4
_____________________________


__________📚Wani mugun kallo ta watsa masa tare da yatsina fuska ta qara cokalo dankwalinta gaba tacr “wato kai Lameer bakajin mgn ko ban isa dakai ba jiya jiyannan mukayi muku sulhu da wannan yarinyar arziqin Mubaraka amma yau ma dake kai dan tsiyane Saida ka qara towai meye matsalarka ne kullum ku kenan a sulhu kamar qananun yara?"

Tattare girar sama data qasa yayi yace “yanzu dai qarata ta kawo miki kenan towai ita yaushe zata fahimceni ne yanzu ace matarka ta sunna ta kasa gane matsalarka to waye zai gane kuwa" daquwa ta watsa masa ta gyara zaman mazaunanta tace “qaniyarka dan kusun uwa taya zata gane baka yi Mata ban ruwa yanda ya dace har cemin tayi fah sai kayi wata baka nemeta ba idan kuma ka nemeta din saidai kabarta da ciwon mara dakayi kuruf kuruf na minti biyar ka gama oni Kandala qanwar maza anya wannan da ba mace zaayi ba kuwa aka manta akayima abin maza kai komai naka a sanyaye"

Wata uwar kunyace ta kama Lameer kamar qasa ta tsage ya shige shikam ya shiga uku da barbada a dangi tun yana boyewa iyayensa matsalarsa yau gashi Mubaraka ta tona masa asiri ta yaye masa zani a kasuwa shiwai wacce irin mace yake aure mara sirri bata riqe nata bama bare ta riqe na wani to waima yaushe ma sukayi auren ne duka duka har yanzu basu rufa shekara uku ba da yarsu daya amma duk ta tallatashi a dangi bayan shima bashi yayi kansa a hakaba hakanan ya tashi yaganshi bashida qarfin sha'awa.

Ruwa yaji Hajiya ta watso masa tace “soko sakarai tashi ka bacemin a guri nikam na haihi Ladidi da hula har mace take kawo qararta dubi jikinka duk wani farin abu ya bushe kamar wani Fadwah yar cikinka ma tahika natsuwa"
Kallon jikinsa yayi da sauri yana tunanin to meye a jikin nasa tunawa yayi da yanda suka rabu da Hauwa yar fillo dutse a hannun riga baisan sanda yayi murmushi ba tare da shafa kansa yace “nono naje siyo mana rugar Sambajo a garin Alqalawa wlh wata sokuwar yarinya Hauwa tayimin barinsa a jikina wai kawai saboda by mistake na taba hannunta a shirmenta wai goggonta tace idan kado ya tabata mutuwa zatayi"

Dariya sosai Hajiya takeyi tace “dada fillo bazai waye ba batasan kaima hakan take ba" fara'ar fuskarsa ce ta dauke ya tsuke fuska idanunsa ya kada yayi jajir yace “zan daina zuwa gidan nan Hajiya tunda nayi aure bantaba zuwa gdannan na tafi da farin ciki ba kullum sai kin fadamin kalma mara dadi akan lalurata Hajiya idan ban samu tausayi dajin qai a gurinki ba a gurin wa zan samu?"
Binsa tayi da kallo cike da sanyin jiki kuma fa mgnr dan nata haka take kamata yayi take kwantar masa da hankali tabe baki tayi tace “hotiho kawai"

__________Horn yaketa dokawa a gidan nasa kafin maigadin yazo ya bude masa ya shiga yayi parking ya dauki kayan dayazo dasu ya bude qofar parlourn ya shiga TV tanata aiki ga yarsa nan Fadwah tanata baccinta a saman kujera ita kuma uwar bata parlourn.
Iska ya furzar ya nufi qofar dakin ya kama jarmlock din amma sai yajishi a kulle yayi Knocking ya juya ya shiga kitchen ya nade hannun rigarsa ya fara jera naman da yazo dashi a ciki ya koma kan kayan miyan Suma yaji an bude qofar parlourn an mayar an rufe, to be kawo komai a ransa ba saboda zuciyarsa ta tafi tunanin Hauwa wanda ya addabi zuciyarsa cikin kwanakin nan ko kwanciya yayi itace da sakarcinta sukeyi masa yawo a kwanya saidai yayita zuba murmushi shi kadai gashi gobe zaiyi tafiya zuwa sounth Africa zaiyi missing dinta sosai.


Baiji shigowarta ba sai ji yayi ta bugeshi ta baya ta wucce ya dago manyan maganansa ya kalleta ta daga masa hannu tace “oh sorry mistake ashe ka dawo" murmushin kawai yayi ya matsa gabanta yace “naji saqonki na gode waike Mubaraka yaushe zakiyi hankali ne ki riqe mana sirrinmu kinsani fah nafi kowa son naga na zama jarumin namiji wanda bakeba zan iya gamsar da wasu matan ma amma ban samu wannan damar ba ya kikeso nayi don Allah kina gani kullum cikin neman magani nake kuma kin sani ko banyi sex ba Ina iyakar qoqarina naga na cire miki kewa amma komai nayi miki bakya gani saboda kawai wannan matsalar  Mubaraka mata da yawa irin damarki suke nema sun rasa kinga ke ba rashin ci ba ba rashin sutura ba duk abinda kikace shine nakeyi miki Toni meye ya hana ki karbeni a yanda nake bayan kin sani abubuwa da yawa naki bayimin sukayi ba Amma saboda kada tawayar tayi yawa nake qyaleki yanzu idan baki rufa asirinmu ba a duniya waye zai rufa?"

Tabe baki tayi ta juye indomie dinta a flat sai yanzu ma ya lura da yanda gashinta yake a hargitse shi dama ba kirki ba, kafin yayi mgn tace “dallah malam kauce na wucce" matsawa yayi ta wucce har takai bakin qofar yace “yinin yau banci abinci ba Ina abinci na?" Ko kallon arziqi bai samu ba tayi ficewarta.
Ajiyar numfashi yayi ya dauki yourghut da cake ya fita ya nufi dakinsa dake sama abin takaici da mamaki dakin kaca²  gadon harda danshi alamun baa dade da tashi akai ba ya ajiye yourghut din ya fara gyara dakin ya gama ya shimfida sallaya yaci abinda zaici ya miqe yayi wanka ya dawo ya dauki laptop dinsa ya fara aikace²nsa sai wajen daya sannan ya kwanta saime?

Zuciyarsa taqi hutawa da tunanin Hauwa da zarar ya rintse idonsa kallonta yakeyi matse jikin mota ya hade jikinsa da nata yana sauke mata kiss a kuncinta jikinta na rawa tunaninsa gabadaya ya karkata ya koma Rugar Sambajo qauyen su Jiddoh yasan dai bai barta da matsala ba tunda ya biyata kudin nononta da wautarta tasa ya zubar da haka ya kwana ko cikin baccinsa itace wai tana shafa gemunsa tana cemasa “I LOVE U My Lameer" shikadai yaketa zuba murmushi yana qara qanqame pillow.



*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*

MATAR LAMEERWhere stories live. Discover now