_____________________________
*MATAR LAMEER*
_30% TRUE LIFE FICTIONAL STORY 30%_ _AND COMEDIANS STORY 40%_*_LATEST HAUSA NOVEL FOR 2020_*
_____________________________
*Fauziyya Tasi'u Umar*
_____________________________
Pay before read 300 single section VIP 500 recharge card MTN ta WhatssApp a wannan number 09013718241 ko wannan 09031307566, ko ta account number: 0255526235: Fauziyya Tasi'u Umar
GTBank._____________________________
*15*
_____________________________*LAST FREE PAGE*
________📝Cikin tausayawa Inna Jumme tayi masa gdy ta nufi hanyar da zata isar da ita gda tana zuwa ta tarar da Jiddoh tsaye tana leqensu ta cafketa ta.
Juyowa tayi cikin muguwar kidima tana ganin Inna Jumme ta sauke ajiyar zuciya tace "inna Kado tausayi yake bani wlh kamar nayi masa kuka yau har qwallah naga yanayi dazun fah"Kamata tayi tare da daukar ledar kayan suka shiga suka bajeshi a tsakar daki Jiddoh ta rinqa bin kayan da kallo kayane bana wasa ba ya hado Mata harda dogayen ruguna turaruka hijjabai da takalma sannan kayan kwalliya hatda relacxer ta manya guda biyu.
Wani tsalle tayi tace "Aradun Allah wannan shi zan rinqa shafawa nima jikina ya koma irin nasa ya daina kaushi da kirci Inna Jumme jikinsa fa shi har wani danshi yakeyi kuma duk jikinsa gashine irin na yan majigi"Daquwa Jumme tayi mata tace "ke ar wannan ai saidai abawa Gwaggonki amma yayi miki yawa a man shafawa irin nasa farin nan nefa ke kuwa ai farace"
Turo baki gaba tayi tace "aa ne yaseen shi meye yasa baiyi farin ba nidai kibani abuna na bude na gani" mangari takai mata tace "uwariyonki ko sille baki tabawa cikin kayan nan nasan baffanki bazai bari ki karba ba ki bari mu boye sai mu nunawa Gwaggnki kudin kinsan su bakinsu daya da Ardo fah"Shiru tayi kamar me nazari kafin ta kunto kudin daya bata kel kel dasu yan dari bibbiyu har na dubu ashirin ta zaro ido tace "Inna jaka dari ce mun shiga uku siyemu zaiyi fah"
Karba Inna tayi ta qirga jikinta na rawa tace "mun boni Jiddoh jaka dari uku da hamsin ya bamu Ina zamu kaisu?...."
"Ku kawo nan sukaji an ambata tare da bude labulen Ardo ya shigo a fusace yace "wato na lura kema kina daya daga cikin masu budewa yarinyar nan ido da kudi ko to bari kiji Jumme aradun Allah ko Moddibo ubana daya kawoni dunniya zan iya dagawa sanda akan wannan shegen yaron me idon agwagwa"Wartar kudin yayi da qarfi a hannun Inna ya fita da sauri duka suka miqe suka bisa ya nufi madafi da aka balbala wutar kashin shanu ana girki ya cusa kudin.
Inna Jumme tace "Ardo sheden ka qona da wuta oye Ardo kanada hankali kuwa jaka dari uku da hamsin fah Ardo"
Itakuwa Jiddoh durqushewa tayi a gurin ta rusa ihu tace "na shiga ukuna Baffa ka qona masa kudinsa wayyohh Kado dama ban karbar maka kudinka ba Baffa me zance masa...."Sanda ya daga zai maka mata Gwaggo ta tareshi tace "oye Ardo diyagga da gaskiyarta wannan qiyayya taka da yaron nan Lameeru tayi yawa koma meye ai bai kamata ka huce akan kudi ba yanzu idan yazo yace a biyashi me zaka bashi"
Hayayyaqo Mata yayi yace "ya kada galkena ya tafi dasu ai dama ba yau suka saba kashe mana shanu da hada baki da barayin burtali su kada mana shanu ba aradun Allah Hari da Jumme kowacce ta sake sakan baki akan mgnr makirin yaron nan jikan sarkin noma qur'anin Allah saita tafi gdan tsohonta"Yana fadin haka ya juya ya shiga dakin ya dauko kayan kwalliyar ya fita dasu Jiddoh ta bishi da sauri cikin tashin hankali tana kuka tana fadin "ayyah Baffa kada ka rabani da kayan kwalliya na nima so yake nayi kyau na zama yar gayu...."
Bai tsaya sauraronta ba ya zubasu a wata tsohuwar rijiya ta qarasa da gudu ta leqa rijiyar ko hango batayi saijin zubarsu ciki tayi ta zube a gurin ta dora hannunta akanta ta runtuma wani ihu tare da fizgar ledar ta rungume a qirjinta shi kuwa Ardo ya angijeta ya wucce abinsa ya barta rungume da leda tana kuka tana kirar "shikenan kayan kwalliya na sun tafi rijiya Kado yaushe zaka dawo ka kawomin wasu..................*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*

YOU ARE READING
MATAR LAMEER
General FictionLabarin wani mutum da baya iya gamsar da iyalinsa hakan yasa suka samu damar cin amanarsa. Shin ya zata kasance a garin Rugar Sambajo Baffa Ardo zai bawa Lameer auren Jiddoh ko kuwa zaiyi sadakar da ita?