MATAR LAMEER

1.9K 58 1
                                    

*25*

Cire hannunsa yayi daga abinda yakeyi ya zuba Mata ido duk wannan uban surutun da takeyi idonta ruwa yake zubarwa, girgiza kai yayi ya gyara zama ya yago naman yakai mata bakinta ta kawar dakai ya Kira sunanta ta dago yayi ajiyar zuciya yace.
“Duka zanyi miki idan bakici abinci ba banson qananun iskanci" ai kamar ya zugata ta sake rushewa da kuka taja da baya tace “ni wlh bazanci ba ni tausayinta nakeji"
Wani takaici ne ya sashi zama kawai yayi watsi da iskarta yaci namansa sosai saida yayi hani'an sannan ya miqe ya shiga bathroom yayi brush.


Dawowa yayi ya debe kayan dake gurin ya fita dasu ya shiga dayan dakin ya cire kayansa ya rage dagashi sai boxes ya nufo dakin hannunsa dauke ta bottle na ruwan swan ya bude qofar ya shiga.
Tana zaune inda ya barta ta ta dunqule guri daya tanata rawar sanyi ya kalli A.C yaga a qure take ya matsa ya rageta ya kashe glub ya kunna deem ya matso gabanta ya sanya hannunsa ya dagata ya dorata a katifar yana shirin kwanciya ta wuntsilo daga katifar tana wani haki kamar wacce tayi gudu, fasa kwanciyarta yayi ya zuba Mata ido.


Miqa Mata hannun yayi taja da baya yace “kizo mu kwanta dare yayi" wata alkafura tayi taja baya tace “waye zashi kwana dakai? Tabdi kai kanama rainamin hankali godode dakai na kwanta tare dakai ni kama fita daga dakin nan bazan kwanta da qato a daki daya ba salon tambarin iskanci ya fitomin a goshina.
Wannan karon yarinyar ta kaishe qarshe saboda haka ya matsa zai kamota ta janye ya qara matsawa ta janye har saida sukakai qarshen katifar ya tunkudata kai yabita zai danne ta mirgine gefe jikinta na rawa ta rushe da kuka tace.


“Ni kada ka fado kaina ka karyamin kwankwaso don Allah ka tashi ka fita bazan iya kwana tare dakaiba" miqa yayi ya gyara kwanciyarsa yace “babu inda zani in kinga dama kiyita tsaiwa a gurin amma ki sani kuma ki rubuta ki aje duk wayon amarya watarana sai ansha manta Hauwah bazan takura miki ba amma akwai ranar qin  dillanci"
Daga haka bai kuma cewa da ita komai ba yaja duvet ya rufe jikinsa  ita kuma ta zauna a qasa idan tayi kukanta me isarta saita dago ta kalleshi da haka har bacci ya dauketa ya tashi ya dauketa a hankali ya kwantar da ita.


Shima kwanciya yayi ya hada jikinsa da nata yana shafa kanta a hankali zuwa  cikin gashinta yana shaqar kamshin jikinta da haka yayi musu addu'a bacci me dadi ya daukesa tattare da wani matsanancin farin ciki yau Allah ya cika masa burinsa gashi ga Hauwan sa shimfida daya a kwance.
Yana manne da ita hannun daya sanya cikin gashinta ya mayar dashi gasan mararta ya rungumeta hannu biyu a haka suka kwana, Kiran assalatu ya farkar dashi ya janye jikinsa a hankali ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala ya dawo ya tasheta daqyar yana shafa fuskarta tayi miqa tare da bude idonta.

Ai a zabure ta miqe tace “waye ya dawo dani nan?" Murmushi yayi yace “nima tambayar da nakeyi kenan waye ya dawo dake nan kikazo kika naniqeni harda wani rungumeni ke dadi miji" murguda baki tayi tace “a tsinewa me qarya" zaro ido yayi tare da kwashewa da dariya yace.
“Idan kika tsine kanki zaki tsinewa kiqi albarka yarinya ni tashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah" bathroom din ta shiga ta tsaya tana kallo can ta tuna inda taga ya taba jiya itama ta tabashi ruwa yazo tayi alwala ta miqe ta fito.


Tana fitowa ta tarar dashi ya idar da raka'atainul fajr yace “kinyi wanka kuwa" yatsina fuska tayi tace “to ba jiya nayi wanka ba kuma yauma sai nayi" daga Mata kai yayi yace “eh kullum ma sai kinyi zo muyi sallah sai kije kiyi"
Noqe kafada tayi bai kulata ba balle suyi tazo sukayi sallar suna idarwa yace “tashi kije kiyi wanka" ita kuwa ta zame ta kwanta ta tace “nifa bazai yuwu ka takuramin ba naga jiya da dare ka matsamin saida nayi wankan nan sannan yauma kace sai nayi ni ka mayar dani gurin su Baffa na ma na huta da jarabarka"


*UMMUH HAIRAN CE...✍️

MATAR LAMEERWhere stories live. Discover now