page 1

35 1 0
                                    

💅🏻💅🏻 SLAIM💅🏻💅🏻

Free book

By

Miemie Muhammad

Page 1-5


Kallonta tayi sama da qasa cikin bacin rai sannan tafurta "biyo ni ciki" dakin da matan ta shiga nan itama ta shiga.

Dakine mai dan girma muta ne maza da mata kowa na zaune akan table dinsa dake dauke da littattafai sai kuma yan tsiraru dake kai komo.

Inda matan ta taje daidai wani table da bah kowa, zama tayi akan kijeran dake wajen batare da'an bata izinin zama bah.

Matan dake mgn da wani ne tajuyo da kallonta wurin cikeda mamaki take kallon wurin don koh kadan bataga wata sanye da uniform bah balle tayi tunanin tabiyota, ahankali take bin dakin da kallo idonta ya yakai inda take zaune cikin tsawa tafara cewa "SLAIM ke wace irin yarinya ce kwata kwata bah kya ganin girman na gaba dake,yanzu ya dace ki zauna akujeran malaman ki" wace akira da SLAIM ne tafara magana cikin muryanta da bayada amo sosai tace "cewa fah kiyi na biyoki so kikeyi na tsaya atsaye sakace jami'ar tsaro" kallonta matan tayi da nufin yin magana amma kafinta furta wani abu saita taji wani murya daga bayan SLAIM nacewa "malama da Allah kuyi haquri da halin SLAIM" dukan su kallon qofan suyi da ajiyan zuciya Slaim ta sauke ahankali kafinta ta kau da kanta gefe qarasowa yayi inda suke tsaye malaman ne ta cigaba da cewa "malam Ibrahim saidai fah kuyi haquri wannann karan amma bazamu cigaba da zama da wannan yarinyan amkarantanmu bah mugaji bazai taba yiwuwa bah ace kullum sai munyi shari'a da itabah, saboda 'yar ka kullum makrantan nan cikin tashin hankali yau tayi da wannan gobe da wannan bazai yiwuwa gaskiya" ta qare maganan tana kallon SLAIM dake gyada kai datun fara maganan ta ta maqala earpiece akunnenta.

kallonta yayi cike da takaici yace "wato bazaki bata haquri bah?" Bata dago ta kalleshi bah ballantana yayi tunanin zata tankamai bah, hannu malaman tasa tatureta tareda fadin kifita awurin nan" cikin tsawa tayi maganan, SLAIM da mp3 dinta yafadi battery dinshi suka wayse aqasa ta dago kai takalleta tafara cewa "karki qara tabani koh kuma kice zakimin tsawa danni yanzu bah daliba bane" tana kaiwa nan azancenta tafara qoqrin dauko mp dinta da battery din tana gamawa ta fice awurin batareda ta kalli inda suke bah, malaman ne tayi qarfin halin cewa "kaga irin halin 'yar taka bah?"ajiyan zuciya ya sauke mai qarfi ya qara bah malaman haquri hade da ficewa jiki asanyaye.

Ita kuwa tana fita daga cikin makarantan ta nufi wata qaramar mota dake fake agefen gate din makarantan inda ta zauna akujeran gaba dake gefen driver, mintuna qalilan da shiganta motan malam Ibrahim yashigo cikin motan koh kadan bata daga kai ta kalli inda yakebah.

Tuqi yake ahankali kaman yana lallaba motan, SLAIM da kunninta ke maqale da earpiece ta dago ta kalli hanyan da suke fuskanta dauke da mamaki tafara cewa "ina zaka kaini?" Ta hurgo mai tambayan batareda ta kalli inda yakebah, shima cikin halin ko inkula yabata amsa da "wurin Inna zan kaiki tunda ke ba'a isa dake bah bakya ganin kowa da gashi kowa kin rainashi kowa sa'ankine toh can zan kaiki ku qarata inyaso idan na kaiki karki zauna kitafi yawon balbal dinki nagaji da ire iren halinki arayuwa" ajiyar zuciya SLAIM data kafeshi da ido ta sauke hade dacewa "wurin Inna?" Ta tambayi kanta tsaki ta ja kafintayi kwafa.

Hannu yasa ya tallafe bayan kanta hade da cewa "ke wace irin yar iskan yarinyace, komai amiki bah ayi miki daidai bah" kallonsh kawai tayi tareda kauda kanta gefe batareda tace dashi komai bah. Tunzura yayi da abinda tayi mai nan ya qara kai hannu ya shiga dukan, ita kuwa batayi yunqurin hanashi bah kaman yadda batayi yunqurin bashi haquri bah.

Saida yakaimata duka sama da goma sannan ya qyaleta, kallon fuskanta yayi yaga bako alaman hawaye acikin su tsaki yaja sannan yafara cewa "aikin banza kume amata batayin kuka" dagowa tayi tabkalle shi sannan tace "ya za'ayi nayi kuka bayan kukan rashin mahaifita da nayi bah abinda zanqara zubarma hawaye" tsayawa tayi da maganan na ɗan wani lokaci kafin tace "kun kashemin ita hakalinku ya kwanta ku mori rayuwanku" ta kai maganan hade da fashewa da kuka mai tsuma zuciya, ahankali ta ɗago ta kalleshi tacigaba da cewa "bazan ta6a faranta maka ranka bah" shuru motan ya ɗauka bakajin komai sai shesheƙan kukanta dake tashi ahankali.

Adaidai wani dan madaidaicin gidan yatsaya da motanshi bah tareda yakalli inda take bah yafice amotan. Kayanta daya ɗauko tunda aka kira shi amakarantan su Slaim ya shiga fitowa dasu daga motan.

Cikin sayin jiki Slaim ta biɗe motan ta fito ta tsaya batareda wani ya tanka ma wani acikin su bah mahaifinta ya juya da niyan zai koma cikin motan. Slaim ce ta fara magana cikin wata siririyar murya da take cike da rauni "bazaka shiga ku gaisa da Inna bah?"

batareda ya kalli inda take bah yace"meye ruwanki, bazan shiga bah" ya bata amsa haɗe da shigewa cikin motan shi ya mata key sannan yabar ƙofar gidan. Slaim durƙushewa tayi abisa gwiwwowinta tareda sake wani irin marayan kuka mare sauti.

SLAIMWhere stories live. Discover now