FOUR

1.8K 92 0
                                    

Saurin d'aga kansa Dr Khaleel yai, yana duban Inna Bilkisu. Jaddada kai yai alamun yayi na'am da zancen, Murmushi ya fad'ad'a akan fuskar sa yace,

"Wannan abu yayi Inna..Wallahi yayi, dama na jima ina son had'a Saifullahi da wata acikin yaran nan, sai dai duba da su d'in duk yara ne duka- duka sha biyar suke, kuma ko gama makaranta basu yi ba."

"Haka ne.. Amma ai ana aurar wa ko k'asa da hakan, sai dai yanzun ba kamar lokacin mu bane tunda inaga Islam ce ma kawai tayi shekaru goma sha biyar ko?"

"Eh haka ne Inna, ashe akwai tazarar shekara d'aya tsakanin su da Hafsat, ita Hidaya ce dai suke sa'anni da Islam."

"Eh..To amma fa ba cewa nayi lallai ba, ba kuma cewa nayi dole ba, kuyi shawara da d'an uwan naka yadda kuka ga ya dace sai ayi hakan."

"Haba Inna, ai wannan kyakkyawar shawara kika bayar kinga dama fa aiki yake yi, duk sa'annin sa sunyi aure, kuma shine dai-dai da Nusrah, saboda kinga ta gama komai na karatu, rantsar da su kawai xa'ai watan gobe su zama lauyoyi.."

"Masha Allahu, Allah ya sanya albarka a abinda aka karanta. Munyi waya da wannan yaron, (Ya Bala) yace shima yau zai shigo Habujan, amma ban sanar masa ba tukun sai yazo sai ayi komai a gama ko?"

"Kwarai kuwa Inna.. Hakan yayi wallahi sosai, Allah ya k'ara miki lapiya da nisan kwana mai amfani, Allah ya jikan Malam (mahaifin su) yasa aljannatul firdaus makoma ce agare shi."

"Ameen ya Allah.. Allah yayi muku albarka"

"Ameen Inna..Bari naje ciki na gaya musu a yiwa Ya Bala girki kafin ya k'araso."

"Eh hakan yayi. A gaida su"

"Za suji Insha Allahu, yau mazajen naki basu shigo miki bane Inna?"

"Ni nace abarsu garin ya d'an rufa tukun na, sai akawo min su, kaga yanzu da d'an sanyi yau."

"Eh haka ne kam.. Toh bari naje Inna sai na dawo."

"Yawwa d'an tsaya.."

Gani yai ya tsaya daga tafiyar daya soma yi ya dawo ya tsugunna cike da girmamawa yace.

"Maganar su Karimatu ne, dan Allah nasan kana adalci sosai a tsakanin su, kar ka gajiya da hakan, ka cigaba . Allah yayi maka albarka." Kansa a k'asa cike da girmamawa yace,

"Insha Allahu Inna..Na gode k'warai"

Mikewa yai ya fita bayan ya mata sallama, ko bata fito ta fad'a ba, sarai yasan kishi ne ya rufe idanun su jiya suka zo suka yi masa sharri. Murmushi kawai yayi yana cewa,

"Mata.. Kai Allah ya shirya mana zuri'a"

Sashen Helwa ya fara shiga don anan yake, ita kadai ce sai ma'aikatan ta don 'yan biyun ta ma kullum a sashen Haj Aysa suke wuni, sai dai bacci ya dawo dasu. Wani lokacin ma acan suke baccin.

Sun d'an taba hira nan yake sanar mata zuwan Ya Bala. Kitchen ta shiga bayan fitar sa don yin abincin tarbar yayan mijin nasu. Daga nan ya nufi sashen Haj Aysa, ya jima yana d'auke da 'yan biyun sa, gefe kuma su Arfat sai d'ane k'afafunsa suke yi, Islam dake kusa dashi ta zumburo baki,

"Daddy..."

"Na'am Mamana"

"Daddy yanzu kafison su Areef. Sam baka sona kaman da" Ta k'arasa fad'a tana shagwabe fuska.

Murmushi yai yana riko hannun ta da yake a kusa dashi take, cikin muryar lallashi yace,

"Haba nina isa?! Mamana ai kece gaba da komai, kawai dai kinga su ne 'yan fari a maza amma kuma ai kece 'yar auta a mata ko?" 'Daga kai tayi tana murna.

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now