FOURTEEN

1K 92 0
                                    

Saifullah na barin gidan ya nufi gidan su Khaled kansa tsaye, jijiyoyin kansa duk sun tashi, bugun zuciar sa ya canza, Sosai kansa yake ciwo tamkar zai bar gangar jikin sa. Ko gyara parking dai-dai bai yi ba, yai fitowar sa yana mikawa driver Aunty Lateefa mukullin, da hannu yai masa alama da yai parking dinta, kansa tsaye ya wuce part din Khaled na da, wanka yayi ya 'daura alwala ya yi sallar nafila, ya jima zaune akan prayer mat yana addua, kafin ya mike jiki sanyaye ya nufi sashen Aunty Lateefa. Samun su yayi a zaune itada Humaira, suna shan fruit salad, zama yayi a kujerar mutum biyu dake kusa da wadda Haj Lateefa take, Humaira ta gaishe shi ya amsa, ta mike ta haura sama abunta, bin bayanta yayi da kallo, sai yanzu ya lura fushi take dashi, sunku yawa yayi yana gayda Haj Lateefa, ta amsa murmushi fad'ad'e a fuskar ta kafin tace,

"A kawo maka abinci auta? Favorite dinka a kai, faten dankali, wannan karan an saka kifi."

"Okay Aunty, a zubo amma kad'an."

Mikewa tayi ta shiga kitchen din su dake k'asa, mintina kadan tadawo da food flasks guda biyu, da plate da serving spoon, sai wani jug dake cike da zab'o da yasha kayan had'i aciki anyi decorating dinsa da ice blocks. Zuba masa tayi yace ya isa, ya 'dan caccakuna ya barshi, tana hankalce dashi, zobon ya sha sosai, ya goge bakin sa da tissue yana hamdala kafin yace,

"Aunty! Wajen ki nazo fa"

"Toh auta, Allah yasa alkhairi ne"

Murmushi yayi, yana shafa 'keyar sa, kafin yace.

"Aunty..a..Akan maganar Islam ne"

"Islam kuma? What about her?"

"Aunty nasan kin sani, dan Allah temako na zaki yi, ki bawa Mami hak'uri."

Murmusawa Haj Lateefa tayi kafin tace,

"Auta ka daina zurfin ciki kaji? Damuwa na damun ka, ka samu wani kuyi shawara, sai kaita barin abu a ranka, sai yaci yacinye ka sannan kazo kana magana a 'kurarren lokaci, in dai akan Islam ne gaskia bani da abun da zan fada maka, Tunda zance ya koma wajen manya."

"Aunty kiyi hak'uri, ni fushin da Mami take dani yafi damuna akan komai wallahi."

"Wato auta har yanzu baka fara saka Islam a cikin ranka ba kenan? Kuma fushin da Mamin keyi ai duk akan hakane, ni banida abunda xan iya maka auta, kai zaka dage, fight for ur dear self, kayi lefi admit it, shikenan fa, amma duk wannan 'kunbiya-'kunbiyar da kake ba zai maka amfani ba.."

Tana gama fada ta mike ta shiga kitchen, domin halin Saifullah na 'kona mata rai, gashi ta sanadiyyar ta akai auren, ko kadan ba taso hakan ya kawo ruguntsumi ko rabuwar kawuna. Tana shiga kitchen ya hau sama wajen Humaira, a parlorn sama ya tarar da ita tana danna waya, kallo d'aya tai masa ta mai da kanta kan littafin da take karantawa. Zama yai a kujerar dake kallon tata kafin yace,

"Humaira..."

Ya fada cike da damuwa, 'daga idanu tai ta dube shi, kafin ta ajiye littafin agefe tace,

"Ya saif.."

"Kin san meyasa nazo wajen ki?"

Girgiza kai tayi alamun a'a, ya jaddada kai shima kafin yace,

"Akan 'kawar ki ne Islam, deep down na san kina 'boyemin wani abu, ki fadamin me na yi mata? Ita Islam din."

"Babu komai Ya Saif.. Allah ni Islam bata fad'amin komai ba"

"Toh waye ya gaya miki? Ki dena nuna bakisan komai ba, kin san halina dai sarai."

Sanin indai ya canza yanayin sa bazata ji dadi ba, yasanya ta saurin bashi labarin abunda taji game da maganar da Islam suka yi da Lee, ta 'kark'are da,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now