free page 4

179 9 0
                                    

🧕🏼 JUMANATU 🧕🏼

  Story & writing by

RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

بسم الله الرحمن الرحيم

  Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ƙai.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Free page

4️⃣

      Ganin yanda take ta faman lumshe ido yasa ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya yi shiru  wani restorant ya ya shiga da su ajiyar zuciya ta yi saida ya waigo ya kalle ta kauda kanta ta yi gefe ta fuske parking ya yi sannan ya fito itama fitowa ta yi ta bishi a baya   zama ya yi tsaye ta yi wayarsa ya karɓa a hannun ta ya fara dannawa saiga Waiter ya zo yana tambayar su me za'a kawo masu menu ɗin hannun sa ya karɓa  ya zaɓi abinda za'a kawo masa ya miƙa masa juyawa ya yi ya bar gurin kallon ta ya yi sannan ya ce "wai ko kin fara aikin soja ne?"

     Bata bashi amsa ba sai zama da ta yi abinci aka kawo masu komai biyu kallon sa ta yi ta ce "sir Ammat banida kuɗin biyan wannan abincin ka bari idan mun fita idan naga maisaida abinci a hanya nasiya."

      Bai ɗago ba ya ce "zakici ko sai kin gama surutu?" Cike da fargaba ta fara cin abincin sai gata ta zage tama manta da yana gurin ta ɗirki abincin ta shika tsayawa ya yi yana kallon ta ganin ta kusa cinyewa ga nashi ko rabi baiyi ba ya ƙoshi saida ta cinye nata tas ta kora da lemu sannan kuma tasha ruwa ɗagowar da zatayi suka haɗa idanu sauke kanta ta yi ƙasa dan taji kunya ta shi ya yi yaje ya biya kuɗi sannan suka fito   shiru ba wanda ya ke magana a cikin su har suka kai office  shine gaba ita kuma tana binsa abaya har suka shiga tana kallon Halima dake laɓe bayan fulawa da aka ƙawata gaba bolding ɗin dashi bata bi ta kanta ba ta shige ciki numfashi Halima ta sauke tana cije yatsa sannan ta gyaɗa kai ta shiga ciki itama  tana zaune sai ga wani yazo yana son ganin Sir Ammat waya ta ɗaga zata kirashi sai kuma ta kalle shi ta ce "wa za'a ce masa?"

     "Kice masa Alhaji Wadata ne." Kara wayan a kunnen sa ta yi ta ce "Sir Wai Alhaji Wadata nason ganinka." Wayar ta sauke ta ce "ka shiga."

      "Idan na fito zamuyi magana gaskiya kinada kyau." Bata tanka masa ba har ya shiga ciki wayar ta ta ɗauko ta kira Ummi ringin biyu aka ɗaga "Ummina yakike?"

    "Lafiya lau Jumanatu na ya aikin?"

   "Alhamdulillah Ummi. ya kika sami su Aunty Sadiya?"

    "Duk suna lafiya. Zaki sami zuwa kuwa?"

     "A'a gaskiya saidai ranar Lahadi dan duk agajiye nake."

    "To shikenan babu laifi."

    Sun gaisa da Aunty Sadiya da ƴar gurin ta Husna sun ɗan jima suna fira fitowar Alhaji Wadata yasaka ta katse wayar gurin ta ya ƙaraso yana washe baki ya ce "hurt girl ya zamuyi?"

    Murtuƙe fuska ta yi ta ce "name fa?"

    "Number ki zaki bani sai ki bani gurin da zamu haɗu." Bai ƙarasa rufe baki ba yaji saukar mari a fuskar sa ɗagowa ya yi da mamaki yana kallon sai huci takeyi cikin masifa ta ce "ba zaman da nakeyi anan ba tsohon banza."

    "Ni kika mara sai kinyi dana sanin marina da kikayi sai naga ubanda ya tsaya maki."

      "Ni na tsaya mata ko kana da abinda zakayi ne." Sukaji muryar Sir Ammat yana faɗin haka  waigowa Alhaji Wadata ya yi  yace "ranka ya daɗe marina fa ta yi."

JUMANATUWhere stories live. Discover now