🧕🏻 JUMANATU🧕🏻
Story & writing by
RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comFree page
5️⃣
Murmushi ta yi dan haka Abba keyi mata idan tana fushi sai ya yi ta lalaɓa ta har ta sauko ya daɗe a ɗakin su sannan ya yi masu sallama ya fita washe gari ta kama assabar sai shirye_shiryen ɗaukar azumi ake da ake sa ran gobe za'a tashi da shi duk wanda ka gani yana cikin farin ciki zuwan azumin watan Ramadan babba da yaro sai murna akeyi da misalin ƙarfe biyu na rana suka tafi kasuwa ita da ya Abbakar da Batula ba su suka dawo ba sai gurin la'asar duk sun jigata ɗakin su Jumanatu ake shiga da kayan take Innah Rabi da Umma suka ji wani irin baƙin ciki ya taso masu sun saba ganin wannan duk watan azumi amma ganin wannan karon kayan sunfi yawa ana cikin haka saiga Siyama ta zo gidan ta kawowa iyayen ta kayan azumi duk da ko rabin waɗan da Jumanatu ta siyo basuyi ba haka Innah Rabi ta yi ta sakin habaici tana cewa "ƴar albarka irin arziƙi mudai ta hanyar halal muke ci ba mu tura ƴa kamfanin masu kuɗi suna iskanci da su suna samo mana kuɗi ba."
Umma ta amsa da "wallahi ko yaya mun aurar da su suna gidajen su hankalin mu kwance saidai su kawo mana wasu ko saidai su tura ƴar su karuwanci."
Haƙiƙa mai haƙuri bai iya fushi ba fuskar Ummi ta yi ja kasancewar ta fara ce ita miƙewa ta yi daga zaunen da take ta isa gaban su ta ce "idan fitsari kayan rago ne to kazama tayi mugani miye ban sani akan naku yaran shiru kawai nayi."
Nan dai Ummi ta yi masu wankin babban bargo sai da ta yi ma su tas sannan ta juya ta ɗauki kayan ta ta shige ɗaki duk shiru sukayi dan basu zaci Ummi zata yi irin wannan dogon magana ba bare akai ga faɗa mama dake ge ta ce "idan dai zagin ƴaƴan mutane ne aikin ku to kuci gaba duk wanda ya ƙi ji bayaƙi gani ba."
Caaaa suka mata suna kiranta munafuka kwaɗayayya shigowar ya Anas yana faɗan hayaniyar da akayi ya saka su yin shiru dan kowa na tsoron ya masa hauka har ya gama faɗan sa ya fita Siyama bata bar gidan ba saida ta kasa kayan da ta kawo tabama ko wane ɗaki Innah Rabi nata faɗa akan ta raba kaya sai dare mijin ta yazo ya ɗauke ta ganin watan Ramadan da akayi sanarwa yasaka dukkanin al'ummar musulmi farin ciki haka aka kwanta da niyyar tashi da azumi da misalin uku na dare ahalin gidan suka tashi daga manya har yara hakan ya saka Jumanatu ta shi bata fita ba gas ɗin ta kawai ta janyo ta kunna dama tun dare ta shigo da ruwanta ruwan zafi kawai ta dafa ta ɗibi nata sannan ta haɗawa Ummi nata da Batula falo ta fito sai tagan su zaune duk sun ta shi ajiyewa ta yi ta koma ɗaki sai gata ta dawo da sauran kaya wani kofi ta ɗauka ta zuba tea ɗin sannan ta gutsiri biredi tana cewa "Ummi bara na kawa ya Abbakar kayan sahur."
Fitowa ta yi duk da dare ne amma bai hana ƴan gidan haniya ba dama haka suke shiyasa duk gidajen da ke kusa da su basu makarar ta shi, wucewa ta yi bata yiwa kowa magana ba da kallo suka bita da kallo ɗakin samarin ta bubuga da yake suna da ƙofa ta ciki kuma sunada ta waje ya Anas ne ya buɗe "ah Hajaju har lokaci ya yi kenan bara na tado maki Abubakar ɗin dan nasan nashi ne."
Murmushi kawai ta yi dan duk gidan babu wanda baisan shaƙuwar da ke tsakanin ta da Abubakar ba takan hanawa ƙannan ta bawa Abubakar duk yan da Innah Rabi ta yi ta rabasu ta kasa ta yi masa faɗa amma ya yi kunnen uwar shegu da ita hakan ya sa ta zuba masu idanu fitowa ya yi yana miƙa da hamma "Hajiyar gidan mu kece haka?"
