🧕🏻JUMANATU 🧕🏼
Story & writing by
RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comFree page
7️⃣
"Cab nikam Allah ya tsareni haka kawai ya tayimin shiru idan ina magana."
Tuƙinsa ya ci gaba dayi ba tare da ya sake kallon ta ba "sir Ammat wai kaji azumin jiya harda kuka nayi." Shiru ya mata bai bata amsa ba taɓe_taɓe ta fara idan ta janyo wannan ta janyo wance "wai kin bani ajiya ne ko kuma na miki sata ne?"
"Eh wallahi sir Ammat ranar nan da muka fita na manta cingwam ɗina a motar ka. Kudai ka gani ka cinye?"
Be kulata ba ya faka motar sa yana ƙoƙarin buɗe wa ta ce "sir Ammat magana da nake maka ka yiman baza kamar ma bakaji abinda nakecewa ba."
"Ooo miss Jumanatu ki min shiru koda na minti talatin ne haba kinbi kin isheni da surutu." "Sir Ammat kodai ka fara jin yunwa ne?"
Tsuki ya ja sannan ya buɗe motar ya fita da sauri ta bi bayan sa ya awa biyu suka ɗauka itakam har ta fara jin bacci ga sanyin AC ga gajiya da zama, suna hanyar dawowa ta yi laƙwas baka jin komai sai ƙira'ar Shaikh Muhammad a'arafi ke tashi kwanciya tayi a kan kujerar koda suka isa office har ta yi bacci tsayawa ya yi yana kallon ta saida ya ƙare mata kallo sannan cikin ɗaga murya ya ce "Miss Jumanatu."
Firgigit ta buɗe idanu ganin sun kawo ya saka ta turo baki "haba Sir Ammat bafa haka ake tayar da mutum daga bacci ba."
Bai tsaya bata amsa ba ya buɗe motar ya fita itama fitowa ta yi tana mita "duk kaina ya yi ciwo kaida Allah."
Ƙarfe biyar suka tashi aiki dan haka koda taje gida a gajiye take wanka kawai ta yi ta lanƙwashe tanaji alamar saƙo ya shigo a wayar ta amma ta kasa dubawa saida aka sha ruwa sannan ta duba taka alart na kuɗi kusan dubu ɗari sunan sir Ammat da ta gani shi yasaka ta mamaki kiran sa ta yi amma ba'a ɗaga ba kira ta yi tayi saida ya ɗaga yana ɗaga wa ya ce "miss Jumanatu what is wrong with you."
"Sir Ammat alart na gani na kuɗi yanzu da sunan ka na ɗauka ko kuskure kayi."
"No kuɗin cingwam ɗin kone na biya." Zaro idanu tayi ta ce"sir Ammat kuɗin fa da yawa har fa dubu ɗari na gani ko dubu ɗaya kayi niyya ne baka sani ba ka ƙara."
"Nasani madam dan Allah sai anjima." Daga haka ya kashe wayar sa da kallo ta bi wayar "can ta matse maka."
"Keda waye?" Cewar Ummi dake gefen ta "ogan mu ne ya turo mani kuɗi shine nake tambayar sa yake ceman wai kyauta ya mani."
"Kyauta akan me zai baki kuɗi?"
"Dama an gaya mani yanada kyauta idan har ka riƙe amana kuma ka riƙe aikin ka da gaskiya."
"To Allah ya biya shi." "Amin." Kwance tashi ba wuya sai gashi har an shiga goman ƙarshe anata shirye_shiryen sallah ba yanda Jumanatu batayi ba da ta ɗauki hutu amma ya hana ana saura kwana biyar sallah tana zaune saiga wani mai kama da Sir Ammat ya shigo gaida shi ya yi ya amsa "wa za'a ce masa?"
"Kice dashi Amjad ne."
Waya ta ɗauka ta kira sa "sir kayi baƙo sunan sa Amjad." Ajiye wayar ta yi ta ce "ka shiga."
"Thanks dear." Daga haka ya shiga ta bishi da kallo komai nasu ɗaya har haɗe fuskar taɓe baki ta yi taci gaba da abinda takeyi agogo ta kalla taga biyar saura miƙewa ta yi ta shiga office ɗin suna zaune sai fira sukeyi suna dariya gurin sa ta nufa ta miƙa masa takardar hannun ta karɓa ya yi ya karan ta ya ce "na miyene wannan?"
"Gaskiya nikam sir Ammat kana kaini bango kafa karanta kuma kaga abinda ke ciki kuma sai na sake ma bayani ni gaskiya kana sakani yawan magana."
"Miss Jumanatu....."
"Sir Ammat takardar hutuna ne daga gobe zan fara." Wani takarda ta miƙa masa "ga sticker ɗina nan ka duba idan akwai abinda kake buƙata ayi maka sai kayi magana." Wata ta ciro ta miƙama Amjad ta ce "maikama da yallaɓai gashi kaima idan kana buƙata kayi magana."
Karɓa ya yi yana murmushi dan dai shikam ta burge shi "kai nake jira sir Ammat ka sa hannu na kama gaba na dan tun ɗazu biyu_biyu nake ganin ka."
Tsuki ya yi ya wurga mata takardar ta "kai_kai sir Ammat wannan wulaƙanci fa?"
Takardar ta mayar masa ta nufi ƙafa "miss Jumanatu idan kika tafi to karki dawo, sai ki zaɓa aiki ko tafiya hutu."
"Ko ɗaya bazan bari ba kuma duk wanda ya yi gan gancin hawa kujerata to ya shiga ɗari uku."
Daga haka ta fita dariya Amjad ya yi ya ce "bro ashe haka P.A ɗinka take tama fika masifa."
Makullin motarsa ya ɗauka ya ce "idan ka tashi mu je ko na rufe ka a nan."
Cikin kwanakin da suka rage sallah ba ƙaramin aiki sukayi ba dan ta sami masu siya da yawa, ranar sallah ilahirin jama'a suna murnar zuwan wannan rana a cikin motar da Anas ya ke sana'ar tasi suka ɗuru saura kuma suka shiga keken ya Abubakar suka ta fi masallacin idi bayan an taso ne suka je kallon hawan sarki yara kam sai murna sukeyi suna gefe inda mutane ke tsayawa sai ga sarki da tawagar sa abin mamaki ɗaga idon da Jumanatu zata yi sukayi ido huɗu da Ammat dake kan doki ya sha kayan sarauta murmushi ya sakar mata ganin irin kyaun da ya yi da ya yi murmushi ya saka ta hangame baki ihun da su Munsura sukeyi ne shi ya dawo da ita duniyar da ta lula "ke kinga murmushi da haɗaɗen gayen can ya yi mani kilama sona yakeyi." Cewar Mansura da ke ta tsalle tana gayama su Ikilima kallon ta Jumanatu ta yi ta taɓe baki bayan sarki ya wuce su Jumanatu suka kamo hanyar gida suna zuwa gida Jumanatu ta kaɗa kan ƙannan ta suka tafi gidan Aunty Sadiya.
**************
Zaune suke a babban falon fulani suna cin abinci mai martaba na tsakiyar su dan duk sallah haka yakeyi duk ƴaƴan sa da jikokin sa da ƴan uwan sai sun taru bayan angama cin abinci mai martaba ya yi gyaran murya hakan ya sa dukkanin shiru suka maida hankali su gareshi addu'a ya farayi sannan ya fara cewa " a yau zan yi marabus kuma za'a naɗa ɗana Abdallah da misalin biyu na rana."
Wata irin zabura Dady su Ammat ya yi ya buɗe baki ya yi magana mai martaba ya ɗaga masa hannu "ba shawarar ka na nema ba wannan hukunci na riga da na yanke shi kuma babu wanda ya isa ya canza shi sai ka shirya ƙarfe biyu ne za'ayi naɗin sarauta."
A fusace uwar gidan sarki gimbiya Zulfa ta fara magana "haba ya zakayi haka ko ka manta yana da yaye zaka ɗauki sarauta ka bashi."
"Na riga da na yanke shawara ta babu kuma wanda ya isa ya canza da kike maganar yayen sa duk cikin su akwai mai ilimin addini ne ko kin ɗauka duk bansan me sukeyi ba?"
Shiru gurin ya yi duk da da Fulani mahaifiyar Abdallah bata ji daɗin hakan ba bare kuma uban gayya akan haka ne ya ƙauracewa gidan sarauta amma duk da haka bai tsira ba.
Kuyi maneji Please banajin daɗi ne.
Wannan littafin na kuɗi ne idan kina buƙata ki nemi wannan number 09035637947 ko Kuma 09031974044.
Sai najiku.
It's Rashma.
