Part 31

292 5 0
                                    

PRINCE AIRAN AND MAIMOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love,Betrayal,Sacrifice,Sorrow)

✍️31✍️

Story
           And
Written by

KHADEEJAHT HYDAR
🌸YOUNG NOVELIST🌸

✍️From the experience writer ✍️
🌺IHSAN🌺
🌺UQUBAR UWAR MIJIN🌺
🌺WATARANA SAI LABARI🌺

AND NOW
🌺Prince Airan and Maimoon🌺

Dedicated to the cared one

✨Mustapher🌹 Basheer 🌹Tal✨

                    🌸
        🌸  NASIHA 🌸
        A matsayinka na cikekken musulmi kuma mu'umina kazamo me tsarkakken zuciya da nufin mutane da alkhairi koda kuwa su da sharri suke binka saikaga Allah yasaka maka yamaidamusu aniyarsu

Wattpad user
YoungNovelist4

Wattpad link
https://my.w.tt/lPwoUkZrs8

            🌸
Da isarta gida tashiga riƙe da jakarta,tundaga main gate aka fara mata ƙirari tare da ƙarbar jakarta sukayi part ɗin Amminta dashi.

Zaune suke suna cin abincin rana(Lunch) sai kawai sukaji wani bafade yana sanar musu da isowar Maimoon,da saurinta tashiga tana sallama haɗe da kiran Ammina i missed you.

Cikeda farinciki da ƙauna suka tarbeta saida tabi kowa ta masa oyoyo saikuma ta haɗa fuska ta kalli Aslam wanda shima jiya ya dawo tace"...Yaya kadaina sona ko Oyoyo babu"..

Murmushi yayi yace"...ai yanxu kin girma u are 23 fa,u are now a big girl next year sai aure,ɓata fuska tayi tace".....Mama kingansako wlh kicemasa banaso".

Ƙyalesa kinji jekiyi wanka zan aiko da abincinki  kici  ki kwanta anjuma zamu haɗu a fada,to ta amsa sannan tafara tafiya hartakai ƙofa saikuma tajiyo takalli Fahad tace"....Bro anjuma zamuyi magana if u are free".

Murmushi yayi yace"....to anti Moon saikin zo jeki huta kinji am free for u,thanks Bro daga haka tawuce ɗakinta.

Tana zuwa tashiga bathroom ta watsa ruwa tayi salla taci abinci tabi lafiyar gado sai bacci,se la'asar ta tashi a gurguje ta watsa ruwa tayi salla saboda ganin 4:10pm.

Alkyebba ta daura aƙan doguwar rigarta tayi hanyar fada dogurai da ƙuyangi na kwasar gaisuwa ta amsawa,hartazo wucewa taga kishiyar Mamanta wato mumynsu Kamal da  wata mata kamar ta wuce saikuma taga rashin dacewar hakan sai kawai ta ƙarasa ta gaishesu taci gaba da tafiyarsu Mummyn tarakata da muguwar harara.

Gimbiya Habeeba tace"....Hasiya kice surikartawa kyekkyawace fiyeda yadda kike faɗa ah dole muzauna cikin shiri nan da kwana kadan muzo zancen aure,murmushi Gimbiƴa Habeeba tayi tace".....lallekam hakan zaifima nide burina nazama Mamar sarki me jiran gado".

Tace"....nima haka wlh kinga muyi sallama naje naga me Martaba yayi ƙiran meeting a fada sai munyi wayar duk yadda akayi kya ƙirani a waya ki sanar dani cewar Gimbiya Hasiya,to ba matsala sai kinjini daga haka suka rabu da ƙudirin banza a ransu.

Fadar tacika duk iyalan sarki kowa da ƴaƴanta a gefe ana jiran jin miye musabbabin taron,waziri da advisers na sarki ne kawai agun babu fadawa ko kuƴangi ɗaya saboda abune daya shafi cikin gida.

Bayan Waziri ya buɗe taro da addu'a akayi shiru ana jiran cewar sarki, saida yakalli kowa kafin yafara jawabi kamar haka.

Allah nagodemaka dakasake haɗamu a wani karon cikin ƙoshin lafiya da aminci,kamar yadda mukayi alƙawari yau zamu zauna tunda Aslam ya dawo koda Maimoon bata dawoba zanbarmata saƙona saboda zanyi tafiya zuwa dubai don duba lafiyata to Allah da ikonsa Maimoon ma tadawo kuma inamata sannu da zuwa da kuma jin daɗin ganinta bayan shekara da wasu watanni Alhamdulillah.

Abunda yasa na tara ku anan shine alƙawarin danayi daku wato samari da ƴenmatan gidannan shine baƴan Maimoon da      Safiyya sungama makaranta zanbaku zaɓi ku fitar da abokan auran ku dukda kai Aslam da Kamal na daɗe da faɗa muku amma naga bakubani amsaba to wannan ce dama ta ƙarshe dazan baku inba hakaba zakuga ɓacin raina,nabaku nan da wata ɗaya kows yazomin ds amsarsa.

Bayan haka kafin kuma kafin na sallami kowa inason naja hankalinku akan banson naji kona ga wani saɓani ko faɗa a tsakaninku,ku zauna lafiya da juna har zuwa lokacin da kowa zai kama gabansa,dafatan kowa yaji zancena?,amsawa sukayi da toh kafin aka rufe taro da addu'a kowa yakama gabansa ya rage daga wazirin sarki sai Maimoon da mai martaba..

Rarrafawa tayi taje gun Abbanta tanamasa sannu da hutawa daya jiki,da murmushi yace"....Mamana sai kuma akamana zuwan bazata to Alhamdulillah tunda kunzo lafiya Allah yamuku albarƙa,Amin suka amsa daga haka tawuce part ɗin su Aslam"..

Taci sa'a kuwa Fahad ne kawai a part ɗin ya miƙe kan kujera yana kallo,amsa sallamarta yayi yace"....to iyayen naci zauna murmushi kawai tayi donta ƙagu taji bayani akan sweet ɗin".

Yace"...gaskiya sis nayi matuƙar girgiza da sakamako yanuna cewa sweet ɗinnan yana ɗauke da guba me ƙarfin gaske da alama anyi niyyar salwantar da Auta ne amma ya kare,but don Mummy na kishi da Mama haryakai ta haɗa hannu da wata akan acutar damu harda son poisoning Auta"...

Tace"..dazu naganta da wata mata kuma ina kyautata zaton matarce amma na ɗauki hotonta zannunawa Auta ko'itace sannan let it be secret between us saboda karmu tadawa kowa hankali kaga a sirrince zamunabin diddiginsu amma sai munzama masu ankarewa dakowane movement nacikin gidannan,eh haka zamuyi cewar Fahad to make it easy zansiyomana cctv camera guda biyu ni ɗaya ke ɗaya amma ki tabbatar kin ajiyeshi inda bame gani sannan computer ɗinki yaxamo cikin tsaro da kula saboda da alama shirunsu ba akanmu kawai ya tsaya ba duba da yanda kullum sai mum tafita koda rana koda dare".

Zare ido Maimoon tayi tace"....this is serious but Allah natare damu kuma zai karemu,Fahad yace"...hakane bari naje na siyo,tashi itama tayi tace"...bari naje na nunawa Auta hoton daga haka tamasa sallama ta fita.

A ɓangarensu Airan kuwa malamin fada na zuwa yayi tofi cikin ruwa yabata tasha kawai saita fara amai sai suma yabiyo baya,ta daɗe a sume kowa ƙirjinsa yafara jump banda Mummy da take fatan tawuce daga hakama.

Sunɗau a ƙalla awa ɗaya tukun tafarka tana shirin guduwa su Airanne suka riƙeta Usman sarkin kuka kuwa haryafara ganin Ammi cikin ciwo kamar mahaukaciya kuma duk Mummƴnsace sila.

Malaminne yamusu bayanin cewa kurciya akamata to sai Allah yasa da ƙarfin addu'a sihirin da 'akamata da kuma abunda aka zubamata cikin abinci baiyi tasirib.

Sororo kowa ke kallonsa saboda jin zancen, mafi ƙaɗuwama wai a abinci aka zubamata,a zuciye Airan ke fitar da numfashi a ransa yana ƙissima me zaiwa ƙuyangin dake kula da abincin Ammin.

Addu'a yayi mata da basu wani magani da adduo'i anamata,to alhamdulillah tadaina fizge-fizgen tasamu bacci.

Dukansu in akacire mai Martaba da Mummy babu wanda beyi kukaba ganin yadda ta koma ta lalace,Airanne yafita zuwa ɓangaren bayi.

To nima ana na ajiye alƙalamina fans sai kunjini gobe,namuku fatan alkhairi.

✨✨✨✨✨✨✨✨
YoungNovelist.
      🌟🌟
Alƙalamin Auta
           ✨✨
ROYALTY
.    ✨✨✨✨

PRINCE AIRAN AND MAIMOONWhere stories live. Discover now