Part 40

331 19 0
                                    

🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
PRINCE AIRAN AND MAIOON
🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
(Love,Betrayal,Sacrifice,and sorrow)

✍️40✍️
Story
    And
Written by
Khadeejaht Hydar
(Young Novelist)

From the experience writer of.
🌺IHSAN🌺
🌺UQUBAR UWAR MIJINA🌺
🌺WATARANA SAI LABARI🌺
🌺KANKI KIKA CUTA🌺
And now with the most intresting one.

*Prince Airan and Maimoon.*

Dedicated to
Hafsat Taheer chocolate patner.

Happy Birtday Dear.
ABDULLAHI JIDDA.
May Allah bless ur new age,I LOvE U❤️

Jama'a da fans karkumanta da karanta suratul Kahf.

Jumma'at Mufeedaht to u all.
     💫
Mahaifin Maimmon ne Sarki Alhassan na II zaune da iyalinsa gaba ɗaya harda Mummynsu Kamal suna tattauna matsalar ɓatar su Aslam,Mama tace"...ni yanzu damuwatama yadda babu wanda yasan inda Usman ƴaje ko kuma aka kaisa,saboda na tabbata akwai alamun tambaya a action ɗinsa,Abba yace"...muci gaba da addu'a insha Allah komai zaizo da sauƙi,yauwa Fahad kaje ka ɗakko  Auta gidan Abbanku gobe zasu koma makaranta ,kuma kacema Farouqh da Hydar su kula sosai,to Abba daga haka yakama hanyar fita"..

Waya take ƙasa-ƙasa tace"...yanzu za'azo ɗaukarta ku tabbatar kun kashesu gaba ɗaya,to Hajiya angama daga haka ta kashe wayar tana dariyar mugunta taƙira gimbiya Habiba  tace"..nabada aiki kawai kamar angama,tace"...sai isa nakeson aiki dake Hasiya akwai kwanya mai kyau,dariyar mugunta sukayi  gaba ɗaya".

Bayan ya ɗakkota har sunfito Abba yace"...Farouq kaida Hydar  kuje ku ƙarbomin saƙo gun abbanku amma inkunga yamma tayi ku kwana acan,to Abba saimun dawo.

Haryashiga motarsa ya tada su Hydar suka tsayar dashi  suka shiga tareda shaidamasa aiken da Abbannasu ya musu,sunyi nisa sunbar masarautar sosai sukaga wata mota tasha gabansu.

Cikin  sauri Fahad dake tuƙi yafara koƙarin juya kan motar don kaucemusu amma kafin ya ankara sunzagayesu da bindigogi a hannunsa,sunada yawa gasu ƙarfafa baƙaƙe fuskarsu ba annuri suka umarcesu dasu fito.

Hydar wanda yafi kowa tsoro shiya fara fitowa jiki na rawa ganin hakan yasa Farouqh da Fahad fitowa Autarsu Maimoon kuwa tana cikin mota tana kuka idonta a rufe.

Fizgota wani daga cikinsu yayi yace"...all of you inside komawa sukayi cikin motar jikinsu na rawa Hydar ne yaƙi shiga ciki ganin basu basu Auta ba"..

Mari akasakar masa nan suka taru suka fara masa duka ba tausayi yana ta faman karekansa amma saida suka masa dukan fitar rai tukun suka sakasa da Auta cikin motar da suka kulle su Faruq aciki,Fahad ne yayi saurin taresa tare da daura kansa akan cinyarsa duk jikinsa ya ɓaci da jini,Faruq kuma auta ya riƙe wacce yaga alamun tana lalubensu,da sauri yace"...Deeja open your eyes we are here,da sauri tace"...am not seeing you bana ganinku ya Faruq i cant see,cikin ɗimuwa yace"...mesuka miki mesukasamiki a idon tana kuka tace"....sun buɗe idona suka fesamin sheltos,cikin gigita Fahad yake kallonta at the same time yana ƙoƙarin riƙe Hydar da jini ke fita tabaki da hancinsa yana ƙiran sunan Usman da Mummy,cikin ƙaduwa Fahad yake neman ruwa yabasa kafin yacema Faruq ya miƙomasa kawai sukaji kamar anyi sama dasu,bakajin komai sai ƙarar glasses dake fashewa,daganan kuma basusan inda kansu yakeba.

Dayake gun mutane basa wucewa sai isa suka aiwatar da aikinsu batare da matsalaba har suka bar gun.

Tafe suke cikin motasu uƙu ɗayar tace"...Hasna wai meyasa zakice mubi hanyarnan bayan kinsan mutane basabin hanyarnan ,cikin shews tace"...kawai hanyar short cut ce tafi sauƙi daga haka taci gaba da tuƙinta,abinda suka ganine yakusan sasu a ɗimuwa,yarinyace yashe a gefen gun ga wata ƙaramar mota tashige ƙarƙashin babban trailer,da sauri suka fito Hasna tace"...innalillahi hatsari akayi ga yarinya a kwance ko iyayentane a cikin motar,da sauri suka ƙarasa gun motar tasu tayi raga-raga bakaganin komai sai jini a jikin glasses ɗin".

Da gudu Hasna taje bakin titi ta gayyato mutane aka ƙira ƴaɓ agaji suka ciro motarsu Fahad,duk wanda yakegun saida yayi kuka saboda mutum ɗaya acikinsu yayi mummunar rauni.

Ambulance ce ta ɗaukesu sai babban asibitin dake cikin gari,Hasna sam batagane suwayeba donhaka akafara bincikar wayoyinsu,dakyar aka samu number mai martaba Mahaifinsu Airan aka sanar dashi abindake faruwa.

Cikin tashin hankali ya ƙira ɗan'uwansa sukayo asibiti,abinda sukagani shiyafi ɗaga musu hankali a duniya,ƴaƴansune kwance a emergency ko wanne da taimakon  oxygen yake numfashi amma ɗaya acikinsu yafisu jigata ,shiga sukayi don sunkasa komai.

Gadon da Hydar yake sukafara zuwa yana kwance duk yafisu jigata duk ƴa karkarye badon numfashinsaba da bazakace yana raye ba,hannu mai martaba ya ɗaga ya riƙe na Hydar yana zubda hawaye saboda sosai ganinsa ya taɓa masa hankali,idonsa ya buɗe yana kallon mahaifinnasa hawaye na zuba a idanunsa amma ba halin magana.

Bakinshi ke motsi donhaka Abba yaciremasa abun abakinsa yakai kunnensa donjin mezaice,ba abinda yake faɗa sai Usman da Mummy daga haka kuma yafara salati batare da yasake hannun Abba ba,can kuma yayi shiru idanuwansa na kallon sama.

Wasu hawaye masu zafi suka saƙƙo daga fusƙar Abba a lokacin daya fahimci Hydar y amsa ƙiran mahalicci,yanason Hydar sosai saboda shida Usman sam basubiyo halin mahaifiyarsuba gashi da shiga rai ga biyayya,kasa daina hawaye mai martaba yayi saida Abbansu Maimoon ya riƙesa ya zaunar donyaga alamun kamar faɗuwa yake shirin yi.

Allahu aƙbar kulli nafsin za'ikatul maut,yau wani jigo na labarinnan ya fita wato Hydar,Allah kajikan duk mamatanmu ameen.

Fuskarsa Abbansu Maimoon yashafe tare da lulluɓesa yana share hawayen fuskarsa,gida suka nufa da gawarsa don kaisa gidansa na gaskiya.

Da shigarsu yayi dai-dai da dawowar Jabeer,Ishaq,Khaleed daga gun Sadiq,da Mummy wacce yanzu itama take shigowa tadawo daga gun boka itada Mummynsu kamal wacce ita tayi tafiyarta gida bayan sungama bada aikin akashe su Fahad sukaje gun boka don plan ɗinsu na gaba.

Abunda sukagani a tsakar gidanne yasasu fitowa batare da kashe motar ba,Khaleed ne ya ƙaraso da saurinsa yaname kallon fuskar iyayennasu,cikin ɗimuwa yace"...Abba waye akwance acikin makara Abba wamuka rasa yau,baijira cewarsuba ya buɗe likkafanin da'ake rufe Hydar dashi".

Da ƙarfi yace"...Hydarrrrr wanda hakan yasa Mummy dake shirin shiga part dinta dawowa da sauri hartana tuntuɓe ta nufesu donjin an ambaci ɗanta amma da tayi niyyar shigeqa dukda taga gawa a kwance ita duk a tunaninta Fahad ne ko Farouq,kuka duka sukeyi ganin Hydar akwance cikin makara wai ya mutu,cikin kuka Jabeer yace"...dazu muka rabu dashi yana cewa insiyomasa turare gashima acikin mota,Hydar dan Alla katashi karkamana haka munrasa Aslam ba Airan ba Maimoon gashi kaima zaka barmu dan Allah ka tashi,furucin Jabeer yasa kowa kuka harda Ammie da ta fito yanzu bayan wata baiwa tafaɗamata".

Khaleed ne yace"..Abba meyasamesa?,dakyar Abba yamusu bayani yana goge hawayensa,Ishaq ne yace"...Allah sarki Hydar dashi muke neman su Airan,dan Allah katashi zamusamu su Airan insha Allah,kaga yanzu mu shida muka rage su Fahad ma zasuji sauƙi katashi mucigaba da rayuwarmu muna sonka sosai".

Mummy wacce sai yanxu hanƙalinta ya dawo jikinta ta rusa ihu tana tashiga uku,Hydar suwaye suka kasheminkai wayyo nashiga uku na lalace,wayyo yarona mai biyayya dan Allah katashi wlh nadaina nadaina ,haka tadinga sumbatu ,dakyar aka kaita ciki,Ammi ma kuka take don sosai takeson Hydar bata taɓa banbatasa da ƴaranta ba.

Cikeda kewar Hydar yaron kirki aka kaisa gidansa na gaskiya bayan dubun jama'a sun halarci jana'izar Hydar tare da masa fatan saduwa da ubangiji saboda shikam kowa yamasa shaida me kyau..

A lokacin da labarin mutuwar ta riski su Maimoon a bakin Sadiq ba ƙaranar ƙaɗuwa sukayiba Usman kuwa zaucewa yakusanyi saboda sosai mutuwar ta shigesa kuka yakeyi kamar ransa zai fita,don sun shaƙu da Hydar sosai,dashi suke shawara akan lamarin mummynsu gashi yatafi yabarsu.

Maimoon da Airan har Aslam ma sunyi kuka amma dole suka daina suka shiga rarrashinsa saboda ciki ɗaya ba wasa bane,duk sunshiga    damuwa amma sun godewa Allah da jarabawar dayayi musu.

Amin uzuri ba typing dayawa abubuwanne sunyi yawa.

Taku a kullum.
🔥🔥🔥
Young Novelist.
    🌼🌼🌼
Royalty.
  💃🏼💃🏼💃🏼
AUTARSU.

PRINCE AIRAN AND MAIMOONUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum