Cikin jarumta kamar koyaushe Abdulrahim ya tashi da kansa ya wuce gaba garba na biye dashi a baya yaje bakin kofar dakin ya tsaya yana jiran azo a bude masa kofa ya shiga, wannan abu ba karamin bawa kowa mamaki yayiba domin ko manya gardawa na tsoron dakin wasuma idan za’a sakasu sai da kokawa ake kamosu a saka amma shi gashinan ya wuce kamar babu abinda ya faru hankalinsa kwance, bayan an sakashi aka kawo wata sarka aka daure masa hannu da kafa wadda itace suke kira da marin sannan aka maida kofa aka rufe aka barshi shi kadai cikin wannan dakin cikin tashin hankali na duhu, cinnaku da sauran mugayen kwarin dake ciki, kawai sai Abdulrahim ya fara wani tunani; tunanin kabari! shima fa haka yake cike da duhu da mugayen abubuwa ga wanda baiyi sa’a ba dan haka maimakon yayi kuka kamar yadda sauran yara keyi idan an sakasu a dakin sai ya kama istigfari tare da addu’a da annabi ya koyar damu ta neman tsari da azabar kabari.Tunda aka saka Abdulrahim a dakin mari Abdulrahman ke zaune a bakin kofar wajen yana kuka tare da rokonsa Allah da annabi akan ya fadi inda kudin suke ko malam zaiji tausayinsa ya sakeshi amma Abdulrahim ya tubure yace shi babu wasu kudi a hannunsa “na gaya muku na kashe idan zaku sakeni ku sakeni dan bani da inda zan samesu” ko kuma idan yaji anyi kiran sallah ko an shiga karatu sai yace “abdul ka tashi kaje ka yi sallah/karatu dan zamanka babu abinda zai canja”.
Malam yasa an caje kayansu tare da jikinsu gaba daya amma ko naira biyar ba’a samuba babu kuma wani abu da aka gani wanda zai nuna ya siya da kudin. A takaice dai sai da Abdulrahim ya kwana uku a cikin wannan dakin kullum sau daya ake bashi abinci ruwa kuma sau biyu sai kuma da safe a kaishi bandaki duk abinda yakeji bayan na safennan sai dai ya rike abinsa amma duk wannan azabar yaki ya fadi abinda suke so din, ganin haka dole malam ya saka aka fito dashi domin a yanzu ma malam yasan ya sha wahala ba kadanba idan aka cigaba da haka zai iya cutuwa, yadda Abdulrahim ya kwana uku a dakin mari haka abdulrahman ya kwana uku a bakin kofa yana kuka tae da rokonsa, idan yayi kukan ya gaji yayi bacci idan ya farka ya cigaba da kukan yana rokonsa ya fadi inda kudin yake amma tamkar wanda da dutse aka halicci zuciyarsa ba tsoka da jiniba ko gezau sai dai wani lokacin idan kukan abdulahman din ya isheshi sai yace “abdul kayi hakuri ka tashi daganan dan bazan iya fadaba ka daina azabtar da kanka zamanka anan yafimin zamana anan wahala” jin irin wannan maganar ne ke sakawa yaki tashi din saboda yanason yin amfanin da son da Abdulrahim din yake masa yaji tausayinsa ya fadi, wani lokacin kuma da masifa zaice masa “dallah malam ka tashi anan ka barni naji da abinda nakeji anan basaika karamin da kukankaba”.
Ranar da kwana uku ya cika da yamma malam yace aje a fito dashi sannan a kirawo wannan matar, bayan sun zauna malam ya kalli matar nan me kudi yace “to baiwa Allah kinga dai yadda mukayi da Abdulrahim a yanzu kam na yadda ya kashe wannan kudin saboda wannan wahalar da ya sha tabbas da kudin yana hannunsa da tuni ya fito dashi, dan haka ina me baki hakui kiyi hakuri” bata bari ya sauke numfashi ba ta fara bala’i “wallahi bazai yiyuba sai ya biyani kudina ni yanzu kudin ba nawa bane da yaya akeso na biya?” malam yace “sai ki dauki kudinsu da kika dauka musu wancan karon ki biya wannan” tace “ni na dauka? Na fada ni ban daukar musu kudiba” kallonta malam yayi na wasu seconds sannan yace “kinaso ayi tonon asirine ko kuma kinaso abar kaza cikin gashinta? Nasan ke kika dauka kawai na basu hakurine a lokacin idan kuma kinaso yanzu na tona asirinki yadda kika dau kudin ba tare da bankin ya fasheba da abinda kikai dashi gaba daya na sani, ke kika jawowa kanki tun farko da baki taba musu kudiba da basu taba miki nakiba, dama idan tsoho baiji kunyar hawa jakiba bahausge yace jaki ba zaiji kunyar kayar dashiba, kai kuma” ya juya kan Abdulrahim “idan ka kuma dauka mata wani abin wallahi kaji na rantse wajen yan sanda zan kaika suyi maka duk yadda suka ga dama na kashe wannan maganar duk wanda ya kuma tayar da ita zai gamu da fushina” kunkuni matar ta fara da basajin abinda take cewa malam yace “me kike cewane? Idan ma kina tsammanin zakiyi musu wani abu to wallahi kema kinji wallahi idan kikasa aka kuma taba min almajirai sai na saka an daure ko wa kikasa ya tabasu, ina da mutane a sama idan baki saniba yan siyasar nan duk mun sansu idan na daure yaro sai dai uwarsa ta haifi wani kinji na gaya miki ku tashi ku bani waje” yana gama fadar haka ya jawo buta ya kuskure bakinsa sannan ya jawo alquraninsa ya fara karatu.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...