Chapter 42

60 8 4
                                    

Photo of Khadijatul kubra at the top👆

Khadija karatu takeyi sosai babu kama hannun yaro dan tasan yayyenta sune gatanta karatu shine gatanta, ta maida hankali a islamiyya sosai haka ma bokon itama ba'a barta a bayaba dan yanzu Khadija idan kanayin turanci tana iya fahimtar abinda kace indai ba manyan grammars kake using ba, mayarwane dai ba zata iyaba, yanzu watannin mal musa shida kenan da komawa gida kememe yaki dawowa ya makale a can ita kuwa jaru bayan dambarwar da akasha da ita sai kawai ta hada kayanta tasa 'yayanta suka hada mata kudi tabi 'yarta lagos a cewarta badai dan su Abdulrahman sunyi kudine ake neman ci mata mutunciba to itama zataje tayo kudin sannan ta dawo ta rama, amma maganar gaskiya ba wannan ne babban abinda ya kaita lagos ba neman 'yarta ta tafiyi dan tunda ta tafi babu aike ba waya shekaru uku kenan hankalinta yana wajen yarinyar dan ko zuwan da sukayi basu tarar da itaba wajen wata mata ta tafi a gusau wadda suka tafi lagos din tare da bintu ance mata matar ta dawo shine taje neman bayani amma sai matar tace mata ai tun ranar da suka shiga Kano suka rabu ita da bintu dan ko lagos dinma basu je tareba.

Kamar yadda Abdulrahman yace zasu bawa Usman chance mistake daya idan yayi zasuyi masa kafa hakance ta faru amma fa Khadija ta tare duk wata hanya da zasu fahimci yana aikata mistakes din, duk abinda yayi mata ita kadai take shanyeshi ko Bello bata bari ya fahimta, sunsha yin fada kaca kaca da Usman dan tunda ya fahimci ita kanwarsu Abdulrahman ce sannan kuma batayi karatuba sai ya zamana kamar ya rage ganin kimarta da da yakeyi, son da yakeyi mata ya ragu nesa ba kusaba, wani lokacin har tunani yakeyi wai ta yaya da yayi mata wani mugun so lokaci daya amma yanzu sam babushi, sam ya daina kiranta ko tura mata text kamar da wani lokacinma sai dai ita ta kirashi ko ta tubure tace zataje gidan dady kawai saboda ta ganshi wanda shi yanzu duk ya daina, idan sun fara shiri kamar gaske dan mistake kadan sai ya hau ya kuma ki saukowa akwai wata rana suna zaune a dan filin dake bayan gidansu khadijan wajen kamar garden ta maidashi tana danyin yan shuke shukenta sai ta maida wajen wajen zance duk sanda yazo zata dauko musu fararen kujeru su zauna a wajen, suna zaune tana ta faman bashi labarin Bello irin abubuwan da yake siyo mata idan ya dawo daga duk inda yaje aiki da irin yadda yake nuna mata soyayya kamar zai cinyeta Usman ya danyi tsaki yana juyar da kai gefe Khadija tace "menene yaya Usman?" ya kalleta fuska a hade yace "ke wai baki da abin magana ne sai Bello? Yaya Bello this yaya Bello that haba" Khadija ta dan harereshi irin na wasa dinnan tace "kishi kake?" Usman ya kuma daure fuska ya harareta yace "Allah ya sauwake na rasa da wanda zanyi kishi sai almajiri" Khadija itama ta dan hade rai tace "wai yaya Usman dan Allah me yasa kakeyin haka? Komai akayi kace almajirai da tone din da yake nuna kamar su din abin kyamane" Usman ya danyi murmushin gefen baki yace "au da ke baki taba sanin cewar almajirai abubuwan kyama bane?" ta mike tsaye "yaya Usman yayyenane fa" shima a zuciye ya mike yana kallonta yace "idan bakyason na nuna asalin yadda nakeji akansu ki daina yimin maganar wani Bello" hawaye ya fara taruwa a idonta tace "Allah sarki shi kuma kullum yana cikin tambayar yadda kake shine kadai yake goyon bayan soyayyarmu amma kai babu wanda ka tsana irinsa" Usman yace "eh na tsaneshi saboda munafikine sonki yakeyi amma sai ya dinga nuna kamar ba haka bane" Khadija ta goge hawayen idonta tace "ai gwarashi ko yana sona amma ya danne son da yakemin din saboda farin cikina ba irinkaba da kullum kake kaunar bakin cikina" Usman ya watsa hannu sama yana cewa "ok then zeki aureshi mana na damune?" ya juya zai bar wajen ta dan daga murya tace "yaya Usman ka daina yimin abinda kakeyi" a zuciye ya juyo yace "me nayi miki? Eh yeh nace me nayi miki?" ta cigaba da tsiyayar da hawaye tana kallonsa ya kare mata kallo sannan yayi tsaki yace "matsalar mu'amala da jahili kenan dan kauye komai kayi masa laifine" ba tare da ya kuma bi ta kantaba ya juya yayi ficewarsa daga wajen.

Ire iren wadannan abubuwan na yawan faruwa sai dai ta zauna tasha kukanta ta godewa Allah amma ba zata gayawa kowaba da farko Amira taso ta dinga gayawa sai kuma tayi tunanin Usman dan uwan Amira ne kuma ance blood is thicker than water dole wata rana Amiran zata iya jin haushinta akan dan uwanta, taso gayawa Bello kuma sai tayi tunanin ya rantse indai Usman din ya wulakantata sai ya rabasu ita kuma batason a rabata da Usman din sasantasu takeso ayi, su Abdulrahim kuwa ko giyar wake tasha ba zata taba fada musuba dan tasan dama can ba kaunar Usman din sukeyiba.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now