Watan Ramadan watan albarka wata mai girma a duniyar musulunci, watan sadaka da kyauta kowa na cikin farin ciki da zuwansa, hakan ceta kasance gasu Abdulrahman wannan shekarar duk da wancan Ramadan din da sukayi sun dan sha wahala amma wannan kam basu da wata damuwa dan suna da abinci na buda baki da sahur kullum a gidan dady, wani lokacin ma har sai dai su bayar saboda wasu mutanen ma sunayin sadaka to idan sukazo wucewa sukaga ana sadaka sai su tsaya su karba sannan kuma ga na gidan dady wanda wani lokacin ma acan suke shan ruwan, duk ranar da sukaje shan ruwa can to kuwa ranar Usman bazaici abinci cikin jin dadiba, wani lokacinma tashi yake yayi tafiyarsa duk da bawai tare sukeci ba, wannan yasa sai suka koma duk ranar da akace suzo suci abinci a gidan to a harabar gidan inda dady ke ajiye mota suke fita suci abinsu acan sai dai fa tabbas ranar Amira ma anan zataci nata dan kwano daya takeci tare dasu.Haka sukayi azumin har yakare sallah ta gabato dady yayi dinkin sallah har dasu dama Amira ta gaya musu an kai musu dinki sai dai basuyi tsammanin da gaske takeba sai da sukaga kayan a hannunsu harda sababbin takalma irin kyadi dinnan kowa daya, ai kuwa sunyi murna sosai ranar sallah suka yi wanka suka saka kayansu sai gidan dady, suna zuwa suka tarar suma sun shirya zasu tafi masallaci dan haka suka rankaya tare sai dai fa Usman na fitowa ya gansu kuma suma sunyi kwalliya duk da yadin ba iri daya bane amma kalar dayane daga nesa zaka zata iri dayane ai kuwa ya juya yace wallahi masallacinma ya fasa zuwa sai da suka tafi sannan ya fito ya je wani masallacin daban.
Haka suka jera kamar family daya sukayi sallah sannan dady ya tasosu a gaba gaba dayansu suka dawo gida inda suka tarar momy ta kamala abincin sallah aka zubo musu kowa ya baje sukaci suka koshi sannan dady yace su taso a tafi yawon sallah, da fari da suka fito su Abdulrahman sallama sukayi musu da niyya sanin kuma inda dare yayi musu sai dai dady na fitowa ya gansu suna fita daga get din gidan yayi kiransu bayan sun dawo yace “ina kuma zakuje? Sai mun jiraku ko me? Oya ku shiga muje muyi sauri” kafin ya gama rufe bakinsa Usman da ya shiga mota yayi saurin fitowa yana shirin komawa cikin gida dady yace “kai kumafa? bana son iskanci ina yiwa wasu Magana kaimazaka fito wallahi sai na tafi na barku” Usman na zumbura baki yace “dady na fasa zuwa” dady yace “saboda me?” Usman yace “yanzu dady tsakani da Allah gidan Innan (kakarsu mahaifiyar dady takwarar Amira) ma sai munje da wadannan almajiran? Shikenan yanzu mu bamu da sirri komai dasu zamuyi? Ni gaskiya bazan iya wannan abin kunyarba haka kurum abokaina su ganni da almajirai a mota” tsawa dady ya doka masa yace “zaka wuce ka shiga mota ko sai na ballaka? Wane rashin mutuncine wannan ni zan yanke hukunci kace wani kai ba zaka iyaba? Ni na haifeka ko kai ka haifeni? Dallah malam shiga mota muje” Abdulrahman da yayi tsuru tsuru a tsaye yace “dady ko kuje kawai mu…” kafin ya karasa dady yace “zaka shiga mota muje ko sai na makeka kaima? Kaima musun zakayi dani?”da sauri yace “aa dady yi hakuri” sannan ya shiga motar.
Gidan kakarsu Amira suka fara zuwa, tsuhuwa mai kirki da son yara suna zuwa Amira ta tafi da gudunta ta dane cinyar tsohuwar suna dariya tana cewa “takwarata nayi kewarki” Amira ma tace “nima haka Inna ganinan yanzu nazo karbar barka da sallah ta yana ina?” inna ta dungire mata kai tana cewa “bazan bayar dinba ai ba ajiya kika kawominba danane ya bani” Amira tace “dadyna kenan?” duk suka saka dariya.
Bayan an gama gaggaisa wane inna take tambayar dady “Mansur wadannan yaranfa ina ka samosu?” yana murmushin jin alfahari da dadin abinda zai fada yace “almajiran gida nane ko nace yayyen Amirane” sannan ya kwashe duk labarin yadda akayi su Abdulrahman suka shigo gidansa ya gaya mata, yar tsohuwa inna tace “Allah sarki yan yara kyawawa dasu Allah ya rayaku kunji?” duk suka amsa da amen sannan ta kira mai aikinta tace ta zubo musu abinci amma yaran kowa yace ya koshi, Usman ta kalla tace “Usmanu ya akayine tunda kuka shigo kake cin magani ko gidan nawane bakason zuwa?” yana kallonta ya kwabe fuska kamar zaiyi hawaye tace “subhanAllahi me ya faru?” dady yace “hajiya kyale wannan babballashi yakeson nayi idan bai shiga hankalinsaba” inna tace “tohh kaida baban nakane ashe to Allah ya sauwake” daganan bata kuma kulashiba itama sai hirarsu da suka yi tayi da Amira sauran na musu dariya gwanin sha’awa, da zasu tafi ta dauko ‘yan N10 sababbi ta bawa kowa biyar biyar barka da sAllah harsu Abdulrahim sannan suka tafi, daga nan sai gidan anty zulai kanwar dady da yaranta sadiq hamim da muhammad itama sunsha hira sannan ta basu barka da sallah suka tafi, ranar haka sukayi ta zuwa gidajen abokan dady da ‘yan uwansa kowa sukaje ya tambaya su waye su Abdul sai dai yace “’yaya nane” daga nan komai bin kwakwkwafin mutum sai dai kawai yayi dariya amma baya kara cewa komai, Haka ranar suka wuni suna yawo daga wannan gidan sai wannan har dare sannan suka dawo gida da tarin kudin yawon sallarsu.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...