1&2

70 3 1
                                    

💓💔💓💔💓💔

        *SON ZUCIYA NE*

           💓💔💓💔💓💔

(A hrt touching story)

BY
*RABI'ATU AHMAD MU'AZU* ( _Rubby_)



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

_
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai...tsira da amincin Allah su kara tabbata akan Manzon mu Annabi Muhammad S.A.W_

   🌸 Jinjina gareku iyayena INA matukar alfahari daku, a duk Inda nake tare da adduar Allah ya jikan mahaifina ya gafarta masa.

Sadaukarwa ga: anty haleema(Mrs Basheer)
         &
Zahra Abdul(momyn ahlan\in-law)
Allah ya bar zumunci da kauna na gode.

Wannan shine littafina na farko dan haka ina rokon Ku da idan an ga kuskure ko gyara to kofa a bude take.
#one love.

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 1 & 2

 

Kuka ta ke wiwi kamar ranta ze fita, "me ya sa ka ke wulakantani? Me na rageka da shi ? Wanne irin so ne bana maka?" ta kara fashewa da matsanancin kuka hadi da kwanciya akan katifar dake dakin
Ana ta buga kofar amma naki budewa nayi biris da koma wa'ye dan a halin da nake ciki bazan iya magana ba ma ballantana hayaniya, ci gaba da buga kofar aka yi.
"Najla ki bude mana plx nice fa" sauke ajiyar zuciya nayi tare da mikewa ina dafa bango saboda jirin da ya ke neman ka dani, na isa wajan kofar na zare sakatar na juya abina, komawa nayi kan katifar na kwanta tare da rufe idanuna saboda har yanzu zuciyata bata daina radadi ba
"Najla me ya sa ba ki da tunani ne? Shin akanki aka fara soyayya ne ko kuma ke naki salon na hauka ne?" Cewar Asma'u.
"Najla sai yaushe za ki gane Annabi ya faku? Sai yaushe za ki gane karatun maza?"
tsaki nayi tare da juya mata baya.
"hmmm ai dama ba kya so a fada miki gaskiya kuma wlh ko za ki mutu sai na fada ehee!!"
mikewa nayi tare da fadin.
"Dalla Malama!! kiyi abin da ya kawoki ki fitar min a daki dan kina kara min ciwon kai ne!!"
"Hmmm ai dole kice haka tun da bakya son gaskiya" Cewar Asma'u,mikewa tayi tare da fadin.
"wlh Najla ki cire Kabeer daga ranki Sam ba sonki yake ba saboda na sha faɗa miki yaudarar kanki ki ke yi amma kina ganin kamar karya ne, ya kamata ki dawo hayacin ki,ki farka daga duniyar mafarki,ki dawo zahiri dan rayuwarki tayi kyau" mtseww naja tsaki hadi da harararta.
"Ai ba wa'azi na kiraki ki min ba,kuma wlh wlh son kabeer yanzu na fara koda kuwa kullum zai din ga dukana ne, ko kuma ya din ga yankar naman jiki na, karewarta kenan ko!!? to a haka nake son shi"
"Najla kenan ai ke mahaukaciya ce!! kuma wani abu na Damin kwakwalwarki amma ba komai akwai lokacin da za ki gane ba'a ma namiji haka, ba dai Kabeer ba hmmmm to ga ki ga shi ai ance _SON ZUCIYA_ b'acinta!!"
Fita tayi tare da bugo min kofar da karfi, komawa nayi na kwanta tare da jawo wayata na fara dialling number Kabeer amma wajan  20 missed calls bai daga ba sai na tura masa text kamar haka
"Haba Hubby kasan dai yadda nake son ka kuma nake jure duk wani wulakancin da kab ke min,ina bakin kokarina dan kaucewa bacin ranka amma still ban tsira ba sai ka din ga tozarta ni a gaban mutane,hmmmm duk da haka dai bazan gaji da baka hakuri ba, am very sorry dear I will never repeat it bcos I realise my mistake and I promise wannan ya zama na Karshe amma dan Allah ka daga wayana" tura masa nayi duk da nasan bazai min reply ba amma ko ba komai zai karanta,to me yasa dan ya ganni a mota da Mahmood zai mareni ? ba tare da ya ji menene tsakanin'mu ba? kishi ne yasa ya miki haka zuciyata ta bani amsa,  amma bai kamata ya mareni a cikin mutane ba kuma na ba shi hakuri? mtseww ko da yake laifina ne da na tsaya da Mahmoud, mikewa nayi na bude kofar na fita tsakar gida saboda wata azababiyar yunwa na ke ji kuma Ummynah bata nan amma nasan yanzu zata dawo tun da yamma tayi na nufi bakin rijiya naja ruwa nasaka a bokiti na wanke fuskata dan ba na so Umma ta fahinci me ya faru.


Yana zaune a kujera ya kura ma ya jinginar da Kansa a daya daga cikin trowing pillows din kujera yana rera waka hankali kwance ya ji karar wayarsa alamun text ya shigo gajeren tsaki yayi hade da furta "mayya zanyi maganin ki ne a hankali,dan ni ba shashashan namiji bane kuma wlh sai na miki abin da zai kona miki rai fiye da yadda ki ka min, hmmmm!!" wayar ya jawo tare da karanta sakon ya tabe baki yana cewa.
"Yarinta na damunki Najla amma da sannu za ki gane cewar ni KB bana daukar raini I promise 2 teach u a lesson..
tun da nake a rayuwata babu macen da take irin abin da kike min,duk kuwa da cewa ina sonki hakan bazai hanani na hukuntaki ba dan ni na tsani raini,but ke naga kanki na hayaki da yawa amma ba matsala I know what 2 do tashi yayi ya nufi bedroom dinshi Wanda komai na ciki take kamar brown ne ga dakin sai tashin kamshi ya ke yi, toilet ya fada ya sakar ma kansa shower ko zai samu nutsuwa bai wani Dade ba ya fito ya shafa mai ya dauko wata rigar polo yellow ya saka ya saka wando brown tare da agogo da takalmi na kamfanin Gucci ya fesa tirarensa na oud sai tashin kamshi yake,makullin motar shi Mercedes ya dauka ya fito tare da nufar gate yana kwalawa Malam Habu mai gadi kira, a guje ya taho dan yasan halin me gidan na shi da saurin kosawa, russunawa ya yi tare da fadin.
"barka da fitowa yallabai" a dakile KB ya amsa da.
"yawwa dama ina so na ce maka zan fita kuma duk Wanda yazo karka barsa ya Shiga koma wa ye!!"
"Yallabai ko Nasser ne?"  cewar Mal Hadu.
" a'a ko uban Nasser ne!!"  KB ya ba shi amsa tare a shiga mota Malam Habu ya juya da gudu ya nufi gate tare da bude masa ya fice  a guje rufe gate din ya yi yana cewa.
" mutum sai shegen girman kai mtsewww Allah dai ya kyauta."

"Najlah!!!? wai me ki ke yi ne a dakin da ba za ki fito ba ki na ji tun dazu ina kiranki?" turo baki tayi tana cewa.
"Allah sarki Ummynah na gaji ne fa kin san ba wani lafiya bane dani ai na fada miki kaina na ciwo"
Najla ta fada tana fitowa tsakar gida daga ita sai wani three quarter din wando maroon da top baka kan nan ya sha acuci maza.
"yauwa Najla maza ki dauki kudin nan ki kai wa Atikah ta saka min zubin yau dan kinsan na satin nan za'a bani dauka"
" OK Ummynah ba Matsala bari na saka hijabi to"
mikewa tayi ta Shiga daki da sauri jin wayar ta na ringing sunan Hubbey ta gani yana yawo akan screen din wayar gabana ne ya fadi.
"Na Shiga uku me zan ce masa?"
daga wa nayi nasa a kunne "ki fito ina kofar gidan Ku" abinda ya fada kenan ya kashe wayar.
"hmmm yau akwai tashin hankali kenan tun da har ya zo a yau to bai hakura ba wlh nikam ya zanyi da KB ne?"

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Ku cigaba da bina dan jin wannan labarin mai cike da sarkakiya,yaudara,soyayya da kuma cin amana
  RABYN KU CEH
#ana tare one luv

💕💔SON ZUCIYA NE💔Where stories live. Discover now