9&10

9 1 0
                                    

💔💔💔💔💔💔
_
     SON ZUCIYA NE

       
*         💔💔💔💔💔

BY
RABI'ATU AHMAD MUA'ZU (Rubby)
_

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*__ 🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Sadaukar wa ga: Anty Halimah (Mrs Basheer)
         &
Zahra Abdul (Momyn Ahlan \in-law).

Allah ya bar kauna.

Ana tare
#one luv.


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
    _Page 9 & 10_

 
Najla da Kabeer sun hadu ne a wajan siyayya ranar da ta raka kawarta Asma'u, nan take suka kamu da son juna,kuma ita ma Asma'u a lokacin ta kamu da son    Kabeer kuma ta kwallafa a ranta cewar komai rintsi sai ta mallakesa..

@@@@@@@

CIGABAN LABARI

Naseer kuwa mintina 20 ne suka kawo shi gidan Kabeer bai fita a motar ba ma ya kira shi a waya
"Hello friend?"
"Naseer ka iso ne"? cewar KB.
" eh na iso ina bakin gate"
"OK to ka shigo da motar dan ba da ita zamu ba" inji KB
"Ban gane ba da ita zamu ba? me ka ke nufi? to da wacce zamu?
" da BMW " ya bashi amsa a takice.
"OK to bari na shigo da ita" ajiye wayar Naseer yayi,tare da danna ma mai gadi horn, a guje kuwa ya taho ya leka ta karamar kofa, da yaga Naseer ne yayi maza ya bude masa yana ta jera masa gaisuwa, fuska a sake Naseer ya amsa yana ajiye motar a parking lot.
Cikin gidan ya shiga kai tsaye yaga KB a kwance akan kujera yana latsa wayar sa.
" to ai nasan kaji shigowata mal, sai ka tashi mu tafi idan ka gama izzar"
Mtseeww KB yaja tsaki yana cewa
"Bana son hayaniya ai kasan ba kwana zan yi ba ko?"
"Kai dai massifaffe ne wlh cewar Naseer" mikewa sukayi KB ya kullo kofar,suka nufi parking lot, BMW din KB ya Ciro musu,ya cillawa Naseer key.
"Me kake nufi da bani key?"
Kai ne zakayi driving dan wlh ba zanyi ba".
Kwafa Naseer yayi ba tare da ya ce masa komai ba,ya bude motar ya shiga,shima KB shiga yayi suka fice a gidan mai gadi nata daga musu hannu.

Najla kuwa bayan sun gama waya da Kabeer mikewa tayi ta fita tsakar gida, ummy ta gani tana kokarin kunna gawayi,
" ina kwana ummynah"
"Lapiya lau mamanah" dafatan kin tashi lapiya?
"Eh ummynah lpy lau" karbar gawayin Najlah tayi ta cigaba da hurawa suna hirar su da ummy cikin shauki da son junan su.
Mardiya makociyar su ce tayi sallama tana dosar inda suke,
" ina kwana ummy?"
"Lapiya Mardiya,yaya kike, ya kuma yaran"?
" lapiya lau Maman Najla, dama nazo ne na tambaye ki ko kayan nan sun iso? dan matar sai kirana take yi kuma kamar sun matsu ne, kin san nace miki anko ne"
"To mardiyya kin san wlh kayan ne na saro su da yawa,to nadai kira shi dazu tinda kinga daga kano zuwa jos ba za'a dinaga sintiri ba,zai saka kayan zuwa anjima,idan an kawo Najlah zata kawo miki"
Nunfasawa Mardiyya tayi tace
"to shikenan ba damuwa Allah dai ya kaimu lapiya".
  Bayan fitar Mardiya ne na kammala abin karya war,muka shiga cikin dakin ummynah muna karyawa.

Karfe 1:30pm su KB suka isa Kaduna dan ma sun tsaya karbar sako a Zaria kafin su wuce, kai tsaye " THE GREEN HOTEL" suka fara sauka kafin su wuce inda zasu je, suna isa sallah suka fara gabatar wa kafin Naseer ya musu order abinci, fried rice & chips kawai suka iya ci sai coffee da KB ya sha..

Zama yayi ya jawo wayar sa ya dialling number Najlah amma bata daga ba, ajiyewa yayi ya kwanta, ba wuya bacci yayi gaba dashi..

   Najlah kuwa suna gama karya wa tayi wanke wanke,bayan ta gama ne Asma'u ta kirata a waya lokacin tana shirin shiga wanka, dagawa tayi tace
"Hello babe ya akayi ne? cewar Asmy"
"Lapiya lau,ya kike?"
"Qlau,kin San me?"
"a'ah cewar Najlah"
"Ki shirya zuwa anjima yau akwai birthday din Fateemah kanwar Deejerh da za'ayi da yamma"
"OK a ina ne"? Najlah ta tambaya"
"a Red Valley ne"
"Karfe nawa ne? Najlah ta sake tambaya"
"Zuwa dai irin 5:00pm haka"
"Asmy wlh bana son zuwa kinga Kabeer ya hanani,
" dalla matsa,ke banza ce wlh,ina Kabeer din baya gari? to tayaya ma za'ayi yasan kin je?"
"To shikenan Asmy zan shirya muje amma bazan dade ba nikam"
"In dai zaki je ba matsala"
Ajiye wayar Najlah tayi ta shiga wanka, koda ta fito mai kawai ta shafa da humra ta saka kaya marasa nauyi tayi kwanciyar ta.
  

Asma'u kuwa suna gama waya ta dannawa Mahmood kira take fada masa ta amince, wata dariyar mugunta Mahmood ya kece da ita
" hahaha ai Najlah mallaki na ce,kuma wlh sai na dan dana ta tinda nayi niyya, Asmy ke dai kiyi yadda nace miki,fatan kin  fahimta?"
"Eh na gane yadda muka tsara haka zamuyi dan na fada ma Deejerh ma"
"Yawwa Asmy na gode kwarai da taimako" cewar Mahmood,
"Karka samu damuwa ai yiwa kai ne" daga haka ita ma ta kashe wayar tana dariya a ranta tace
" the deal is done, KB nawa ne ni daya,nasan yau rabuwar Ku tazo kai da wannan sakaryar,dan wlh Kai din "SON ZUCIYA TA CE" ta fada tana sakin wani killer smile hade da kwanciya akan katifar ta.

*****

Karfe 4:45pm Najlah ta gama shirya wa cikin wata haddadiyar gown maroon colour,rigar fited ce kuma ta fito mata da duk wasu hallitun jikinta, kwalliya ta buga na kece raini dan dama ita gwana ce a wannan fannin, takalmi ta dakko hill gold colour,da mayafi medium shima gold,ta dakko Yar karamar baby bag dinta, ta zuba kayan kwaliyya,sannan ta dakko 5k a cikin kudin da KB ya bata ta zuba a ciki, turarukan ta masu dadin kamshi ta fesa, waya ta dauka ta kira Asma'u,
"Hello na gama shirya wa"
"OK to mu hadu a bayan layi dan a nan za'a dauke mu"
"To shikenan sai na karaso"
  Fita Najlah tayi taga ummy a tsakar gida da wata mata,zuwa tayi ta gaishe da matar,amsa wa matar tayi cikin sakin fuska, Najlah tace
"Ummynah, na gama bari mu wuce gidan bikin"
"To a dawo lapiya,Allah ya tsare hanya,a dai kula,banda rawar kai, dariya na saka nace to Ummynah sai na dawo,
Fita nayi na nufi bayan layi, ban kuwa dade da tsayuwa ba motar su Asmy tayi parking a inda nake, bude wa nayi na shiga na rufe kofar suka ja muka dauki hanya, 
Kallon Asmy nayi wacca taci uban gayu fuskar nan sai kyalli take yi, nace
" yan mata kyau kenan?"
"Ai kin fini kyau"
"Hmmmm haka dai kika ce"
Hirar mu muka cigaba dayi kafin a isa wajan.

Kabeer bai farka ba sai wajan karfe 4:00pm, wayar sa ya jawo amma bai ga kiran ta ba, mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ya dauro alwala,yana fitowa Naseer na shigowa, bai masa magana ba ya tada sallah, bayan ya idar ne suka fita zuwa company su na Kaduna wanda yake unguwar Malali dan su fara gabatar da abinda ya kawo su.

Koda muka isa wajan,fitowa mu kayi cikin taku irin na manyan mata, muka doshi cikin wajan, guri ne na yaran wane da wane dan kuwa ba karamin kyau wajan yayi ba,gefe daya kuma anyi decoration na balloons, ga kuma wani cake 2 step a wajan, kowa yana ta harkar gaban shi yayin da maza da mata suke ta rawa.
"Najlah bari na kira Deejerh,dan bata San munzo ba kuma na kira wayar ta baya shiga,may be ma ta kashe ko kuma network"
" OK to kiyi sauri cewar Najlah"
Mikewa Asmy tayi ta nufi wata kofa, ni kuma na cigaba da danna waya ta, bayan kamar 10mins sai gasu ita da Deejerh,taci kwalliya kamar wata aljanna,dan wani wando da ta saka kamar zata fashe,saboda yadda ya matse ta,kan nan yaci gashin doki,tana tafiya kamar wacca aka saka dole, karasowa sukayi inda nake, bayan mun gaisa tamin sannu da zuwa, mun zauna muna hira dasu  MC ya fara cewa celebrant ta iso kuma yanzu za'a fara,mikewa Deejerh tayi ta jawo hannun mu nida Asmy,fita muka yi dan shigo da Fateema, bayan mun shigo da ita ne na koma wajan zamana nabar Asmy da Deejerh a wajan.

Deejerh ce ta kawo min wine (non alcohol) ta tsiyaya min,karba nayi da murmushi a fuska ta na  sha,murmushi naga tayi tace
"Na manta bari na kawo miki pizza kici"
"OK to ba damuwa"
Tafiya tayi dan tasan yanzu shirin su zai fara

  Dariya Deejerh ta fashe dashi, Najlah kin gama yawo yau...dan wallahi sai Mahmood ya more..


Toh pha Najlah tana cikin tsaka mai wuya.

Ku cigaba da bina dan jin yadda zata kaya

_RUBBBY CE_
*#ana tare..one luv*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 16, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

💕💔SON ZUCIYA NE💔Where stories live. Discover now