7&8

4 0 0
                                    

💓💔💓💔💓💔

        *SON ZUCIYA NE*

           💓💔💓💔💓💔

BY
*RABI'ATU AHMAD MU'AZU* ( _Rubby_)


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Sadaukar wa ga: Anty Halima (Mrs Basheer)
          &
Zahra Abdul (Momyn Ahlan\in-law).
   
Allah ya bar kauna.

Ana tare
#one luv

Wannan shine page 7&8, nayi mistake ne a wancan page din,shi zai zama 5&6 ne,amin afuwa dan Allah, na gode da kaunar Ku .

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌸
   Page 7 & 8_

Kabeer mutum ne da baya son raini dan ya iya tsare gida, Idan ya hade rai zaka dauka mutuwa aka masa.

Bayan ya kammala Secondary School sai ya wuce (ABU) Zaria, inda ya hada degree dinsa guda biyu a business admin,
Shi kam yana da sha'awar irin kasuwancin mahaifinsa amma kuma yana so ya zamanantar da sana'ar ta hanyar bude kamfanonin sarrafa auduga, dan gaskiya yana da wannan burin tun yana yaro, kuma mahaifinsa Alhaji Al~mustapha ya yi na'am da wannan shawarar ta dansa.

Cikin ikon Allah kuwa a yanzu kamfanonin su babu garin da babu a Nigeria har da ma ɗaɗɗaiku a kasashen ketare (MAI AUDUGA INVESTMENT) sun shahara wajan sarrafa ko wanne irin kayan sawa ne, kuma Allah ya daukaka su dan sun yi suna sosai, dan Kabeer yana da kokari da hazaka akan duk abin da ya yi niyyar yi.

Naseer abokin kabeer ne koma a ince amini,dan shi Naseer ɗa ne ga Al~ameen wato aminin Alhaji Al'Mustapha, kuma su na da kyakyawar fahimta dan tare suke gudanar da harkokin su.

*********
WACECE NAJLAH ?

Mal Muhammad mai siga haifaffen ɗan garin Jos ne a wata unguwa da ake ce masa (NARKUTA) yana da shagon saida siga da shinkafa a kasuwar  y'an kwalli,kuma yana zaune ne a Narkuta tare a matarsa Aminah da yaransa guda biyu.
Adam shine dansa na farko sannan Rabi'u.
Su na zaune cikin rufin asirin Allah,  dan mahaifin su yana tafiya kasuwa dasu dan yana so ƴaƴansa su iya sana'a saboda ita ce gatan da zai nuna musu, sunyi karatun su dai-dai gwargwado, kama daga makarantar boko data islamiyya,.
Adam ne ya fara yin aure inda ya auri wata Yar makotan su mai suna  Maimuna,amma su na zaune a unguwar Zinariya, su na zaune cikin rufin asirin Allah dan Adam mutum ne mai son iyalinsa dan yana kyautata musu, a haka Maimuna ta samu ciki amma har so uku cikin na zubewa baya zama,sai ana hudun ne Allah ya bar musu, murna a wajan bayin Allah'n ba a magana dan su na son haihuwa, tare da addu'ar Allah ya basu mai albarka.

Kwanci tashi ba wuya a wajan Allah Maimuna ta sauka,inda ta haifi ya Mace,amma dai CS aka mata dan bayan haihuwar ma an juya mata mahaifa dan likitoci sun fada musu sai dai a juya mahifar dan tana da matsala kuma ba zata iya daukar wani cikin ba, a haka suka fauwalawa Allah komai, su na fatan Allah ya raya musu yarinyar da suka haifa.
Ranar suna yarinya taci Amina wato sunan mahifiyar Adam amma su na kiranta da (Najlah).
  
Lokacin Najlah na da shekara 2 a duniya Allah ya karbi ran Mal Muhammad Mai Siga da dansa na biyu Rabi'u,sakamakon hatsarin mota da suka yi a hanyar tafiya daurin Aure ɗan abokin Mal Muhammad a garin Katsina, mutuwar da ta girgiza mutane da dama, a lokacin da Adam ya riski labarin mutuwar sai da ya suma dan Allah ne ya yi ba tare da shi za'a tafi ba, saboda Idan suka tafi dukkan su babu wanda zai kula da shagon su Idan suka tafi dukkan su, mahaifiyar Adam ma ta shiga damuwa dan kuwa rashi biyu a lokaci daya ga miji ga danta ba abu bane mai sauki, amma a hakan take daurewa ta danne, dan kuwa ta yi tawwakali da kaddarar da Allah ya aiko mata.

Adam shi ya ci gaba da kula da shagonsu bayan rasuwar mahaifinsa da kanninsa shi da abokinsa Anas,tare suke gudanar da komai nasu cikin aminci da rikon amana, kuma a lokacin ya gina gidansa a nan Zinariyar inda suka tattara suka koma shi da Iyalansa.

Najlah ta kammala makarantar primary da secondary (AREWA MODEL SCHOOL)
Najlah yarinya ce kyakyawar dan fara ce ita amma ba irin sol din nan ba,tana da madaidacin hanci da kuma dimples, ita ba doguwa bace kuma ba za'a kirata da gajera ba tana dai tsaka-tsaki, Najlah ta taso da rawar kai na ban mamaki saboda lakabi da ake mata da MATAR MANYA, shi yasa take jinta a sama,dan ma tana yi tana tsoron mahaifinta,amma Idan ta fita gari za ka dauka yar wani mai mukamin gwamnati ne.
Kawancen su ya samo asali ne da Asma'u tin daga school dan tare suke zuwa kuma su dawo tare kasancewar layin su daya,
Asma'u baka ce amma ba ƙirim din nan ba sai dai ta bata kanta da bleaching dan ita tana hassada da kawarta saboda ta fita kyau nesa ba kusa ba,kuma ita akwai munafurci sabanin Najlah da bata da boye-boye Indai an mata sai ta fada, dukkan su yan gayu ne na karshe musamman Najlah da take jin kanta a sama dan Idan ta dau wanka ba zaka tantance Yar waye ba.

   Kwatsam Allah ya yi Mal Adam rasuwa,sakamakon  zazzabin kwana daya daya yi,dan ya jigatu gaskiya,Ashe ciwon ajali ne ya kama shi, mutuwar da ta razana Najlah da Mamanta, dan wannan rashin ya dade bai sake su ba, ya rage daga su sai Kakarsu Amina a cikin gidan dan tin da aka yi rasuwar bata koma gidanta ba.

A haka Mal Anas amininsa ya ci gaba da tafiyar da kasuwancin nasu inda yake rike musu dukiyarsu tsakaninsa da Allah kuma yake kula dasu, ita kuma Mama Maimuna tana saye da siyarwar kaya, kamar su atampha, laces,shadda,gyale,da takalma, shi yasa gidanta baya rabo da mutane,kullum mata na sintiri a gidanta dan siyan kaya.

        @@@@@

Ku ci gaba da bina dan yanzu aka fara labarin.

*Comment & share*

*RABYN KU CE
#ANA TARE°°*

💕💔SON ZUCIYA NE💔حيث تعيش القصص. اكتشف الآن