5&6

7 0 0
                                    

💓💔💓💔💓💔

        *SON ZUCIYA NE*

           💓💔💓💔💓💔

BY
*RABI'ATU AHMAD MU'AZU* ( _Rubby_)



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Sadaukarwa ga:anty haleemah(Mrs Basheer)
       &
Zahra Abdul (momyn ahlan\inlaw)

Ina godiya sossai da karamcin Ku a gare ni,Allah y bar kauna.
   
   Wannan shafin naki ne my cwt sis smart feenert b~smart, kiyi yadda kike so dashi, luv u like.......
Ana tare
#one luv

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 5 & 6

Kara sheƙewa da dariyar mugunta suka yi tare da tafawa.
"hmmmm ai wlh sai na raba soyayyar Ku wannan alkawari ne na dauka"
"ki bar komai a hanunna" cewar Deejerh
"ni na san maganinta,sai na saka mata kunci da bakin ciki kuma sai nasa taji ta tsani soyayya wannan alkawari ne na dauka"  ci gaba da hirar su suka yi ni kuwa na ce Allah ya kyauta.

   Koda gari ya waye tashi na yi zuciyata fes da ita na jawo wayata na kira Kabeer, ɗagawa ya yi daga can bangaren ya furta
"Hello" murya can kasa.
"ina kwana?"
"lpy lau Babyta,da fatan kina lpy?"
"lpy lau,ba yanzu za ka tafi bane?"
"eh sai kamar 9" ya bani amsa.
"OK to Allah ya taimaka" da ameen ya amsa, ya san yana son Najlah amma rawar kanta ne yake damun shi kuma hakan zai iya haifar mata da matsala ko da nan gaba ne, duk da shi ma ya yadda da son da take masa amma dai ya san ba shi kadai take kulawa ba, to meye nata na raba kafa? ,wannan abu shi yake kara ba shi haushi Idan ya tuna.
"Hello kana jina?" ajiyar zuciya KB ya yi dan yama manta waya ya ke yi, sbd ya tafi duniyar tunani.
"Idan na shirya amm zan kiraki"
"OK to shikenan, I will be expecting, but pls luv make sure u find something and eat before u leave dan nasan halinka" dariya ya yi tare da fadin.
"alright karki damu zan karya" ajiye wayar ya yi, ya miƙe ya shiga hadadden toilet dinsa ya yi wanka ya fito yana shafa mai ya ji wayarsa na ringing gajeren tsaki ya ja mtseww ya dauko ya ga Nasser ne.
" hello frnd?"
"ya aka yi?" cewar KB.
" lfy lau skipper Ashe ka tashi, yaushe zamu wuce?"
" nan da 40mins haka"
"owk Allah ya kaimu"
"Ameen ya rabbi" ajiye wayar ya yi, ya gama abin da yake yi ya isa wajan drawern kayansa ya dauko wasu hadaddun suit, da gani kasan masu tsada ne ash colour da Yar ciki fara kal da ita sakawa ya yi tare da agogonsa baki da takalmansa suma black ,wow Ma sha Allah na furta da na yi arba da kyakyawan saurayi,gaskiya KB ya hadu ta ko ina,shi skin din sa chocolate colour ne amma kuma ya hadu masa da tsabar hutu,jin dadi da kwanciyar hankali kuma ga arziki Allah ya masa ta ko ina ,idanun nan nasa masu kyau kuma shi dogo ne amma ba siriri ba,ga hancin shi irin na Fulani ,
"Keys ya kwasa tare da wayoyinsa yana fita daga bedroom din kai tsaye parlour ya nufa ya zauna a kujerar dinning yana hada tea, wayarsa ya dauko ya fara kiran naseer.
" hello Alhaji na gama ka sameni a gida mu wuce" abin da ya fada kenan ya kashe wayarsa ba tare da yama ji me naseer din yake fada masa ba.

Waye Kabeeer?

Alhaji Musa Ibrahim haifaffen garin kano ne a kumbotso local government,yana zaune da matarsa Inna Dije,da kuma yaransa guda 3 maza biyu mace daya, Al~Mustapha shine Ɗansa na farko sai Nurudeen sannan Ikleema, su na zaune cikin rufin asiri dan shi manomin shinkafa ne sannan yana harkar auduga dan Idan kaje kumbutso kace kana neman Alh Ibraheem mai auduga to an San shi dan fitacce ne a wannan harkar kuma ana ma gidan shi lakabi da gidan mai auduga, yaransa sun taso cikin tarbiyya da gata, ba wai ya sangartasu bane ba, dukkan su su na zaune cikin soyayya da kaunar junan su, Al'Mustapha yana da shekara 20 ya gama secondary school anan garin nasu inda ya samu gurbin karatun jami'a a university of jos (u j),inda zai karanci political science, shi kuma Nurudeen yana SS 2 ne makarantar government secondary school kumbotso,lokacin yana da shekara 17 a duniya,ita kuma Ikleema tana aji daya a makarantar lokacin shekarar ta 12, duk da su na karatun boko hakan ba ya hanasu karatun addini dan kuwa Alh Ibraheem mai auduga a tsaye yake dan ganin ya'yansa sun samu karatun duniya dana lahira,
  Inna Dije ƴa ce a wajan mai garin na kumbotso, mace ce ita mai tarbiya da sanin ya kamata gata da kawaici da daraja dan adam, auren soyayya suka yi da Alh Ibraheem,har Allah ya albarkaci zuri'ar su...
  Al~Mustapha ya fara karatun shi a sa'a kuma shi ma ya fantsama harkar auduga daga kumbotso zuwa jos kuma Alhamdulillah ba shi da wata matsala dan bama ya tambayar mahaifinsa kudi kuma mahaifinsa na taimaka masa sosai, kaf department dinsu babu Wanda bai san Al~Mustapha Ibraheem mai auduga ba sbd hazakarsa da kuma nutsuwa,akwai kwakwalwa ga kwarjini a idanun jama'a, abokanansa guda 2 ne a cikin makarantar Al'ameen da Auwal su ma tasu tazo daya ne dan su na son mutum mai hazaka,yana da zuciya Idan ka tabo shi kuma baya daukar raini,
  Yana ajin karshe amma zaka dauka wani dan siyasa ne sbd yadda yayi fice a jamiar ta uni jos, akwai wata wadda suke mutunci da ita Sumaiyya Abbas mai atampha, mahifinta sananne ne agarin jos dan yana da manyan shaguna a abuja market inda yake siyar da atampha,laces,shadda a mayafai ga kuma gyale da dogayen riguna, mai atampha ventures ya shahara sosai dan saukin su da iya kasuwanci,
Sumaiyya mace ce fara tas da ita tana da hanci dai-dai nata da idanu dara dara,amma fa akwai son gayu dan Idan ta dau wanka sai ta burgeka ta baka sha'awa gata da tsafta, amma fa tana da nuna isa da son asan ita wata ce.


Mujee xuwa......



RABYN KU CEH
#ana tare luv u all

💕💔SON ZUCIYA NE💔Where stories live. Discover now