Auren Bazata page 9

400 15 0
                                    

✨AUREN BAZATA ✨

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
     SHUKRAH


Edited page....


0⃣9⃣


7:30 pm safeer ya isa gidansu Shukrah, bayan yayi parking motar sa ya fito ya nufi cikin gidan rike da shopping d'in daya yi musu,dukkansu a palour ya samesu ya  durkusa  har k'asa suka gaisa da Daddy sannan Ammii.
Ya Shafa kan Areef dake kwance kan carpet da book's a gabansa da alama Assignment yake yace "Boy,how are you?"
Areef ya masa murmushinsa me kyau yace "Not bad" kafin ya mayar da hankalinsa kan abinda yake.
Bayan kamar 10mints suka fito gabaki d'aya don musu rakiya, har gaban motar su suka rakasu Ammii na dad'a yiwa Shukrah nasiha kan tabi mijinta. Areef dake rik'e da hannun Safeer ya marairaice kamar zeyi kuka yace "Uncle zan biku"Safeer ya kalli Ammii kafin ya kalli Areef d'in da sigar lallashi yace "A'a Areef gobe akwai school ka bari ran friday zanzo sai mu tafi"
     "To" kadai yace yayi pouting don baiji dad'i ba,a hankali kuma ya juya ya  koma cikin gidan kamar zai fashe da kuka,Ammi ma tabi bayansa bayan taga tashin motarsu.
Minti talatin ne ya kaisu Shukrah gida, bayan Safeer yayi parking  suka fito a tare  kowa ya nufi dakinsa.

washe gari Safeer gidansu yakai Shukrah da zai tafi office. Da murnar Mamah ta tare ta, bayan ta gabatar mata da abun motsa baki ta kira mata Aysher ta fice ta basu guri.
    Hira sosai sukeyi da Aysher anan ta gane Aysher nada kirki,aranta tace dukansu suna da kirki da son mutane sosai.
Zuwa can kuma ta,kalli stairs kamar me neman wani kafin ta mayar da idanunta kan Aysher tace  "Aysher wai ina Miemie ne?"Aysher tati murmushi tace "Miemie taje school amma yanzu zaki ganta ta dawo sabod suna exams ne" a hankali Shukrah tace "To Allah ya dawo da Ita lafiya"
     Da"Ameen" Aysher ta answer sannan suka cigaba da hirar su as if they know each other for a long time.
  Ko da lokacin girki yayi ma tare sukayi da Shukrah kasancewar Shukrah ta iya girki sosai. 12:14pm Miemie ta shigo cikin gidan da gudun ta kamar an jefo ta aiko tana ganin Shukrah tayi gurin da gudu ta fad'a kanta tana murnar ganin ta. Itama da murnar ta take tambayar ta "ya exams" with over excitement Miemie tace "Exams Alhamdulillahi Aunty, ina ya safeer?"Shukrah taja cheek d'in Miemie da har lokacin tana jikinta softly tace "Yaje office miemie" Ta answer da "to" kafin ta d'agata sannan tashiga cikin don yin wanka,a tare sukayi lunch suna ta hirarsu abun sha'awa sai dariya suke most especially in Miemie tayi wani shirmen,daga baya Mamah tayi joining d'insu suka cigaba da hirar,ta kuma sha mamakin yadda Shukrah ta saki jiki da ita kamar ita ma 'yar ta ce suka dinga hira,a hankali Mamah ta dinga jin k'ainar Shukrah a ranta,Asr prayer ce ta tashesu daga zaman hirar,bayan sun idar kuma sukaje sukayi clearing dishes tare suka shiga aikin girka dinner kuma.
     08:40pm Safeer yazo ya d'auki Shukrah inda Mamah ta cikata da tsaraba suka rakasu har gurin mota,suna ji a ransu basa son rabuwa da ita don a d'an yinin da sukayi tare ba k'aramin shiga zuk'atansu tayi ba. Miemie data kasa hak'uri ce tace "Aunty Shukrah zan biki" ta k'arasa a hankali yadda Safeer  ba zaiji ba,Shukrah cike da k'aunar yarinyar tace da sauri "To jeki d'ebo kayanki mu tafi" in a whisper Miemie ta kuma cewa "Aunty Mamah bazata bari ba saboda school" Shukrah da bata ji dad'in maganar ba tace "To kiyi hak'uri ran friday zansa Ya Safeer yazo ya tafi dake kimin weekend a chan ko?" Ihu murna tasa ta shige cikin gida da gudu. Mamah daketa kallonsu ta girgiza kai tana murmushi itama ta juya ta koma ciki suka bar Aysher a tsaye har sai da taga sun fita gate ta koma.
      

*Friday*✨
Yau ta kama friday kamar yadda Safeer yayiwa Areef alk'awari yaje ya d'auko shi bayan sun sha fama da Ammii wai baza shiba zai takura musu.
  Ko da suka shiga cikin gidan Shukrah da Miemie da Aysher wanda basu d'ade da zuwa ba  suka samu a parlour suna hira abinsu. d'akinsa ya zarce bayan sun gaisa dasu Aysher don watsa ruwa.
mamaki ne ya cika Aysher ganin Shukrah ko kallon Safeer batayi ba ballan tana ma ta gaida shi,sai ta fara wondering wai dama har yanzu basa zaman lafiya ne?.
Ataikace dai su Miemie yini sukayi a gidan sai da daddare Safeer ya maida su gida.
11:00pm Shukrah,Safeer, Areef na zaune a palour suna kallo, Safeer ne ya mik'e yayi wa Areef sai da safe sannan ya wuce room d'insa. Mik'ewa shima Areef yayi yana rik'e hannun Safeer yace "Uncle ni a gurinka zan kwana" murmushi Safeer yayi yace  "To Areef je Aunty tama wanka kazo mu kwanta"
  "To" yace sannan ya wuce d'akin Shukrah da tunda suka mik'e itama ta tashi ta tafi nata room d'in.

Bayan Shukrah tayi wanka ne tayi diciding saka wata sleeping gown d'inta dake cikin akwati a saman wardrobe,kujerar dressing mirror ta janyo gaban wardrobe ta hau,accidentally k'afarta ta zame ta fad'o k'asa aiko ta fara k'ara sosai ta rike k'afar tana cigaba da ihu,tun tanayi ita kad'ai a daki har ta saki ihunda yasa Safeer farkawa a gigice.Besan yadda akayi ba kawai sai ganinsa yayi a k'ofar room d'inta,da sauri ya k'araso d'akin inda ya sameta tanata juyi a k'asa. jikin sa har wani rawa yake yana k'ok'ari d'agata sai jero mata sannu yakeyi.
Haka dai ya d'agata ya kaita motar sa sannan ya dawo d'akinsa d'aukan key,Duk wannan abun da akeyi Areef be saniba baccin sa kawai yake hakan ne ma yasa Safeer be ta6a shiba ya d:auki key d'insa ya fice da sauri.
Kai tsaye Aminu kano teaching Hospital ya wuce da ita inda cikin sa'a aka kar6eta akayi emergency da ita.kaiwa da komowa kawai yake a bakin emergency gumi duk ya jika shi, sai tunani yake azuciyar sa 'wannam wani irin ciwo ne yarinya sai ihu take gashi tak'I bari ma ya duba mata k'afar,yana cikin wannan tunanin ne wata Nurse ta fito take gaya masa an bawa Shukrah gado amma ba wani serious abu bane kawai buguwa tayi a k'afar sai kuma cikinta daya rik'e tace mararta na mata ciwo, takuma bashi list na maganin da ake buk'ata. sai asuba bayan Safeer ya dawo daga mosque ne yasamu ganin Shukrah. koda yashiga cikin d'akin idonta biyu tana ganishi ta d'auke kai tare rufe ido kamar me bacci. a sanyaye yace "ya jikin?" ya tambaya yana zama abakin gadon. Kamar baza tayi magana ba sai kuma chan tace "Da sauki" ya d'ora da "Allah ya k'ara sauki to". shiru ne ya ratsa d'akin kafin Safeer ya d'auko wayarsa yayi dialing number'n Aysher,Bayan sun gaisa ne yake fad'a mata Shukrah ba lafiya yanzu haka ma suna Asibiti. Suna gama wayar Aysher d'akin Mamah ta shiga ta gaya mata sannan ta wuce kitchen don had'a musu breakfast.

**
  Kallon sa take tanason masa magana amma takasa.,shine ya fahimci hakan a nan ya tambayeta "wani abu kike so?"ta,langa6ar da kanta gefe tace "Ammii nakeso ka kira min" bece komai ba yashiga dialing number'n Ammii inda yana shiga ya m'ika mata tare da ficewa a d'akin.
kusan tare Ammii da mamah suka iso,Bayan sun gaisa ne Mamah ta yiwa Shukrah ya jiki. da ladabi ta answer sannan ta gaidasu duka.
"Shukrah wai meke damunki ne?" Ammii ta tambaya,kamar bazata answer ba chan tace k'afana ke ciwo da marana",Baki sake Ammii take kallon ta da mamaki waiciwon mara. ita dai tasan in mace na ciwon mara da zaran tayi aure take denawa, likitoci da kansu suke bada shawarar auradda mace mai ciwon mara. to meyasa har yanzu Shukrah take ciwon mara, kardai har yanzu ba abinda ya shiga tsakanin yaran nan?

   Inko hk ne Shukrah zata gane kurenta,ta ayyana a ranta zuciyarta tana k'ara 6aci...........


Shukrah Cute

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now