Auren Bazata page 13

387 15 0
                                    

✨AUREN BAZATA ✨
(2017)






WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
     SHUKRAH






1⃣3⃣

Washe gari

Yau ma tare sukayi breakfast after Shukrah ta gama morning routines d'inta,suna kammalawa Safeer ya d'auki briefcase d'insa heading to entrance door yace "Sai na dawo" Shukrah da tun d'azu taketa gathering courage don tana son ta bishi ya kaita gidan Mamah amma she's afraid of him to say she's going no where because a week d'in ya kaita gidan,bayan ta matso kusa dashi ne underneath her breath tace "Ya Safeer zan bika ka sauke ni a gidan Mamah na dad'e ban ganta ba" ta k'arasa tana langa6ar da kanta gefe,kallon pity face d'inta yayi yaji yana son yin dariya amma sai ya dake yana kallon wall clock yace "To je d'auko mayafin ki mu tafi sauri nake", excitedly ta wuce bedroom d'inta tayi rolling veil d'in Abayarta ta fito bayan ta k'ara spraying cool perfume d'inta.
Da kansa ya bud'e mata front seat ta shiga shima yashiga and he dropped away. Tafiyar 30mints ne ya Isa Safeer ya sauke Shukrah a gidan Mamah sannan ya wuce office.
Sanda ya k'arasa be ga  Haiydar a compound d'in company ba kamar yadda ya saba kullum da Safe sai ya jirasa ya k'araso sun gaisa kowa yake wucewa office d'insa.
"Haiydar fa?" Safeer ya tambayi Massinger'n sa time d'in daya k'araso ya kar6i briefcase d'insa,cike da ladabi yace  "Be k'araso ba",sai da suka k'arasa k'ofar office d'in ya kar6i jakarsa sannan yace "okay nagode" ya fad'a yana shigewa office d'insa.
    Sai 5:00pm sannan Safeer ya tashi a office, kai tsaye office d'in Haiydar ya wuce dan yasan yana fushi dashi ne shiyasa ma yau bezo gurin saba"
Da sallama ya k'arasa ciki kafin ya zauna a kujeran dake facing d'insa,Ciki ciki ya answer sallamar ba tare da ya dago ya kalle saba,Safeer ganin he's not ready to talk yasashi cewa  "Haba Haiydar me yayi zafi wai haka?" Harara ya watsa masa sannan strictly  yace "Ban Sani ba",Safeer ya k'ara yin k'asa da murya yace "kaga in dai akan number ne kayi hak'uri ni gaskiya bazan iya baka number yarinyar nan ba dan bana son rainin hankali, ba a wasa da itama ya aka cika balle ana wasa da ita" wata hararar Haiydar ya aika masa kafin yace "kaga malam karka samin ciwon kai ka gane, kace bazaka bada number ba nace zanje da kaina na kar6a ba shikenan ba" Safeer ya d'aga shoulder's d'insa yace  "Shikenan kam, kaga yanzu gidan zanje sai kazo mu tafi ko" Haidar a masife yace "Ba zani ba ai nima ina da motar ka tafi kawai in na gama zani da kaina" sai da Safeer ya mik'e yana dariyar rigimar abokinsa kafin yace  "Allah ya baka hak'uri Haiydar naga ka d'auki abin da zafi, bari na wuce zanje na maida shukrah gida ne, sai ka tawo" Haiydar da takaicin bak'in cikin da Safeer yake masa da haushin pampering matarsa da yake suka had'u suka cikashi yaja tsaki,kafin ya cigaba da abinda yake ba tare da ya kalli inda Safeer yake ba. Safeer ma be k'ara cewa komai ba sai fitar da yayi ya shiga motar sa ya nufi gidansu.

Kan cinyar Shukrah ya taradda Miemie tanata zuba mata zance suna ta kyalkyala dariya abunsu,
zama yayi yana kallon su bayan yayi sallama,yace  "ke zo nan?" ya nuna miemie yana hararar ta,k'ankame Shukrah tayi tana cewa Aunty kin ganshi ko ze dakeni Dan Allah karki barsa kinji?",Shukrah ta k'ara rik'eta a jikinta tana murmushi tace "Me kikayi masa?" ta ida' tana dago kanta. Raba ido Miemie ta shiga yi dan tasan batada gaskiya kafin tace "Nidai Aunty kawai ki bashi hak'uri","To" tace sannan ta juya tana kallon Safeer kafin tace  "Ya Safeer Dan Allah kayi hak'uri bazata sake ba",Safeer yana hararar Miemie yace  "Da kin barni na fasa bakin rashin kunya ai".
Daga haka sukayi shiru har a nan Miemie na jikin Shukrah kamar wata munafika sai leken Safeer takeyi.
Mamah ce ke saukowa daga upstairs tana kiran miemie,duka suka d'ago suna kallonta kafin Safeer yayi k'asa daga kujerar da yake ya d'urkusa yana gaida Mamah cike da ladabi.
Ta zauna tana answer wa kafin tace "Ashe ka shigo bakayi magana ba" cike da ladabi yace "Yanzu na shigo ai, zuwa nayi na zane autar ki" Mamah tayi dariya tace "Me tayi kuma?nifa a kyale min 'ya an takura mata wallahi" yayi murmushi kafin yace 
"Rashin kunya tamin" daga nan ya kwashe yadda sukayi a waya jiya ya gaya mata, Dariyar shirmen Miemie sukeyi dukansu, banda Safeer daya had'e rai don shi bega abin dariya a ciki ba.

      Se bayan sallar isha sannan su Safeer suka koma gidansu.

*********
To haka dai rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin girmama juna amma babu abinda ya taba shiga tsakanin su.

*
   Yau ta kama Friday tun safe Shukrah kejin ciwon mara tana cijewa sai fargaba take kar ciwon yayi worst har dare tana abu d'aya.
7:12pm Safeer ya gaji da zaman falon da yake shi kad'ai, don duk yau bega Shukrah ba se yakejin ba dad'i don ko ba komai sun saba kuma amanarsa ce ita. 'Dakin ya tura ga mamakinsa sai ya ganta kwance tana juyi, da hanzari ya karasa bakin gadon yana jero mata sannu.tana ganinsa kusa da ita ta rik'e hannunsa tace "Ya Safeer dan Allah karka gayawa Ammii banida lafiya xzata min fad'a wallahi" ya shiga shafa kanta duk ya rud'e yace "Bazan fad'a mata ba Shukrah bari mu tafi asibiti" ta k'ara d'amke hannunsa tace "A'a bazan iya ba ka siyo min magani kawai mutuwa zanyi wallahi" ya dafe kansa yace "subahannalli "Bazaki mutu ba Shukrah bari na kira Doctor ya duba ki".
wayarsa ya d'auko ya kira, Dr. Waheeda ya santa tun a Secondry school.
   "Hello Waheeda" yace bayan tayi picking,
"Na'am Safeer ya gida"
   "lafiya kalau Doctor,Dan Allah idan bazaki damuba gidana nakeso kizo Madam ba lafiya" yace.
tace "Subahanallahi yimin sending address din gidan gani nan zuwa",daga haka ya mata sending ya,koma ya cigaba da jerawa Shukrah sannu.
Ba afi 40mints ba sai ga Waheeda ta zo, kai tsaye bedroom din Shukrah ya kaita ya fito ya basu guri.
Waheeda tabawa Shukrah treatments da suka dace amma tana mamakin yadda matar aure take irin wannan ciwon,Kasa hak'ura tayi sai da ta fita ta kira Safeer ta had'a su ta tambaye su "shin wani abu be ta6a had'a su bane ko me?",kunya ce ta rufe su dukansu kowa ya d'auke kansa not ready to talk. Ganin haka yasa waheeda fara masifa,tayi tayu to her satisfaction  kafin ta dawo nasiha tana kallon Shukrah tace  "Haba Shukrah ya zaki hana mijin ki kanki bayan kinsan hukuncin yin hakan (haramun ne miji ya kiraki shimfidar shi ki k'i, mala'ikun Allah zasuyita tsine miki ne har izuwa wayewar gari) ko kinason Allah yayi fushi dake ne? Ko kuma kinason mijin ki ya fara bin matan waje?"
Da sauri Shukrah ta girgiza kanta alamar "A'a" kafin ta fara magana a kunyace
"To aini be ta6a cewa nazo d'akinsa mu kwana ba",Tana gama fad'ar haka tafice daga d'akin da saurinta.
Dr.Dawo da kallonta gun Safeer tayi tana masa kallon tuhuma tace "Hakane safeer?" Ta ida tambar tana hararar sa,murmushi Safeer yayi kafin ya zauna a gefenta.
Nan Safeer ya kwashe duk yadda akayi akai auren da kuma zaman da sukeyi a gidan har i zuwa yanzy ya fad'a mata.
sosai Waheeda tayi mamaki takuma bashi shawara, kafin ya rakota har parlor nan suka sami Shukrah a zaune Waheeda tayi mata sallama had'e da kar6an number ta da niyyar bata shawarwari .
Har bakin mota suka rakata sai da motar  ta fita daga cikin gidan sannan suka dawo cikin gidan cike da kunyar juna...........







Shukrah Cute🥰

AUREN BAZATAWhere stories live. Discover now