Labarine wanda yake fadakar da iyaye akan illan auren jari duba ga yanda yarinyar cikin labarin ta kasance kamilalliya wacce ta samu tarbiyya daga iyaye na kwarai amma daga qarshe bayan sun aurar da ita ga wanda bataso duk rayuwarta ya canza ta yanda shaidan ya ribaci rayuwarta. Haka zalika shima ya kasance a bangaren masoyin nata wacce aka aura mishi wacce bayaso qarshe yashiga mummunan yanayi wanda har takai ya xamto abin kwatance acikin sa'annin shi,ga gorin da kowa yakeyi mishi akan zuciyar shi ta mutu ne shiyasanya ya auri wacce zata ja ragamar rayywar shi.