Dalilan Yakin Badr

11 5 0
                                    

Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)

Kada muyi nisa da yawa, yana da kyau mu ambatawa masu karatu cewa a shekara ta biyun nan dai aka wajabta azumi da kuma shar'anta zakkar fidda kai, sannan a wannan shekarai dai aka fara sallar idi karama, saidai kafin ita akwai wani muhimmin al'amari daya faru wanda zamu ambaceshi da yardar Allah.

Kafin aiken da Annabi yayiwa su Abdullahi bn jahash akwai yakin daya fita da kansa. Wato yakin Abuwa'i ko kuma yakin Waddan. Ya fita don tarar ayarin kuraishawa, amma ba'a gamu ba. Saboda kafirai sun wuce da gaggawa.

Bayan wannan akwai aiken da Annabi ya yiyyi amma shima ba'a haduwa sai akaita sabani. Don haka ne a lokacin da Annabi yayi niyyar zai tura su Abdullahi Bn Jahash sai ya boye abin wanda hatta su yan aiken ba'a basu damar budawa ba sai sunyi tafiya mai nisa. A karkashin wannan saimu gane cewa Annabi bawai rayuwa yake da ka ba. Yana rayuwa ne yana daukar darussa da kuma karantar wajen da yake rayuwa a ciki da kuma mutanen da yake rayuwa dasu.  Tunda sabanin da ake na haduwa da kafirai akwai yiyuwar suna samun labarin fitar Ma'aiki (S.A.W) ko kuma aikensa. Musamman idan muka duba cewa Yahudawa da munafukai suna kewaye da Annabi a madina, don haka duk abinda suka gani zasu iya kaiwa kafirai rahoto... To da yiyuwar bayan tsoro da rashin aminchi da yasa kafirai suke wuce madina da gaggawa akwai munafuncin da ake kai musu akan abinda Annabi ya shirya akansu. Saidai wannan hasashe nane, ban kuma riski wanda yayi irinsa ba a littafan dana leka na wajena. sai dai kamar a yakin badar da wasu yakunan zaka iske akwai ruwayoyi da suka nuna munafukai sun fitar da wani sirri... Nan dinma na bayyana cewa babu maganar a littafan da nake dasu ne don bayyana amanar ilmi. Domin shi rubutu idan akace na addini ne to dole sai an samarwa komai madogara...

Abin lura na gaba shine an fara shar'anta zakkar fid da kai gabanin zakka ta farilla wadda tana cikin rukunan musulunchi.

Hakanan a cikin musulmai na farko farko da suka musulunta a madina akwai wani tsoho mai suna Kulthum Bn Hidm (Siratun Nabawiyya).

Haka nan akwai Usman ibn Maz'un (Nurul Yakin)

Duk da sahabbai sun bar Makkah, amma kafiran Makkah sunata turo musu da sakonni cewa zasu zo har makkah din suyi maganinsu. 

Sahabbai suka zama babu sukuni, basa bacci da daddare sai suzo suyita gadin gidan Annabi, idan wasu basa nan zaka tarar da wasu. Basa jin wani bakon motsi ko kara face sun fito suna duba lafiyar Annabin rahama. Wani lokacin idan akaji wata kara suka fito donsu duba lafiyar manzon Allah (S.A.W) sai su tarar shima ya fito don duba lafiyarsu... Duba wata soyayya don Allah, kowannensu ji yake shine mafi cancanta daya kula da dan'uwansa. Basu daina zuwa tsaron gidan Annabi ba har saida Allah ya sakko da aya wadda take nuna tabbas Allah ya kiyayeshi daga sharrin mutane.

.والله يعصمك من الناس..

Bayan saukarta Annabi ya fito garesu yana farin ciki saboda baya son abinda zai takurawa sahabbansa, ya biya musu ayar sannan yace dasu kowa ya tafi suma su rinka hutawa. Hadisin na nan cikin Sunan Tirmidhi daga Nana Aisha.

Ka tuna irin yadda wannan jibgegen Sahabin Safina yake, baya bacci da daddare saidai yayita kewaye gidan Annabi. Shi da kansa yake cewa idan na tsaya a gaban gidan sai inji kamar abokan gaba ta baya zasu fito, hakanan idan na tsaya a baya sai inji kamar ta gaba za'a bullo, don haka sai inyita zarya...

Ana cikin wannan yanayi kawai sai labari ya iske manzon Allah cewa akwai wata tawagar kafiran kuraishawa data tafi kasuwanchi, harma sun dauko hanyar dawowa daga Syria. Kuma suna karkashin jagoranchin Abu sufyan. Wanda yana daya daga cikin wayanda sukafi muzgunawa game da matsa lamba ga musulmai a Makkah. 

Munji irin yadda kafirai suke da burin zuwa har makkah suyi fata-fata da sahabbai da Annabi musamman dama sun tasamma kashe Annabi, amma saiya tsere musu.

Muna kuma sane da cewa kafiran nan sune dai wayanda suka kwace mata, ya'ya' da dukiyoyin sahabbai bayan tirsasa musu dayin hijira da sukai...

Muna kuma sane da cewa sune dai wayanda suka hana raunanan sahabbai yin hijira don kawai sunada karfin iko a kansu. 

Bamu manta ba dai da cutarwa da sukewa Allah na hadashi da abokan tarayya, da kuma cutarwa da sukewa Annabi da sahabbai.

Kar dai mai karatu ya gafala da cewa; dalilin cin zalin musulmai da sukai har yanzu rainin da sukaiwa musulmai yana nan cikin zukatansu. Duk da dai musulman sun samu karfi ba kamar da ba, amma dai rainin nan yana nan har yanzu cikin zukatan mushrikai, shi kuwa musulmi mai izza ne. Shiyasa kuskure ne kana musulmi kaje wani guri wanda akwai wayanda ba musulmi ba ka kaskantar da kanka kota wacce hanya. Mutukar ba akwai wani dalili mai kwari ba.

Duk na kawo wayannan bayanaine saboda mu san cewa hukuncin da Annabi yayi daidai ne. Tare da cewa nasan masu karatu babu wanda zaiga kamar hukuncin da Annabi ya dauka ba dai dai bane. Saidai ka tuno cewa akwai wasu wayanda suke sukar addinin musulunchi da cewa addinin ta'addanci ne... Mun kawo hakan don kada shubuharsu ta rudu mai karatu. Wanda akwai bayani da zamuyi na rushe dukkan shubuhohinsu ko a kusa ko a nesa.

★ 

Annabi Muhammad (S.A.W) da yaji labarin wannan ayari na kafirai dauke da dukiya mai yawa, sai yayiwa sahabbai umarni da su kasance cikin shiri don tarar wannan ayari na kafiran Makkah. Kamar yadda aka saba, sai labari caraf ya jewa Abu Sufyan don haka ya tura yan aiken gaggawa makkah yana sanar dasu abinda ke faruwa. Su kuwa da jin haka sai suka fito kwansu da kwarkwatarsu don kare dukiyoyinsu da kuma fatattaka musulmai don kece raini. Don haka babu wani namiji mai jini a jika da suka barshi ba tare da sun fito da shi ba. Suka hada gagarumar runduna.

Shi kuwa Annabi ba da shirin yaki ya fito ba. 

Zamu dakata anan.

Sai kuma a rubutu na gaba.

 
Naseeb Auwal
Abj umar Alkanawy!

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)Where stories live. Discover now