Rayuwa kafin Annabta ★

196 17 2
                                    

Bayanai sun gabata akan yanda duniya take kafin Annabtar Annabi Muhammad (S.A.W).

Kuma kamar yadda duk mai hankali ya sani, tabbas Allah mai hikima ne, don haka kafin ya aiko Annabin rahama, saiya zaɓar masa wajen da yafi dacewa da shi. Wato cikin larabawa.

Duk da irin halin da larabawa suke ciki na jahiliyyah, hakan bai hanasu riƙo da wasu halayen kirki ba, kamar gaskiya, karamci, amana, izza, rashin daukar raini da kuma taurin kai akan abin da suke kai. Sannan suna gujewa yaudara da ha'inchi.
(Rahiq Maktum)

Sannan ta fuskar al'adunsu, sunada riƙo da al'ada ta inda zasu iya mutuwa akan kiyaye al'adarsu.
(The life of mahomet vol. 1 & Muhammad rasulullah P. 45)

Don haka a irin wannan yanayi ma'abota addinin hanifiyyah basu da damar yiwa larabawa wa'azi. Domin larabawan a shirye suke da su mutu akan abin da suke kai.
(Muhammad rasullullah 45).

Allah daya zaɓarwa Annabi ƙabila mafi girma sai ya zabar masa dangi mafi girma wato Quraishawa, babu wani waje da Annabi zai kasance face Allah ya zabar masa mafi girma da falala. Kamar yadda ya bayyana hakan (Annabi) a hadisai wayanda Muslim da tirmidhi da wasun su suka rawaitosu.

Fa'ida= Bawai zamowar Annabi ne a cikin larabawan ya sanyasu suka zamo mafiya girma ba, dama Can a cikin ƙabilu sune mafiya girma da falala a wajen Allah, kamar yadda ibn taymiyyah ya fadada bayani a littafinsa Istiqaama!

Zamansu masu falala a kankin kansu yana ƙarawa Annabi falala fiye da ace basu da wata falala shi kaɗai ne mai falala.

Asalin larabawa kafin zuwan Annabi Muhammad (S.A.W) suna kan tafarkin Annabi Ibrahim, har zuwa lokacin da Amru bn luhayyi shugaban ƙabilar khuza'at ya sauya musu tunani da Alƙibla.

Amru bn luhayyi kuwa mutumin kirki ne asali, mai ƙoƙari wajen ciyarwa da bauta da sadaka gami da karamci. Don haka sai suke tsammanin shi wani babban makusancine ga Allah.
(Rahiƙil maktum P.33)

Don haka wata rana yaje sham da yaga yadda ake bautawa gumaka sai abin ya burgeshi, sai ya taho da gunki guda daga gumakan inda aka ajiyeshi a ka'aba. Sannan ya kira larabawa zuwa bautar gumaka kuma suka amsa masa.
(Kitabul Asnam ibn kalabi P. 28 & Rahiq maktum P.33 & Muhammad Rasulullah)

Da abin ya faɗaɗa sai ya zamana kowace kabila tanada nata gunkin.

Zuwa don rushe ka'aba

Tabbas larabawa sun ɓata ɓata mabayyani. Har ya zamana a ka'aba kaɗai ban da cikin garin makkah akwai gumaka kusan ɗari uku da sittin kamar yadda muka faɗa.

Abrahata (wani shahararren sarki) yazo don ya rushe ka'aba, ya taho da gagarumar runduna cikinta harda wata giwa mai tsananin girma. Amma burinsa bai cika ba domin kuwa Allah ne ya saukar musu da tsuntsaye ɗauke da duwatsu na gidan wuta aka hallakasu.
(Sirah ibn Hisham)

Wannan sarki burinsa shi ne ya rushe ka'aba saboda ya hana masu ziyartar makkah, domin wannan ɗaki mai alfarma shi ne babban abin da yake janyo hankalin mutane suke tururuwar zuwa, to don haka idan ya rushe ɗakin ka'aba ya kuma gina wata a garinsa to mutane zasu koma ziyartar garinsa. Don haka ya tashi wannan runduna mai girma wadda Allah ya hallakata.

Sanadiyyar faruwar hakan sai girman Ƙuraishawa ya kuma ƙaruwa a idon duniya.
(Muhammad Rasulullah P.75).

Aure mafi daraja

Al'amarin Abdulmuɗɗalib kuwa wato kakan Annabi. Shine ya zaɓawa Abdullahi dansa matar data dace da shi wato Nana Aminah bnt wahab, a wannan lokacin kuwa itace mafi girman mata ta ɓangaren nasaba da gurin zama.

Kamar yadda muka sani a irin wannan lokaci mahaifin Annabi shi ne mafi girman mazaje a nasaba da asali, kenan mahaifi da mahaifiyar Annabin rahama dukkaninsu mafi girman al'umma ne a wannan lokaci.

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt