Yana zaune a cikin Office ya ji karar shigowar message dinta. Dubawa ya yi ya ga abin da ta rubuta, ya yi bayyanannen tsaki yana al'ajabin mutum irin Mahboobah, yana mamakin zuciya irin tata, wadda sam ba ta san wani abu wai shi fushi ba. Tun da yake da ita sau daya ya taba ganin ta bata ranta, a lokacin da ya ce zai zubar da cikinta.
"Ameerah?" Ya fadi a bayyane, ya ji dadi, sai dai a take ya karyata kanshi, ya karyata jin dadin da yake tunanin ya yi. Halittar da bai taba jin soyuwarta ba ce za ta haifa mishi diya har ya so ta? Ba ya tunanin akwai ranar, ko kadan ba zai taba son yarinyar ba.
Wayar tashi ya ajje, ya jawo wasu takardu yana dubawa, sai dai duk layi daya da zai karanta, text message din Mahboobah ne ke dawo mishi, yana zaga duk wani noti da ke cikin kwakwalwarshi. Sai kawai ya ji yana son ganin hoton yarinyar, yana son ganin ta, sai dai ta yaya? Ba ya son duk waya alama da za ta nuna yana son yarinyar. Idan ya tambayi Khaleed, Khaleed din zai yi tunanin ko son yarinyar yake tun da har ya nemi ganin hotonta. Mahboobah? Ya gyada kai, yana jin dacin tunanin da ya ambatar mishi sunanta. Bai ma da lambarta a babbar wayarshi da yake chatting da ita. Ba ya jin zai iya cewa ta turo mishi don ma kar ta ji dadi.
*
Ba wani taron suna aka yi ba, saboda Mahboobah ta ce ba ta son taron, ita din da ma can ba ma'abociyar son taron mutane ba ce, ko na bikinta ma don an matsa ne, wannan kuwa dole suka bar ta, saboda ta kafe a kan ba ta so din.Har a wannan lokacin Ishraq bai san kalar gudan jinshi ba. Amma duk da haka sun yi kaya na gani na fada, duk da cewa ba shi ya siya ba, Mami ya tura ma kudin ta siyi komai aka kai. Ita kanta uwar jegon kaya kala goma sha biyu aka mata, Ameerah kuwa, ba a magana. Tsadaddun kaya irin na kasashen ketare aka gwangwaje ta da su.
Ranar da suka cika wata biyu, ranar ne Mommy ta sanya musu lokacin komawa. A wannan lokacin sosai Ameerah ta shiga zukatansu, saboda irin yaran nan ne masu tsananin shiga rai, ga ta farar fata, jikinta gubul-gubul, tun kafin a yi arba'in dinta take dariya sosai. An mata aski, amma kanta har ya sake cika.
Fareedah, Saleemah da Haneefa ne 'yan rakiyar, sai Goggo, suka yi sallama da Mommy suna isa motar Yah Aliyu wanda zai kai su.
Ko da suka isa gidan, gate din a rufe yake, karamar kofar jikin gate din ma a datse. Mamaki ne ya kama su, kasantuwar sun san Ishraq ya san da batun dawowar, har lokaci sai da aka fada wa Mami, minti biyar kadai suka kara a kan yadda suka fada din.
Takaici ne ya kama su su duka banda Mahboobah da zuciyarta ke riya mata akwai dai yadda aka yi.
"Ki kira shi mana." Aliyun ya fada, yana tsananin jin haushin wannan rainin wayon na mijin da kanwarshi take aure.
Tana tsoron kiran wayar tashi, sai dai ba ta da zabin da ya wuce hakan. Wayar ta danna tana latsa kiranshi, tana jin gabanta na tsananta bugawa, idan ma ya dauka din, ba ta san abin da za ta fada mishi ba, ko kadan ba ta da kwarin guiwar da za ta iya daga labbanta ta yi mishi magana.
Dukkansu suna lura da yanayinta, suna lura da yadda duk ta daburce daga cewa ta kira shi a waya. Mamaki suke hade da tausayin kangin rayuwar da take cikinsa.
Sau uku tana kiran shi amma bai dauka ba. Kamar za ta yi kuka ta ce da Aliyu "Bai dauki kiran ba Yah Aliyu. Watakila yana wani aikin ne." Tana kokarin kare Ishraq din.
"Ko wanne irin aiki yake amma ai ya san da zuwan mu ko? Ke dai ba kya son laifinshi MB, kuma dole a fada."
Kallon ta ta mayar ga Haneefa, tana rasa kalmar da za ta yi amfani da ita wurin kare laifin da ita kanta ta san ya yi shi.

YOU ARE READING
Bakuwar Fuska
Romance"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan...