Story continued...(Ci gaban labari)
Da yanayin annurinshi kadai Mami ta fahimci akwai kyakkyawan labari a bakinshi. Duk da cewa a iya bisa labba annurin yake, ya yi duk iya kokarinshi na ganin Mami ba ta fahimci damuwa da yake ciki ba, sai farin cikinshi kadai ta iya hangowa.
"Kamar akwai labari mai dadi a bakinka likita." Ta fada a lokacin da take zuba masa farfesun kan rago da sinasir.
Ya dago kyawawan idanuwanshi ya kalle ta, ya sakar mata murmushinshi da yake kara yawaitar kyau a bisa halittar fuskarshi.
"Burinki ne ya cika Mami." Ya furta yana mai sunne kanshi.
Ta sani, duk duniyar nan babban burinta guda ne, ta tabbatar kuwa da cewa shi Ishraq ke nufi. Hakan ya sa ta sakin murmushi a saman dattijuwar fuskarta. "Alhamdulillahi! Allah abun godiya. Gaskiya na ji dadin wannan labarin. Ya sunanta?"
Ya dukar da kanshi kasa. "Sunanta Mahboobah."
"Ma shaa Allah! Kai anya kuwa yau zan iya bacci?" Ta zauna bayan ta gama zuba mishi abincin. "Ko kai fa Ishraq. Yanzu na ji batu. Gaskiya wannan lamari ya yi mini dadi kwarai da ainun. Allah Ya yi maka albarka ya sa yarinyar arziki ce gare mu baki daya."
"Ameen Mami. Sai ku yi magana da su Uncle Fahad. Kila yanzu za su sama mun lafiya da zancen Bilkeesu."
"Ai yanzu ma in banda dare ya gabato da na kira su. Amma gobe da safe da izinin Allah zan kira Fahad, zan kuma kira kanina Salihi, su shirya zuwa neman auren tilon gudan jinina."
Annuri ya kasa boyuwa daga saman fuskarta. Abinci take ci amma murmushi kawai take sakar wa kanta.
"Likita yaushe za a kawo mun ita ta gaishe ni? Na ji kaunarta ta shige ni sosai Ishraq. Ina son duk abin da kake so. Ina son Mahboobah tun kafin in gan ta."
Tausayin Maminshi ya ji, ta yanda take tunanin auren soyayya ne zai yi. A wani bangaren kuma takaicin yanda ta tilasta mishi tsaida mata yake yi, ga shi dalilin haka ya sanya shi zabar wacce bai taba jin ko dison sonta a zuciyarshi ba.
"Mami ba sai na kawo ta ba, na tabbata ma a gidansu ba za a bar ta ba. Mami ita din da za ta zama taki. Ki daina azarbabi gare ki ma za ta dawo har sai ta gundire ki..."
Ta yi saurin katse shi, "Ba za ta taba gundira ta ba Ishraq. Zan so Mahboobah tamkar diyar da na haifa da cikina. Zan gwada mata soyayya tamkar yanda zan gwada maka. Zan ja ta a jikina fiye da yanda nake jan ka, saboda ita mace ce, na so diya mace sai Allah bai ba ni ba, Ya bar ni da kai daya tilo kuma ina godiya gare Shi. Ga Mahboobah nan za ta maye mun gurbin diya mace."
Murmushin dole ya saki, kafin ya goge bakinshi da tissue ya fara kwashe kayan wurin.
*
Bakar cotton long sleeve ya saka, ya sanya ash din trouser, ya yi zanzaro, ya dora ash and black neck tie, ya dora ash suit a saman rigar shi, sannan ya sanya siririn medical glasses dinsa. Ya kalli kanshi a madubi, ya fito sak a Doctor Ishraq dinshi. Me ya rage? Ya dauko comb ya hau sharce kwantacciyar sumarshi. Zahirin kyanshi ya fito."Assalamu alaikum." Ya tsinkayo muryan Mami daga bakin kofar dakinshi. Ya amsa sallamar yana mai waigowa tare da sakin kyakkyawan murmushin tarbarta.
"Mami ina kwana."
"Lafiya kalau likita. Har yanzu ba ka fita ba?"

YOU ARE READING
Bakuwar Fuska
Romance"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan...